19

1.5K 73 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 19

Sai wajen biyar na yamma bakin wakilan Abdullah suka iso  wanda har mlm abu yafita titi sai da aka nemoshi shidinma sheda musu yayi suna jiran baki ne daga ka'oje da tunin sunzo da kansu to haka suka koma suka sanar da dady "take yakira Abdullah byn ya tambayi lfyr jikinsa  yace ko yasan inda dagin Aisha suke a ka'oje ya sanar masa sannan sukayi sallama dady dakan sa sai da yaji gabansa fadi ZUCIYAR sa ta masa nauyi jin sunan   mlm dahiru shine matsayin kawun mahaifiyar yarinyar da Abdullah ke so" yayi shr ya fada duniyar tunani mai zurfi da bai san tsawon  lokacin da dauka zaune ba..... tabbas inda yadda Abdullah yasanar dashi mlm dahiru shima ai kawunsa ne sai kuma wani tunani na daban yazo masa..

    Washegari wajen karfe uku sai ga yusif da mlm dahiru tare da su dady gabadayan su " dady kam asubanci sukawa garin  ka'oje dan a can dady ya wuni duk yinin yau mlm abu bai yi  mamakin yadda hakan takasance ba nan da nan Mlm ya turawa alhj aminu,  shi kam mlm dahiru tun daga ganin zuwan  dady al'amura suka  karye daga gareshi, byn kowa ya hallara hade gaishe gaishe  sannan suka fara abunda ya tarasu da farko dai dady ne yasoma magana hakuri yabayar sosai game da cin fuskar da akazo har gida  akayi musu batare da nasaniyyarsa ba ,yace sai kuma dana ka'oje yau din naga kawuna shima yana daya daga cikin wakillan yarinyar duk da bansa yadda kuke dashi ba Amman hakan yamin dadi matukar da gaske ,  mlm abu ya numfasa sannan yace ai bbu komai haihuwace ta janyo haka sai dai maganar aure ne dai bbu shi a tsakaninmu domin ina son na tsirar da mutuncina dana diyata ko bakada komai yazama ka tsirar da mutuncinka  dady yayi shiru yana sauraron sa  Amman abun mamaki sam dady  bai ji haushin kalaman  mlm abu ba dan bai san iya yawan rashin mutunci dazo aka musu ba , dan ko shine zai iya yin fiyye da haka a yadda yakejin su teema aransa, mlm dahiru shiru yana kallon  Mlm abu rashin kyatawa bai ma duba girmanshi ba to maye amfanin turo yusif dayayi  Killa yayi haka ne dan ya tozartashi kuma  da dukkanin alamu bai san kowaye alhj ishaq ba, da dangantakar dake tsakaninsa da matarsa  yana son yayi magana Amman maganar taki zuwa masa shi kusan duk wunin  yau da mamakin ya wuni wai Abdullah dan ishaq ne kuma shi ke neman Aisha da aure uhmmmm ikon Allah kennan alhj aminu ma yasa baki Amman sam mlm abu yace shidai abar masa diyarsa bawai dan baya sonta da Abdullah bane  tunda dai  mahaifiyar yaro ta nuna  bata so gara a hakura gabadaya kar azo ayi abunda daga baya za'a yi danasanin , Aisha  ita kennan gareni  Diya  mace idan wani abu yasame ta bazai iya yafewa kansa ba ,alhj aminu yayi shiru shi hakan ma dade ne a gunsa dan yafi son Aishar  tazamo rabon dansa ce yasir ,,  falon  ya dauki shiru na wani lokaci yayinda kowane su da abunda yake kissamawa ransa " dady ne yayi godiya tare da mimika musu hannu sukayi musabaha sannan ya Mike yace zai koma Amman zai  sake dawo..tare suka tafi da mlm dahiru yabada izinin amai dashi  ....shi suka wuce tare da securities dinsa...

koda mlm abu yashiga gida a daki ya tadda innarsu taci kuka  har tagaji  tsaye yayi kikam daga inda yake da sauri ta dago Ido tana bin mlm da kallo shima kallonta yake yana sansanin  dalilin kukan nata yadda tamasa shiru shima haka yayi ya karasa inda kayansa suke ya canza zuwa wasu daban  yace mata shi yafita sai yanzu tasamu karfin iya   bude baki tace mlm...yadan ja ya tsaya tace  har sun tafi ne?...da kai ya amsa mata kusan  yasan mezata tambaya gaba shiyasa yayi saurin ce mata bari na dawo zammiki bayanin komai Amman kibar kukan nan haka  .....tanan zaune har bayan sallar la'asar takasa tashi tajin kmr wani abu na shrin samun danuwanta sanadin hana Abdullah Aisha ko shi Abdullah din ,. ,  Jin shiru inna yayi  bata fito ba Kuma alhalin tasan yau ba litinin ba ko alhamis saboda idan inna tana azumi bata fiyesan zaman daki  ba. yasa Aisha shiga dakin da sallamarta ,zaune ta taddda inna tajingina bayanta da gadon dakin ta hade hannuwa waje daya idanunta na kallon celling dakin ta dade tana kallon innarta  kafin daga baya takarasa kusa da ita ta zauna  tana karewa innarta kallo kusan duk kwanakin ta lura kmr  bata cikin kwanciyar hankali hakan yasa  danganta  hakan da   maganar aurenta ne yasa inna shiga wannan hali, ta dade zaune Amman duk inna batasan da shigowar ta ba, ta bude baki  cikin tsanyi. muryarta tace innarmu........jin amon muryarta yasa inna yin frigigib.   tadawo haiyacinta da sauri tasa gefen zaninta   taso goge siraren  hawayen dake  diga ta gefen idonta , Aisha ta girgiza kai tasa hannuta  ta kamo na innna cikin nata kusan second biyar suka dauka a haka Aisha na kallon innarta da san sanin abunda kesata kuka sannan shine karo na biyu da taga zubar hawayen innarta runtse ido tayi cikin sheshekar kuka tace  innarmu dan girman Allah ki daina sawa ranki damuwa akan zance auren nan nifa dama can ba wai ina son auren Abdullah bane balle ki damu kanki  kuma da hakan ta faru ma nafi kowa Jin dadi rabuwarmu  Amman kiyi  hakuri nasan sanadina akazo har gida aka cimuku mutunci keda baba sai kuma ta fashe da matsanancin kuka mai rekitarwa ......itama inna hawayen take har yanzu ta dammke hannun diyarta da kyau tana jin tautsayinta komai nata bata cika damuwa dashi ba balle ya daga mata hankali, tace sam ba  shine yake sani kuka ba kuka na daban, to innarmu me ke damunki tun kwanakin baya  nike ganin cikin wannan hali dan Allah kisanar dani kinji..
...ta marairaice fuska. inna tayi shiru tana nazarin diyarta ta tasa hannu daya tana share mata hawayen fuskarta tace kibar kuka  tacigaba da goge mata hawaye, ta sauke ajiyir zuciya ta zubawa inna idanunta tajin kaunar mahaifiyarta na ratsa mata kowani gaba ta gangar jikinta ita fa banda soyayyar uwa da uba da yanwanta bata San wata aba soyayya ba.... inna ta numfasa har yanzu ita Aisha take kallo tanasan tasan damuwarta, ita da kanta zata so ta sanar daita  dan bata da sama da ita ita rayuwar ta dan  bata da kowa duk duniyar nan  sai tarin  yan'uwa   inna ta kira sunanta   Aisha..... sai kuma tayi shiru....nawani lokacin sannan tace ki kwantar da hankali bbu abunda ke damuna "in ma akwai kece mutun ta farko da zansanarwa duk duniya wa gareni byn ke banda yaya ko kanwa macce dazan kaiwa kukana dan'uwa daya gareni shi kuma yamin Nisa" dan haka tamkar banda kowa haka nikejin kaina" sai ku da Allah yabani dan haka bana son naganki cikin  damuwa dan  ke Yar dangi ce ga da tarin yan'uwa kuma masu tsananin sonki takarashe maganar ta tana dariya har taso bawa Aisha itama ko tadan murmusa tace yauwa diyata ko kefa  maza tashi ki daura mana sanwa yamma tanayi ,a tare suka Mike suka fita Aisha tayi kicin dayake ita tarigada tayi sallar la'asar yayinda inna ta zari buta tayi make wayi......

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now