2

3.1K 101 2
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 2

Sun rufawa dan taxi baya har da salis dake cikin dayar mota gasunan sune har badariya ,har sanda aka sauketa da inda tashiga duk akan idon abdulla har kofar gidan suka isa sukayi parking layin shr bbu wata hayaniyya haka gidan data shiga ba wani babba bane sosai , sun sami kusan mintina goma kafin suga wurgawar wani. daga can km sai ga wani yaro dan kimanin shekaru goma , zai shiga gidan salis ya kirawo shi ,byn yaron yazo yake tambayar sa yarinyar data Shiga gidan ko yayarsa ce.yace A'a ai shi almajiri gidan ne , salis yasake ce masa ,to ko yasan yarinyar gidan yaya sunanta , ya Kuma cewa ai matar gidan batada babbar ya duka yaranta kananane  Kuma Maza guda biyu an Kuma tafi dasu makaranta tun dazu , atare suka gane itama bakuwace  kennan, salis yace to idan kashiga kace ana sallama da bakuwar datashigo yanzu yaron ya shiga bai jima ba ya fito kai tsaye yace wai bakuwar tace dan Allah kuyi hakuri ku tafi ,dama tun da yaron yafito abdulla ke kallonsa yana jiran yaji mai zata ce har ya juya zai sake shiga gidan salis yace kace mata wai mai taxi din dayakawotane yace tayi mantuwa .yaro ya amsa yashiga musa yayi dariya aciki ,ya juya musu kan motocinsu yana daidaita su,ai ko bai wani jiba sai gata ta fito sanye cikin riga da siket na less marun colour mayafin abayar tayafa akanta  da alamun kayan ne acikin abayar dazu "sai yaga tasake masa  kyau fiyye da dazu suna yin ido hudu da abdulla da ya zuba mata idanunshi duka sai tabi ta diririce tana kokari fito sosai don ta hango mai taxi dake kiranta , tsammaninta ko zai ce bata bashi kudinsa bane ita dai tasan tabashi Kuma bata manta komai ba,kwata kwata bata ga alamunsa ba    sai kawai tajiyo  gyaran murya daga bayanta abdulla ne yayi nan da nan salis yace bakiji ba gashi nan fa , ahankali ta sake juyowa duk tsammaninta mai taxi ne ,tana juyowa abdulla dake jingine da jikin mota ya harde hannuwanshi a kirji ya zubamata manyan idanunshi yanabinta da kallo  ganin duk ta daburce yasa yadan saki murmushin har gefen kumatunsa ya lotsa , salis  yace  madam ba gaisawa sai ki leko Kuma zaki  koma . kallonsa kawai tayi mai hade da harara ,ta sake juyawa ta shige abunta salis yadafe kai yayin da abdullah ya cije lebansa yana mai runtse idanunshi,salis  yace  ta leko ta hararemu ta wuce abunta . Hade da cewa  kai dagani  madam fa  za'a dama daita . abdullah ya dubi agogonsa muje kawai salis ai munga inda tazo yashiga suka wuce  .

Tana shiga aunty Maryam tace me kika manta tace bakomai  wlh aunty, irin banzayen kwarorin nan kawai" sukayi me kwarorin?inji aunty su dai nagani awaje  aunty Maryam tadanyi dariya hum kedai baki da kara akan Maza .

Yana idar da sallah yashiga part din maminsa yasame ta itama ta idar da sallah duk da agajiye yake yadan zauna kusa da maminsa ,sister dinshi amina ta Miko masa fresh milk a Kofi ya karba ya Sha ,ya bata cup ta wuce kicin yace mami zandan fita bazan dade ba dan ita mami irin mutane nan ne dabasason arabeta ko ita  tarabi mutun haka ko mijin bata barinsa ya sakewa da kowa inba ita da yayanta ba,mami takarasa jan carbi ta shafa ta kallesa tace Amman kasan salis yatashi daga aiki ko,ko a haka zaka fita daga kai sai musa yace ni kadai nike son  fita ba direba mami tace no abdullah banason fitarka kai daya ga dare gashi kai bawani sanin gari kayi ba sosai" kayiwa salis waya kawai yazo ku je tare abdullah yadan   langwabar da kai yace mami banason takurasa cikin iyalinsa ,tunda yarigada ya tafi a kyaleshi nima ba dadewa zanyi ba ta kada kai ,shi kennan Amman banso ka dade a waje" yayi murmushin ya Mike bazan dade ba har zai fita tasake cewa yanzu kai kadai zaka fita kennan ahankali yace don't worry mamina I can drive my self tace agaida sagir zatonta can zashi  taci gaba da abunda takeyi yayi murmushin ya fita ,.

Cikin natsuwa yake tuki cikin dark green din  benz har ya iso badariya   dai dai kofar gidan dazu yayi parking cikin sa'a mai gidan ya tarar tare da wani bako ya isa yayi musu sallama tare da gaishe su , sannan yadan koma gefe basu jima ba sukai sallama bakon yashiga motarsa ya wuce .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now