Tun daga ranar Saif bai kuma kiranaba, kwanansu Abba biyar da zuwa aka fara maganar komawa gida dady ya yadda zai koma gida amma abin mamaki ga yan uwana nan ni kuma na murje nace ni bazan komaba da aka tambayeni me yasa nace ba komai kawai suje zan taho daga baya.
Halifane ya sameni a dakinmu ina kwance ni kadai ya zauna a gefen gadon yace "fadimatu tashi muyi magana" ba musu na tashi zaune ina kallonsa shima ya juyo sosai yana kallona sannan ya fara magana "fadimatu inaso ki gayamin tsakani da Allah menene dalilin da yasa kikace bazaki koma gidaba? Karki manta nan ba kasarmu bace sannan bamu da kowa anan zaman kadaici mukayi ko a wancan karon to menene dalilinki na cewa bazaki tafi gidaba alhalin dady da momyma sun yadda zasu koma?" Shiru nayi na wasu yan seconds looking for the right words zuwa can nace "Halifa bawai bazan komabane gaba daya ina sone kubarni nan da wani lokaci zan biyoku zan dawo amma ba yanzuba "saboda me?" Ina wasa da yatsun hannuna kaina a kasa ban taba jin kunyar halifaba sai yanzu nace "saboda saif, idan na tafi bazaisan inda nakeba idan ya dawo bazai san inda na komaba amma idan ya dawo sai nima na koma gida at least kaga yasan inda nake" dariya Halifa yayi yace "lallai ma fadimatu sai akace miki idan ya dawo bazai San inda kikeba? Abdul fa? Bazaki iya bashi address dinba ko kuma ki rinka kiran number dinsa idan ya dawo zaki sameshi kin gane? Banaso namiji ya saka ki juyawa family dinki baya family din da muka dade muka kuma sha wahala kafin samunsa, kar kiyi haka ki yadda zaki koma tun kafin dady da momy susan menene dalilinki na cewa bazaki bisuba, kinsan ba zasuji dadiba ko?" shiru nayi na kasa yadda da abinda Halifa yace sannan na kasa karyatashi tabbas it's possible na bawa abdul address din kuma Saif ya samu amma na kasa sanin dalili ji nake kamar idan na tafi shikenan na tafi kenan. Haka dai Halifa ya zauna yayi ta rarrashina da shawarwarin yadda zamu hadu da saif koda na koma gida sannan yayimin alkawarin shima zaiyi iyakacin yinsa na hadu da Saif, daga baya dai har na yadda nace masa "na yadda Halifa zan koma gida zan koma tare da yan uwana" Halifa yayi farin ciki sosai sannan muka tashi muka taho wajen su momy, muna fitowa muka tarar da Na'im tsaye a tsakar gida jikin kofar dakinmu kallona kawai yayi da wani irin yanayi nima kallonsa nakeyi ina mamakin wanne irin abune wannan? Mun kalli juna na wasu seconds sannan ya juya ya fice da sauri daga gidan ba tare da yayimin maganaba.
Bayan na gayawa su momy suyi hakuri na yadda zan koma gida tare dasu, nan aka fara shiri na komawa Niger kowa da abinda yake, mun hada komai na gidan na siyarwa min siyar na bayarwa mun bawa makotanmu sannan aka saka ranar tafiya ranar asabar sati guda kenan da zuwan su Abba. Ranar juma'a da safe muna tsakar gida Rufaida nayimin kitso irin na buzaye da yake kuma gashin nawa irin nasune sai kitson yayimin kyau sosai, muna cikin yi sai ga Na'im ya shigo tare da Halifa da Tj , da sauri Halifa ya matso kusa dani ya tsugunna yana cewa "wow kanwata kinga yadda kikayi kyau kuwa? Gaskiya wannan kitson yayi kyau sosai dama Saif nanan " dariya kawai nayi ina rufe fuskata nace "nagode amma ai kasan ko yayanan ba gani zaiyiba tunda ba bude masa kai nakeba" shima dariyar yayi yace "ohh hakanefa amma kinsan yadda za'ayi?" Kai na girgiza ya cigaba " idan akai bikin ranar da za'a kaiki sai a kuma yi miki irinsa kinga yadda zai gani sosai kenan" dariya muka saka dagani harshi tare da tafawa Na'im dake tsaye bakin kofar kitchen yaja wani mugun tsaki tare da cewa "wai kai Halifa wanne irin banzane kai? Maimakon ka hanata soyayya ko ka rabata dashima gaba daya amma sai kake kuma ingizata ko? Wannan yar jaririyar kakewa maganar aure dan taya bera bari" da sauri na kalleshi ina ture hannun Rufaida daga kaina nace "waye za'a raba dani din?" Yana min wani mugun kallo yace " that so called boyfriend of yours " da sauri nace " don't you dare call him so called" da mamaki yace "ke! Wai rashin kunya zakiyimin? An gaya miki shashashun yayyenkine masu yi miki dariya? Idan nace masa so called din sai menene?" Wani kukane yazomin na kuwa mike tsaye ina cewa "wallahi ko me kace mishi dai ya fika sau miliyan a wajena da wajen mutane da yawa kuma wallahi ka ja girmanka karka kuma cewa zaka bada shawarar a rabani da Saif" yana wani yamutsa fuska yace "sai me idan an rabaki dashi me zakiyi?" Da sauri ina goge hawayen idona nace "saboda shi ruhinane the minute aka rabani dashi za'a dauki gawata a wajen" ina gama fada da sauri nayi daki nabarsu a wajen gabadaya sunyi tsuru tsuru ina shigewa daki Halifa yayi niyyar bawa Na'im hakuri akan rashin kunyar da nayi masa amma bai saurareshiba yayi waje da sauri shima a zuciye. Da yamma aka hadamu ana maida magana wai za'ayi mana sulhu har dasu momy saboda fadan namu yayi yawa, ni akasani bashi hakurin rashin kunyar da nayi masa shi kuma akace babu ruwansa dani babu ruwansa da soyayyata. Naji dadi sosai da ya kasance kowa ya yadda ya karbi soyayyata da Saif shi kadaine yaki karba ban kuma san daliliba ban kuma damuba dan matsalarsace ba tawaba. Muna cikin haka akayi sallama a waje Halifa ya fita zuwa can ya dawo yace "dady wai wanine yake sallama da kai yace ace maka Alh mudassir ne abokinka" nan da nan jikin dady ya fara karkarwa kamar zai fado daga kujerar da yake su uncle Ibrahim suka rikeshi da Na'im amma ina da kyar aka samu ya dawo hayyacinsa kira yake "ku rikeshi kar ya gudu mugune macuci azzalumi ku rikeminshi" haka yayi ta surutu sai da kyar aka samu ya nutsu akace a shigo da wancan mutumin, bayan an shigo dashi ya zauna dady nayi masa wani mugun kallo yace "ban taba tsammanin kai azzalumi bane macuci sai da ka nunamin ina dukiyata ina kudina kalli halin da ka sakani ni da iyalina da duk wani masoyina kai yanzu bakaji kunyar nunamin fuskarkaba?" A hankalin mutumin Wanda zai kai sa'an dady ko ya girmeshi yace "ko daya Alh Kabir banji kunyaba dan banyi abinda zanji kunyaba na tausaya maka kwarai da halin da ka shiga amma babu yadda zanyine nima abin a tausayawane sannan Allah ya Sani na nemeka kamar me sai yanzu Allah yayi zamu hadu" wata dariya dady yayi yace "lallai Alh mudassir baka da kunya na yadda sannan baka da imani yanzu me ya kawoka? Kubra mutumin da ya tafimin da kudinane fa" ba karamain shock mukajiba gaba dayanmu, da sauri Halifa ya yunkura da niyyar damkar wuyansa tayayama zaiyi mana abinda yayi mana sannan yana gaya mana wai baiyi abin kunyaba? Da kyar Tj da Na'im suka shawo kansa ya zauna, kuka dady yake da hawaye yace"mudassir kayimin bayani yadda akai ka damfareni sannan zakacemin wai bakaji kunyaba sannan ka nemeni baka samuba ta yaya?" A nutse mutumin ya fara magana kamar haka "har ga Allah kuma Allan ne shaidata banyi niyyar abinda ya faru ya faruba, banzo maka da maganar business na mota dan na damfarekaba tsakani da Allah na Kawo maka shawarar, bayan na karbi kudinka naje companyn motar kamar yadda mukayi dakai na kuma fara cike papers nayi nisa da cinikin dan payment kawai yayimin ragowa ganin kudin da motocin da zan siya akwai yawa yasa sukace sai sunyi background check nawa kafin mu karasa business din gudun kar na damfaresu dan haka na shirya na tafi aikin hajji kafin su gama a lokacin an fara aikin hajji, naje na gama komai na shirya zan koma American to ni ban sayi komaiba dan abinda na siya yana karamar jakata akwai wani alhaji kuma da mukayi aiki tare dashi wani American mun saba ba laifi sai yaga ban siyo komaiba shi kuma kayansa sunfi karfin jakarsa dan haka yace zai saka kayansa a jakata idan yaso idan mun koma America sai ya karba kaga a matsayin kayanane kenan shi basai ya biya kudi na extra kg ba, ganin ba wani abu zanyi da nawa kg dinba sai na yadda ya zuba kayansa muka taho, a airport na saudia kawai ina zuwa wajen checking sojojinsu suka kamani wai da cocaine cikin jakata nan na tubure akan babu aikuwa suka nunamin ita ina ihu ina komai suka tasa keyata sai prison dinsu, dakyar na samu suka saurareni nace musu ba kayana bane ga yadda mukayi da wancan alhajin amma da akaje shima aka kamoshi kafin jirgi ya tashi sai ya musa akan shi wallahi bai tabamin maganaba ma, yadaisan daga country daya muke dakinmu kuma daya amma dama tunda ya ganni yaji banyi masaba yaki kulani maybe haushi naji saboda baya kulani shiyasa na yi masa wannan sharrin. A ranar nayi kuka kamar karamin yaro tunda nasan halin saudia kasheni zasuyi babu ruwansu kuma shi mai kayan shi kadai zai iya fadin gaskiya shi kuma babu alamun ma zaiji tausayina ya fadi gaskiyar dan wata tsana da yake nunamin zakayi tsammanin da gaske ni nayi masa sharri bashi ba."
"Rashin shedar da zan bayar na kare kaina yasa aka sakeshi ni kuma aka ajiyeni za'a yankemin hukunci nan da wani lokaci da su suka sanshi, kana daya daga cikin dalilan da suka saka nayi ta addu'a akan Allah ya fito dani ya bayyana gaskiya saboda nasan babu yadda zakayi kasan inda nake nima bani da yadda zan sameka na gaya maka inda kudinka suke na kuma san ba karamin mawuyacin hali zaka shigaba idan ban maida maka da kudinkaba, nayi ta addu'a kullum dare da rana da alkawarurruka kala-kala ina fatan Allah ya ji kaina ya fito dani, ban san daliliba suka ajiyeni na tsahon lokaci ba tare da sun yankemin hukunciba, na dade duk wannan lokacin ina prison dinsu dan ma Allah ya taimakeni nasu ba irin namu bane, kawai wata rana ina kwance a dakina akazo akace na fito bayan na fito suka bani kayana da komai tare da kaini airport suka sakani a jirgi, sai a airport dinne nake tambayar dan sandan da yakaini me yake faruwaya? me yasa aka sakeni? Shine yake gayamin gaskiya ta bayyana har an kamo wancan mai kayan ashe harkarsace yana safarar kwayoyin shine yanzu dubunsa ta cika da akayi bincike aka gano shine dai wanda nace kayansane bayan sun azabtar dashi ya fada musu gaskiya shine suka sakeni zakuma a maidani kasata."
"Bayan na koma America na dan murmure na shiryo na taho Nigeria da niyar nemanka na baka kudinka, na nemeka sama ko kasa na rasa babu Wanda ban tambayaba wanda nasan ya sanka har Dr dinka da sauran business partners dinka amma babu labari kowa sai dai yace baisan inda ka komaba name gidanka ma na tarar ka siyar dashi, sai jiya naga sani mai kama dakai na biyo bayansa sai naga ya shigo nan gidan dan haka na tafi na niyyar yau zan dawo idan yasanka shikenan idan kuma bai sankaba sai na cigaba da nemanka" shiru yayi yana ajiyar zuciya zuwa can ya cigaba " nasan nayi maka ba daidaiba sannan kasha wahala a dalilina amma ka Sani cewa banyi domin na cutar dakaiba ko iyalinkaba ban kuma yi don na cinye maka dukiyaba idan kuma baka yaddaba zaka iya zuwa saudian ka bincika idan na dawo maka da dukiyarka sannan ina rokonka dan Allah dan annabi kayimin afuwa ka yafemin dan Allah" shiru kowa yayi na wani lokaci, gaba daya jikinmu yayi sanyi sai zuwa can Abba yayi garan murya yace "tabbas kaima abin a tausayawane domin kaga rayuwa kaga jarabawa sannan dama ita rayuwar duniya haka take jarabawar wani tana haduwa data wani anso dukkaninku a jarrabeku shiyasa abinda ya faru duk ya faru sai dai fatan Allah ya bamu ikon cinye duk wata jarabawa ameen" duk muma muka amsa da ameen nan dady ma yace "mudassir na yafe maka kuma na tausaya maka abinda ya faru Allah ya kare gaba ya rabamu da mugayen mutane" muka sake cewa ameen sannan ya cigaba da cewa "nima ina rokon gafararka akan muguwar fahimtar da nayi maka" da murmushi Alh mudassir yace "babu komai Allah ya gafarta mana baki daya, sannan kudinka yana nan kamar yadda ka turomin yana account dina zamuje har banking ayi maka transfer din abinka" murna gaba daya muka fara. Wato komai na duniya duk wata wuya tana da karshe sai dai idan baayi hakuriba ko kuma anyi hakurin amma kadan.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...