46

1.3K 70 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 58-59

Tunda suka rabu da Abdullah duk daren Allah sai tayi kuka rashinsa musamman inda tazo kwanciya .
gara ma da rana idan tana tare da mutane bata cika tuna shi sosai ba.
ita da kanta bata sanda soyayyar Abdullah tayiwa zuciyarta mummunar illa ba sai a wannan lokacin .
  barin ma irin  rayuwar da take ciki ayanzu.
yasa tafi tuno shi sosai akan da musamman yanzu  daga ita sai inna matar mlm dahiru .

mlm dahiru yawanci shi ke siyo mata duk abinda take son ci, in da har yafi can gidansu a kebbi kennan.
Duk abinda take  bukatar za'a tafi nemo mata shi.
  kuma ba laifi takan dan   cin abinci inna .

da kansa mlm dahiru ya matsa a kaita asibiti da kyar dai Aisha ta yarda suka je .domin daman acan kebbi bata son taga Dr salim shiyasa taki bin aunty suje .
har aka  mata fadan rashin zuwa asibiti inda akarshe suka rubuta mata magunguna sosai dazata dinga Sha.

Da yammacin ranar tana zaune  mlm dahiru yashigo taga ankama dan marakin anfita dashi aka siyar.
wai ashe magani  za'a a siyo mata da kudin  .

Karo na farko data bude handbag dinta da minal ta bita dashi tun ranar da Abdullah ya saketa ,.

ta zazzago abinda ke ciki har da check din da Abdullah ya taba bata lokacin suna Germany na miliyoyi kudi .
ta zuba musu  kudin jiki ido ya isa ya kawo maganin karshen duk wani bbu .
Amman ita basu take so ba kuma  basa birgeta tafison sanya Abdullah   kwayar  idanunta .
yafi komai mahimmanci a gareta.
ta tuna rayuwar da suka yi dama haka kawai  lokacin sai tarinka jin zaman su  ba me dorewa bane.
saboda ta koina abin bai zo daya", kawai taji hawaye ya shiga bin fuskarta . Tana kukanta
Inna ta leko tace mata zata shiga makwafta tayo musu barka" dayake bbu wuta a dakin  sai Yar fitilar kwai " yasa inna bata fahimci abinda take yi ba.

tana fita kuwa ta sake barkewa da wani sabon kukan tasa hannu ta shafo cikin nata tace ko yaya Abdullah zai ji idan yaji zata haifa masa da ko "ya ? .
,Ta tuna wani kokarin can da suke American ya taba ce mata Aisha idan kika haifa min Yar bby mace zanyi ta ttalinta sosai zan koya mata gayu " ita kuma tana kwance akan cinyarsa  tana dariya .
yace Allah musamman idan nasamu tayo kama dake ..Kai ai sai wanda nagadama zan bawa  tayi, ta sake yin   dariya tace to idan namiji aka haifa fa ?
     kake wannan abun yace kinsan ance  duka gadon haihuwa yawanci daga na namiji ne.
to kinga ni Kuma duk gidanmu matane ni kadai ne namiji .
dan haka killa nima da mata zan fara.
sai kiga wata rana nima  ana min layi a gida wallahi sai na duba nutsatten siriki .
Tasa dariya tace uban "ya" kennan yace yes haka ne .
yana dariya itama tana yi .
To sai dariya ta kubce mata tamkar a lokacin suke maganar tana kukan tana dariya.
har tadan kware kadan ai ko nan da nan ta fara Tari ta fito waje da sauri tana yunkurin amai .
ai kuwa sai data amayar da duk abin ta ci tana haci ta kwanta anan kasa gashi  inna bata nan .
  tana kwance kusa da Aman sai data huta sannan ta mike da kyar ta dan kora ruwa sannan ta rarrafa  ta koma daki ta kwanta .
aranta tace kowa yazo yaga jikinta ko dazu ma daga zariya dangin babanta sunzo .

Amman Abdullah yaki zuwa yaganta shikenan Abdullah da gaske  ya daina sonta.
a da ko dan begewa tayi sai yaji kmr ajikinsa yaji .
idan rashin lafiya take"
yi yake tamkar  wanda zaiyi karamin hauka.
tun bata damu dashi ba har yazo yakoya mata yadda zata so shi .
gashi da shiga rai  ko yaya kake tare dashi sai yasan yadda  ya faranta maka.
Amman lokacin daya gashi yanzu ya mata ciki ya barta da damuwarta ita kadai wanda ahalin yanzu tafi bukatarsa fiyye da komai.
ita Tama sanya shi  a idanunta koda bazai cigaba da sonta ba .
tayi kuka sosai .
abin tausayi ita da kanta bazata iya tuna sanda tayi kuka irin haka ba.
tayi fushi da Abdullah da bakinta tace in Allah yaso ko waye Abdullah tabar shi .
ahankali take cewa Abdullah  na barka na barka dama kai kasa na soka yanzu kuma tunda baka sona ka barni.
nima na barka  in Allah yaso har abada bazan kuma barin sonka yay min illa ba.
   har inna ta dawo ta leka ciki tayi kiranta  Amman shiru batayi magana
ba .
inna ta dauka ko ta dade dayin bacci ne shiyasa ta kyaleta.
ita ko har lokacin hawayen rabuwa da son Abdullah take da tunaninsa .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now