Chapter 19

78 9 0
                                    

Wata soyayyace mai tsabta ke gudana tsakanina da saif tamkar abinnan da turawa ke Kira soul mate haka muke, ba karamin so nake masaba, ada idan naga Koreans na soyayya sai nace anya kuwa akwai soyayya da gaske ko kuwa dai lokacinane baizoba? To idan lokacinane baizoba sai yaushe zaizo? Tabbas a yanzu na yadda lokacinane baizoba yanzu kuma da yazo ina jin dadinsa kamar me, nakan tambayi kaina wai ya akai na iya rayuwa ba tare da saif ba? Jinshi nake har cikin kaina koyaushe cikin tunaninsa nake.
Yauma kamar kullum na tashi na shirya na kuma shirya feena bayan min gama cin abinci muka fita tare, sai da na kaita school dinsu sannan na wuce wajen aiki. Wajen 11am na hango mutuminnan na rannan, ba karamin faduwa gabana yayiba na sunkuyar da kai don karmu hada Ido, unfortunately for me abokin aikina bayanan dan haka dole wajena zasuzo su biya, kamar wancan karan shida wannan kaninnasane, bayan sunzo na auna musu kayansu suka biya suka juya nan na dago ido ina kallon bayansa kawai shima ya waigo muka hada ido ya gallamin harara, gabanane kawai ke faman faduwa wannan kamar tayi yawa menene hadinmu da wannan bawan Allahn? Banajin wannan coincidence ne tabbas akwai dangantaka hararar ma iri daya da ta halifana. Wannan tunanin yasa nayi saurin tabo kamal da yake kusa dani yana juyowa na nuna masa computer ta nayi waje da sauri. Kamar wancan karon har sunje wajen mota sannan na samesu nayi masa sallama ya juyo yana kallona sai kuma yayi dariya "kamun kan ya karasa karewane?" Abinda ya fara tarata dashi kenan, na hadiye wani abu daya tasomin sannan nace "ko daya dama ba rasashi nayiba abinda kake zargi ba shine yake faruwaba, kamar yadda kace tabbas kayi kamane da dan uwana wancan karon na fasa fadane saboda ka riga kayi zeroing mind dinka a kaina dan haka ko na fada banajin zaka yadda amma wallahi ban taba ganin kama irin wannan ta kai da dan uwana ba anya bamu da dangantaka?" Wata dariyar ya kuma yi ammafa shi dariyarsa ba irin ta saif bace dariyarsa irin ta rainin hankalinnance sannan yace "babu! Bamu da wata dangantaka dan ni bama dan kasarnan bane kin gane? So cut it out. Tj shige muje wannan tana batawa mutane lokacine kawai" haka ina kallo suka shige motarsu suka tafi suka barni a tsaye a wajen kamar doluwa. Ajiyar zuciya na sauke na juya zan koma ciki kawai naga Abdul a tsaye yana kallona, murmushi kawai nayi masa na wuce amma sai ya kirani sannan ya wuce wajen motarsa dan haka nima na bishi har bakin motar tasa, kallona kawai yake yace "why?" Wata kunya naji dan haka na kasa dagowa na kalleshi na kuma kasa bashi amsa sai da ya kuma cewa "fatima why?" Sannan nace "kamarce tayi yawa Abdul ina son nasan hadinmu dasu" wani murmushi yayi yace "then dolene? Tunda ya nuna baya bukatar ki kulashi shikenan sai ki kyaleshi ai ba rasa yan uwan kikayiba da zai nemi wulakantaki" a hankali na dago na kalleshi wani hawaye mai zafi ya zubomin sannan na kuma sunkiyar da kai kasa nace "neman yan uwan nake ido rufe shiyasa, bani da kowa idanba momy, dady, Halifa da feenaba babu dangin uwa ba na uba ba uncles ba aunties shiyasa hankalina ya tashi nake tunanin anya bani da dangan taka dashi? Amma yace babu shi bama dan kasarnan bane kuma naji hakan a cikin muryarsa, Dan haka Zan daina binsa koda kuwa na kuma ganinsa insha Allah" da mamaki a muryar Abdul ya kuma tambayata "baki da dangi kamar ya" nayi murmushi Allah sarki saif yana da amana bai gaya masa komaiba duk kuwa da kusancin dake tsakaninsu nace "ka tambayi Yayana zai gaya maka komai" yace "no nikam ke na tambaya bashiba" nace "banason Kara tunawa da komai da ya faru a rayuwata amma shi idan ka tambayeshi zai gaya maka kace masa ni nace ya gaya maka" ina gama fadar haka nayi cikin shagon ba tare da na bashi damar yayimin wata tambayarba.
Yau na daddare da mukayi waya da saif yacemin wannan satin zaizo " Fatima wannan weekend din insha Allah zanzo na ganki nayi missing dinki da yawa har fa gizo kikemin" ina dariya nace "kai Yayana gizofa sai kace fatalwa?" Shima dariyar yayi yace "ai da zan iya zama fatalwa kawai dan nazo na ganki wallahi Zan yadda bakisan yadda nakejibane shiyasa" dariya na kumayi nace "ka zama fatalwa ka mutu fa kenan" " to meye a ciki at least kafin a kai gawata na ganki" nan da nan na hade rai kamar yana kallona nace "Bari mana me kuma ya kawo zancen zama gawa?" Yace "kefa kikace na sai na mutu kafin na zama fatalwa" maganar ta fara isata kuma dan haka nace "ya Isa to a canja wata hirar haka" kawai ya Kama dariya wai "kanwata bataso na mutu, to yanzu idan na mutun ya zakiyi?" Ji nayi kamar na kwada masa mari a kufule nace " nace ya Isa haka ko? Ya zanyi kuwa yadda kowa ya hakura haka nima zan hakura naje na sami wani na aura and live happily ever after" ai kuwa shima ya hau "to yanzuma kije ki auri wanin mana ai basai kin jira na mutunba, Malama a canja wata hirar ya isa kuma" dariya nayi masa nace "ohh dama ai nace a canjata kaki wai kishi kake?" Banza yayi dani bai bani amsaba dan haka ina dariya nace "shikenan na daina Yayana yi hakuri yaushe zaka taho? Friday ko Saturday?" Sai da yaja aji sannan yace "oho" wata dariyarce ta kuma tahomin amma na danneta nace "haba Yayana nace fa kayi hakuri kaji?" Sai daya kuma shan kanshi son ransa sannan yace "karki Kara gayamin zaki auri wani ba niba indai ba da gaske so kike na mutunba" da sauri nace "na daina Allah ya huci zuciyarka Yayana na kaina, to yaushe zaka taho?" Yace "wallahi ban saniba sai dai yadda ta yiyu maybe Fri da yamma maybe kuma Sat da safe" nace "to Allah ya kaimu ya kawomin kai lafiya" yace "ameen kanwata me kika tanadar min?" Haka dai mukayi ta hirarmu har saida muka fara jin bacci sannan mukayi sallama kowa ya kwanta.
A ka'ida ranar asabarce off dinmu dagani har Halifa dan haka ta zama ranar yin hirarmu tare da iyayenmu sannan a ranar nake siyo kayan miya da yawa nayi mana miyar sati guda in case Halifa zai dafa musu wani abun sai kawai ya dafa fari, a ranar ne kuma nakeyi mana wani girki mai dan nauyi. Kamar duk Saturday yauma na shirya yin irin wannan girkin sannan kuma da tarbar Yayana masoyina. Tuwon shinkafa miyar kubewa danya na shirya yi dan haka da naje yan kaba na samo kubewata mai kyau da nama (muma yanzu mukanci dan nama occasionally). Bayan na gama tuwona na sakashi a leda na zuba a kula sannan na dauko kubewa da niyyar gogawa, a kitchen nake aikin feena na tayani da surutu Halifa kuma yana dakinsa momy da dady na dakinsu, bayan na gama gogawa na bawa feena ruwan nace taje ta zubarmin dashi a waje amma yarinyarnan tana zuwa bakin kofar kitchen din kawai ta watsar dashi. Da sauri na kalleta nace "a bakin kofa dama nace ki zubarmin?" Sai kuma tayi tsuru tsuru "na gode kin kyauta baki da aiki sai na baki ki tayani aiki amma kalli abinda kikayimin, Allah ma ya kikyaye kema ki kiyaye wallahi idan ba hakaba ke zai fara kayarwa" ina gama fada na juya na cigaba da abinda nake.
Abinka da tsautsayi kawai na cigaba da harkata ban koma ta kan ruwan na shareshiba kawai sai ji nayi an zame ihune ya biyo baya sannan in no time naji buguwar kai da kasa, daga dukkan alamu momyce dan ihun yayi kama da nata dan haka nayo wajen da gudu ina zuwa kuwa na tarar da ita yashe a tsakar gidan bata ko numfashi. Wani mahaukacin ihu na saka bana fatan wani abin kuma ya kuma faruwa damu rayuwarmu ta fara kyau banason ta kuma dagulewa. Bansan me nakeyiba sai ganina nayi jikin Halifa yana rike dani saif kuma na zubawa momyn ruwa yana kuma pressing girjinta, da alama ihu kawai nake ina kiran momy shima halifan daya rikeni kuka yake yayinda feena ke tsaye kawai bakin kofar kitchen din tana kallonmu, ina iya jiyo dady daga daki yana faman Kira "Fadima Fadima menene me ya sami momyn Halifa kuyimin magana me ya sami kubran innalillahi wa Inna ilaihir rajiun dan Allah kuyimin bayani" akan gado yake shiyasa nasan da tuni ya kawo bakin kofa.
Dakyar Halifa ya samu na nutsu amma fa ban daina kukanba ihun dai na daina, still saif na kokarin numfashinta ya dawo sai da kyar muka samu ya dawo din amma tana jansa sau daya ta koma sai kuma bacci, ba karamin tsoro bancin ya bamuba kawai daga suma sai bacci? Ya kamata ace ta dan farka, banda numfashinta dake sauka zan iya cewa ba baccin takeba ko mutuwa tayi.
Haka dai Halifa ya dauketa ya kaita daki, muna shiga dakin muka tarar dadyma ya fado a gadon sai jan ciki yake yanason sai ya fito, haka dai aka kwantar da ita shi kuma dady saif ya dorashi a wheelchair dinsa. Girkin da ban kuma komawa takai ba kenan, ruwan kubewar ma sai halifane ya wankeshi falo kawai na koma na yi ta faman kuka saif kuma na aikin rarrashi, gani nake kamar ni na jawo mata da na tashi da kaina na zubar da ruwan ko kuma da data rubar a wajen naje na wankeshi ai da hakan bata faruba amma kawai sai na cigaba da harkata ga abinda na jawo matanan.
Sai bayan anyi azahar nayi sallah suma suka dawo daga masallaci sannan na fara tambayar saif yaushe yazo? Yace "zuwana kenan na hadu da halifa a waje na tsaya muna gaisawa muka jiyo ihunki, I'm sorry komai zaizo da sauki kinji Allah ya kiyaye gaba" hawayen da ya zubomin na share sannan na amsa da ameen. Mikewa nayi Halifa yace "ina zuwa?" nace "girkin zan karasa nasan kowa ya fara jin yunwa" saif yace "zaki iya? Ko na siyo mana wani abun kawai?" Da sauri na girgiza kai nace "aa ka barshi zan iya" sannan na juya na fice.
Da taimakon saif na karasa miyar dan shirme kawai nayi tayi da naje da yake ya iya girki, bayan mun gama muka zubowa kowa. Zuwa la'asar na koma dakin su momy na gani ko ta farka ina shiga naga tana mika dan haka na tsaya a kanta ina jiran ganin me zatayi ga mamakina sai ji nayi tace "la'ilahaillallahu Muhammadur rasulillah" da sauri na fara kiran Halifa na kuma zauna a kusa da ita, ai kuwa ya shigo harda gudunsa saif kuma ya turo dady, suna shigowa tana bude ido ta kafaminshi kuwa nima na kafa mata nawa sai can nace "momy?" Ta amsa da "naam Fadimatu bani da lafiyane?" Ai kuwa halifa yayi wani tsalle sai gashi a kan gadon yace "momy" ta juya ta kalleshi sai kuma tayi murmushi tana shafa kumatunsa tace "naam halifa" ai bansan sanda nayi mata wata wawuyar rugumaba shima halifan ya hada dani da ita ya rungume, kuka mukeyi kamar ranmu zai fita har bansan irin farin cikin da nake cikiba, sai da mukaji tana cewa "kun shakenifa " sannan muka cikata a tare, yunkurawa tayi ta tashi zaune tana kallon dady dake kan wheelchair yana faman kukan shima nan da nan ta sauko daga gadon ta tsugunna a gabansa tana cewa "dady? Alhmdulillah yaushe har ka fara iya zama? aikin nasu yayi kyau kenan? Kai amma naji dadi sosai wallahi alhmdulillah" sai kuma ta tsaya tana kallonmu daya bayan daya idonta ya tsaya akan saif ta juyo ta kalli halifa tace "wannan fa?" Da sauri nace "kinga momy ko yanzu ki huta tukunna bari na kawo miki abinci kici idan anjima zamu baki labarin komai so much happen kinji?" Kai kawai ta dagamin nayi waje da sauri. Ina kitchen saif ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace "congratulations" na juyo da sauri sai kuma na fara dariya nace "thank you yau kam ina cikin farin ciki ka tayani godewa Allah ya gama min komai momyna ta warke" shima yana dariyar yace " Allah abin godiya, yanzu bari naje gida na barku da momyn idan an jima na dawo OK?" Kai kawai na kada ya kuma cewa "take care" nace "you too ka gaishemin da Abdul" yace "zaiji" sannan ya juya ya fice.

FadimatuWhere stories live. Discover now