Haka aka cigaba da shirye-shiryen biki ba tare da ango da amarya sun shiryaba, ranar daurin aure sagir yace ya shirya mana party kawayen amarya da abokanan ango, a lokacin ya nuna tamkar ya hakura har hakuri yaje ya bawa Kabir hakuri dashi akayi komai na bikin, ranar da daddare muka shirya muka tafi wajen partyn, an fara party lafiya kawai mutane suka fara faduwa tamkar wadanda suka bugu. Ba karamin tashi hankalinmu yayiba ganin kowa a wajen ya bugu sai yan tsiraru babu kuma yadda bamuyiba amma sunki tashi haka dole muka kyalesu aka debesu zuwa gida, ba su suka farkaba sai washe gari da safe ai kuwa anga tashin hankali iyayen kawayena Mata sukayi ta zuwa suna balai wai an bugar musu da 'ya'ya harda masu kai 'yayansu asibiti wai a duba musu ko anti raping dinsu. Ran Abba ba karamin baci yayiba da wannan abu daya faru gashi daga kawayena sai abokanan Kabir shi sagir dinma daya hada partyn babu abokanansa ko daya kuma shima sai safe ya farka balle ace shine dan haka abba yayi concluding Kabir ne ke da abokai yan iska sukayi drugging 'ya'yan mutane, ranar munga tashin hankali dan ba karamin baci ran abba yayiba dan haka sai da ran kowa ya baci a gidan yaya Ibrahim ma daya nemi shiga wankin babban bargo Abban yayi masa. Wannan abu daya faru yasa sai da aka daga kai amarya zuwa washe gari shima kanwar goggona da Maman Na'im sai kawayena su kadai suka kaini dayake gidan namu yana jikin gidan Abba dan haka da kafama mukaje. Tun daga wannan lokacin babu wani da ya kuma faruwa zaman lafiya muke da kabir muna shan soyayyarmu gashi dama can Maman Kabir na sona balle yanxu dana zama 'yarta, Na'im ya hado kayansa ya dawo wajenmu yaki komawa gida sai dai idan xan Shiga gaishe dasu mama mu shiga tare kuma mu fito tare mu koma tare.
Shekarata biyu da aure kafin Allah ya bani ciki kuma sai gashi min samu tare da Maman Na'im wannan abu ba karamin dadi yayiwa yaya Ibrahim da Kabir ba, haka muka cigaba da rainon cikinmu tare hatta da awo tare muke zuwa a lokacin shima sagir yayi aure, duk tsahon wannan shekaru munyi zaton sagir ya hakura ashe bai hakuraba rannan min fito ni da Kabir da Na'im muka shiga gida zamu gaisheda su mama, muna shiga muka Ganshi a harabar gidan Kabir ya mika masa hannu da nufin su gaisa amma instead of shima ya mika masa sai ya rungumeshi Kabir yayi mamakin hakan amma sai kawai ya share shima ya rungumeshi sannan ya cikashi mukayi ciki shi kuma yayi waje.
Muna shiga muka tarar da Abba yana pacing a tsakar dakin mama kuma na zaune ta zabga uban tagumi, da sauri Kabir ya isa garesu yana tambayar abinda ya faru maimakon Abba ya amsa kawai sai ya zira hannu a aljihun Kabir din duka biyun sai ga wata farar leda mai dauke da farar hoda wadda nidai ban san da zamanta a jikin Kabir ba, da mamaki shima Kabir din ke kallo tsakanin ledar da Abba kawai bamuyi auneba sai jin saukar mari mukayi Abba ya mari kabir na tsorata sosai shima haka amma mama ko dagowa batayiba sai kuka da ta fara, a zuciye Abba ya fara magana "ashe duk abinda ake gayamin akanka Kabir ina karyatawa gaskiyane? Cocaine a cikin gidana kuma a hannun dana dana nunawa so fiye da kowa fiye da komai? Kabir ka bani kunya kuma bani kayiwaba kanka kayiwa duniyace ta isheka riga da wando, bazanyi maka bakiba amma kaje zaka gani" yana gama fadar haka yayi cikin daki maybe idonane baiga daidaiba amma hawaye yake gogewa yayin shiga dakin. Da sauri Kabir ya karasa wajen mama yana tambayar me ya faru danshi har yanzu baisan abinda yake faruwaba, tana goge hawaye tace "sagir yasha Kawo sararka akan kana deban kudin Alh kana shaye shaye amma shi Alh yaki yadda shine yau ya Kawo masa hotonka kana siyan cocaine yace baiyaddaba shine yace idan ka shigo ya cajeka maybe ya samu sheda kuma gashinan an samu a jikinnaka, Kabir me yasa? Ka na Neman lalata yaddar dake tsakaninka da mahaifinka ko?" Da mamaki yake kallonta yace "wallahi wallahi wallahi mama ban taba shan komaiba wallahi wannan ma bansan yadda akai tazo jikinaba bani na sakataba ku yadda Dani" nikam tashin hankali ma ya saka na kasa aikata komai, na yadda da mijina wannan abin babushi a jikinsa dan ni na shiryashi ya akwai nasan Zan gani amma kuma ya akai yazo jikin nasa? Babu mai bamu wannan amsar dan haka dole muka karbi laifin da ba namuba domain laifin mijina nima laifinane.
Sai da akakai ruwa rana kafin Abba ya sauko ya Fara amsa gaisuwar Kabir a lokacin ya sameshi ya bashi hakuri ya karbi laifin ya kuma yi alkawarin bazai sake aikatawaba, sai a lokacin Abban ya dan sauko wannan abu kuwa ba karamin kona ran umma da sagir yayiba kuma babu yadda zasu iya sundaiyi mitarsu wadda ta janyo dole sai da Abba ya saka sagir kan harkar kasuwarsa saboda sunce an hana sagirne saboda yana shaye shaye amma an dauka an bawa dan cocaine dan haka anyi rashin adalci.
Bayan wannan ma bamu sake samun wata matsalarba har muka haihu sati biyune tsakanina da Maman Na'im na haifi Halifa itama ta haifi namiji Ahmad akece masa Tj. Tun dana haihu komai na Halifa ya koma hannun Na'im a lokacin shekarunsa bakwai amma har goyo yakemin komai yace Halifa bamaya kula Tj ko kadan idan akayi masa magana ma sai yace ai halifane kaninsa ba Tj ba. Wannan ya wanzar da shakuwa mai kyau tsakaninsu komai ya samo yace Halifa shima halifan tun yana jariri ko muryar Na'im yaji zai fara waige waige.
Ranar wata asabar da bazamu taba mantawa da itaba lokacin watanmu bakwai da haihuwa, Kabir ya gama baccinsa na safe da yake dama da weekend baya fita da wuri, bayan ya tashi ya shirya muka fito tare zuwa cikin gida muna zuwa bakin kofa wani mutum taremu yace " dan Allah Alh Ahmad nake nema" jin Abba ake nema Kabir ya tsaya mu kuma ni da Na'im da Halifa mukayi ciki, nan yace bari ya dubo masa ko yananan sai mutumin yace " koda yake ga wannan kawai ka kai masa maganinsane inji Dr yace ayi sauri yanzu a bashi a cikin tea din dazai sha" da mamaki Kabir yace "wanne irin magani kuma?" Sai mutumin yace "shi yasan da maganar amma Dr yace ayi maza a zubashi cikin ruwa ko tea yanzu" karba kawai Kabir yayi ya shigo jin ance ayi maza sai direct ya wuce dakin Abba duk da kwanan ummane Yau, yana shiga baiga kowaba sai kayan abincin Abban an hada tea, da alama ya hadane ya kuma shiga ciki dan haka sai kawai Kabir ya zuba maganin da niyyar idan Abba ya fito zai gaya masa idan yasan da maganar shikenan idan kuma bai saniba sai a Kira Dr din aji abinda zaice.
Yana gama zubawa ya saka cokali yana juyawa kawai sai jin salati yayi a kansa da sauri ya dago kai yana kallon umma dake rafka salati yana cewa "umma lafiya meya faru?" Maimakon ta bashi amsa sai ta cigaba da salatin har Abba ya fito daga daki shima yana tambayar "lafiya meya faru?" Budar bakin matarnan sai cewa tayi " dama sagir ya fadamin naki yadda wallahi Alh Kabir bayanka yakeson gani guba ya zuba a cikin tea dinka ina fitowa na tarar dashi yana zubawa" da mamaki Kabir ke kallonta yayinda Abba yake kallonsa yace " kabir me nakeji haka me ka zubamin a tea?" Ya bude baki zaiyi magana umma ta katseshi da cewa " au yanzu Alh sai ka tambayeshi? Wato baka yadda daniba ko shiyasa sagir yace na bar audio din daya turomin saboda idan ma wani abu ya faru ba yadda zakayi shi yayi makaba wannan wai wacce irin soyayyace abu kamar tsafi?" Kallonta Abba yake sai data gama yace "wanne irin audio kuma?" Da sauri tace "bari kajishi ma" wayarta ta dauko ta kunna masa wani audio Wanda Kabir bai taba sanin dashi a duniyaba. Muryar kabirce da alama waya yakeyi yana cewa "kaga mallam wai babanka ko nawa? Nace maka kawai ka kawomin gubarnan mai karfi wadda baza'a gani a jininsaba za'ayi zaton normal mutuwace, kaga kaf gidanmu ni kadai nasan yawan dukiyarsa idan ya mutu iyakar abinda na fito dashi iyacinta za'a raba ragowar kuma ya zama nawa nida matata da dana" saboda shock na wannan sharri Kabir kasama defending kansa yayi.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...