ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 8
Karfe takwas da rabi na daren litinin ,alhj ishaq kishigide a karamin falon, daya daga cikin wadan da ke part dinsa sanye yake cikin jallabiya yanayinsa na cikakkiyar kamala da nagarta tana tattare dashi a koda yaushe dan karamin tire inibi ne agaban sa yana sawa abaki , Abdullah yayi sallama yashigo ya isa gareshi daf da tuntun da dady ya tada kai" nan Abdullah ya zauna tare da nade kafafunsa hade dayiwa dady sannu da hutawa ,dady yadan tura masa ragowar inibin yasa hannushi daya ya dauka yasa a bakinsa.
Dady yace Kaci abinci ma kuwa ? Abdullah ya tura lip's din shi duk a baki ya girgiza kai ,sai zuwa anjima ,dady ya kada kai bana son kadinga wuce tara baka ci abinci Abdullah ya amsa bayan Yan hirarrakin abinda ya shafi office da maaikata dady ya kira sunnansa batare da ya kalle sa ba Abdullah ya amsa "dady yace Abdullah akwai abunda yake damunka cikin Yan kwanankin nan
Komai naka ya canza meye ya same ka ? tambayar tazowa Abdullah abazata sai kawai ya zubawa dady Ido shima dady kallon sa yake a hankali Abdullah ya sauke idanunshi tare da sunkuyar da kansa yasa hannushi yana shafa habarsa .bai ce komai ba dady yacigaba da nazarinsa , Abdullah yasake dago idanunshi still har yanzu dady shi yake kallo dady yace uhm tell me I am ur father what's wrong with u ,ya dauki tsawon lokacin Abdullah na tunani abinda zai ce ma mahaifinsa" tun yana yaro dady bai amince masa dayin karya ba, idan yayi laifi yana jin tsoro ya fadi abunda ba daidai ba sai dady yagano shi,dan haka yafi amincewa yafadi gaskiya cikin rawar baki yake son yayi magana murya kasa dady yasake cewa sanar dani Abdullah meke damunka ?Da Kyar sunanta ya subuce daga bakinsa yace dady Ai.. Ai..sha ce ."
Dady ya dubeshi a natse yace Aisha? Kansa Duke yace wata.....Sai Kuma yayi shiru ,dady ya tsaresa da Ido zuwa na dan wani lokacin "sannan ya numfasa domin ya dan fara gano kan al'amarin yayi murmushin yace to Aisha ce ta canza maka yanayi ka shiga damuwa ?ai duk tsanani yana tare da samu muddin za'a gayawa Allah sai a wannan lokacin Abdullah ya tuna da haka daddy yacigaba muddin zaka gayawa Allah bukatar ka da muwarka to zaka Yi nasara idan kaga bakayi nasara ba to daman can ba alkharin ka bace.abdullah ya girgiza kai domin maganar dady tasa yadanji kwarin giwa dady yace meya faru da Aisha?bbu komai daman mudan samu sabani ne kawai dady yasakeyin murmushin irin Nasu na manya tare da godewa Allah a zuciyarsa ,wanda shi har ya yanke hadashi da diyar abokinsa dake karatu a ghana sai ga mami itama tazo da nata batun na hadashi da faiza to daman duk rashin shi Abdullah bai kawo wacce yake so bane, a Fili dady yace a ina take tare da iyayenta ? Kuma waye mahaifinta ? Abdullah yayi saurin furta subuhanallahi acikin zuciyarsa sannan cikin murya kasa kasa yace sunan babanta mlm abu dady yayi shiru kmr bai ji ba yace Na'am? ahankali Abdullah yasake yin kasa da murya ya maimaita ,dady yakira sunansa ahankali mlm abu ......ya daga masa kai yace ina jinka ahankali Abdullah ya warwarewa dadinsa cikakken bayanin Aisha da iyayenta da Kuma inda suke da zama , cikin dabara da hikma duk sai da dady ya bincike labarin su wanda Abdullah ya sani kuma atake a nan dady ya gano matsayin da yarinyar take dashi a ZUCIYAR Abdullahsa.dady ya sauke numfashi ahankali yace maminka tasan da wannan maganar . Abdullah yayi saurin girgiza kai dady yace to ka kyaleta karkasanarda ita sai zuwa wani lokacin zan sanar da ita . Abdullah ya amsa sannan dady ya sallmi Abdullah ya tafi,yayin da yabi dan nasa da kallo , yaji matukar tausayinsa duk jarumta irin ta Abdullah gashi lokacin daya soyayya na neman rikita shi wanda shi kansa Abdullah bai gane ta ba "yana matukar jin kaunar yaronsa aransa domin yakasance mai tsananin biyayya ga uwa da uba, gashi da taren nasarori wani lokacin yakan zabi Abdullah din yayi abu akan shi yayi cikin yarda Allah Kuma sai yayi nasara" shi yasa ya damu da lamarin Abdullah din.Wani abun mamaki duk wannan dadewar da Abdullah yayi a part din dady faiza na makale tana jiran fitowarsa dan haka yana shiga part dinsa ta rufa masa baya frig ya bude ya dauki lemon kwali ya bude ya daga kai zai Sha ya hango ta tana kokari neman wajen zama yayi kmr bai ganta ba yacigaba da abunda yakeyi har yagama yayi jifa da kwalin ya juya yana shirin shigewa cikin bedroom tayi gyaran murya tace Abdullah wajenka fa naxo kana kallona.abdullah ya juyo ya tsaya mata wani matsiyacin kallo, tasake cewa please ka zauna magana naxo nayi maka wani irin kallo yasake mata mai kama da harara yana nazarinta a karshe ya numfasa hade cizan lip's dinshi sannan yasamu kujera nesa da ita sosai ya zauna ,bbu kunya balle tsoron Allah faiza ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa dashi duk dai bai dago ya dubeta ba ,yajingaina da kujera yayin da kansa ke kallon sama cikin salo murya na Yan duniya takira sunanshi Ab..du...llahi..Yaya kake son inyi da rayuwata da soyayyar ka da takamani cikin farar daya , tun zuwana gidan nike binka Amman kai sam bana gabanka kasan dai iyayenmu sun rigada sun gama magana , Kuma mami ta tabbatar min da bakada wata mata nan duniya sai ni" ko kana tunanin tsallalakewa maganar mahaifiyarka ne ,ka auri..... Abdullah ya buga mata wata razananniyar sawa yana mai watsa mata mugun kallo how dare you talk 2 me like dat ,yana mai tsareta da manyan idanunshi masu firgita mutun bata ma kula da duk abunda yake ba sai sake birgeta da yayi "da kallon da ta masa na very serious man kiyi maganar da takawo ki kawai Amman Kar ki kuskura kisa mami a maganar ki.ok naji bazan sake ba Amman ina son kasani zan iya yin komai a kanka muddin burina zai cika Abdullah ya dakatar da ita dan Allah yimin shiru malama ke wawiya ina ce indai akai nane a she zaki mutu burin naki bai cika ba
Ta zuba masa Ido meyasa zakayi haka nifa ina so ka saboda zan iya sallama maka komai da kake bukata kaajiye komai muyi soyayyarmu Abdullah ya dinga Yi mata kallon mara hankali mike tsaye yayi itama ta Mike ta rike hannushi mamaki yasa yabi hannun nata da kallo da ta rikeshi ,yasa ta dauka ko yafara kamuwa ne ", gabadaya sai ji yayi ta fada jikinsa ta rungume shi tare da fadin wallahi Abdullah bbu wanda zai San abunda ya yafaru da sauri abdulla ya hankadeta wanda har sai da ta buge da kujera huce yake yana kallonta ta Mike da Kyar tana kallonsa hade da shafa kugunta "sake motso sa tayi am very sorry....ai bata rufe bakinta taji saukar lafiyayen mari a kicin ta wanda ya gigita ta maganarta ta tsaya cak na 2 second sannan ta make kmr ba ita ba ,ta sake kokarin yin magana yasake dauke da wani agigice take binsa da kallo da kwalakwalan idanunta kmr mayya" if you do any stupid I will del with u now get out from my site "Tayi murmushin karfin hali ok irin rayuwar da zamuyi kennan idan muyi aure ina son haka muddin zamu kasance matsayin miji da mata I said get out in my site "yasake fada cikin tsawa tsawa .
Tasake yin murmushi sannan ta juya tana juya masa mazaunai ta fice Abdullah yaja tsaki stupid girl kawai "ya fada sannan yabi bayanta ya sanyawa kofar key ya shige ciki ya duba agogon sa shadaya har ta wuce ya raya aransa duk inda zuciyarsa take tana can jikin Inna ,ta dade da yin bacci ba irin faiza ba, tsaki ya ja ya shige toilet ya sakarwa kansa shower ya gama ya dauro alwala don yanzu babban burinsa ya fuskanci ubangiji da matsalar sa ko zai samu saukin damuwar sa".MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......