21

1.5K 76 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 21

Cikin gidan kaf bbu wanda yasan da zance yuwuwar auren Abdullah ,hatta mami da kanta illa iyaka taga ana ta gyare gyare ta koina  part din  Abdullah kuwa gabadaya sai da aka canza masa tsari ,to mami dai tasan ana yawan yimusu gyara kusan duk karshen shekara Amman ba kamar wannan ba domin yadda ta ga dady ke rawar jikin bari da kudi a cikin gidan tasan wannan ya zarce gyaran kowace shekara ,zuciyarta tarinka mata zargi iri iri  koda ta tambaye sa game da gyaran sai ya sanar da ita kawai saboda Abdullah ne zai dawo wani sati ..
    Mami tariga tasan yadda Abdullah din yake da matsayi a gurin dady shi yasa bata bawa ranta komai ba Amman duk da haka tasake fahimtar Abdullah ya kara karfi a zuciyar ubansa...

   Faiza kuwa kmr tayi karamin hauka dan dadi tawa mama hafsa waya tasanar da ita dawowar Abdullah har gidan gyaran jiki faiza taje aka mata duk dai akan dawowar Abdullah Mama hafsa daman tayi kwana biyu da tafiya dan haka tana jin wayar faiza tayo shirin tahowa...

Duk wani tsari da shiri sai da dady yakusan kammalawa da shi dan hatta AV na daurin aure ya fito duk inda zaije  tsakanin danginsa dana mami yan'uwa da abokan arziki kusan kowa ya isa gareshi hatta sokoto ya aika sabanin da aka samu ranar da mm hafsa ta taho a ranar katin ya isa dan haka itama batasan da zance daurin auren ba har ta iso ...

Dady yatafi Germany ana sauran kwana shida daurin aure aranar  da ya sauka Abdullah yabar hospital da yake zuwa wani shiryayen plat house wanda Dady ya siya da sunan Abdullah tun ba yau ba" bawani babba bane Amman tsarinsa yayi matukar birge Abdullah a daren  dady ya zubewa Abdullah AV din daurin aure cikin sanyi jiki Abdullah ya janyo ya fara dubawa dady yacigaba zamu koma zuwa  jibi da yamma domin ranar jumma'a yakama daurin aure mun gama magana da doctor  jack idan an daura  auren upper week zaka dawo tare da yarinyar nan acigaba da duba lafiyar ka "dan haka wannan gidan na siya da sunnanka ko byn Raina cikinsa ne zaka  zauna idan  ka dawo ba'a asibiti ba doctor zai dinga zuwa nan yana duba lafiyar ka ... Dady yadan tsagaita sannan yacigaba akwai bukatar a siyawa yarinyar nan  kayan sawa wanda zatayi amfani da su anan domin can mahaifinta ya hana ayi mata ko dai dai da zani daya ...

Abdullah bai gane a yanayin da yake ciki ba dan haka hawaye kawai yaji na farinciki yana zubo masa wanda rabon hawaye a fuskarsa ya jima kai bama zai iya tunawa ba "ya kwanta nan gaban dady yana Yi masa godiya dady ya dafa kansa yace A'a Abdullah ba komai kai ma Allah yayi maka albarka sanadin ka na samu cigaba a rayuwa wanda bazasu lisafu ba.. farinciki Abdullah yaki boyuwa bai san yadda zai misalta wannan ranar ba ,daga can kuma ya dan natsu har da dan tsoro a fuskarsa ,dady ya fahimci sauyawarsa ya tambaye shi cikin sanyi jiki yace  dady mami fa?..

Dady ya numfasa ya riko hannunshi cikin nasa  yace Ab..dul..lah..maminka zata so duk abinda kake so ni nasani ko ba dade  balle ita wannan yarinyar dabance acikin zuciyar Abdullah dinta ,kuma gashi yar'uwa Mafi kusanci agareka Abdullah ya zubawa dady Ido dan bai fahimci komai dady yake nufi ba  in baka manta ba na taba sanar da kai ina da kanwa maimuna Kuma ta taba zuwa   lokacin kana oxford to itace mahaifiyar. Aisharka ...jikin Abdullah yayi sanyi sosai saboda tuna yadda matsayin dady yake Amman yabar su cikin halin rashi Amman me shi duk yadda takasance daidai ne awajenshi dady yace  babu  abunda zance maka Abdullah saboda kai ne tsanin sake hadani da yaruwata  har yanzu Abdullah dady yake kallo. dady ya numfasa sannan yace  ni dai  burina ka kwantar min da hankalinka maganar mami kaajiye a gefe bbu abunda zai faru kacigaba da farincikinka kaji .. Abdullah ya daga kai dady yace  yauwa ya dubi agogon dake manne a bango  yace kaje ka kwanta goma tayi idan bbu wani dalili bana son ka dinga wuce goma baka kwanta ba Abdullah ya amsa ya Mike yashige ciki dady yabishi da kallo har ya bacewa ganinsa sannan ya sauke ajiyer zuciya hadisin ne guda na annabi (saw)  JUBULATILKULUBI ALA MAN AHSANA ILAH  cewa zuciya an Gina tane akan son me kyautata mata , Abdullah bai san musu ko wani gajiyawa akan iyayensa hakan yasa zuciyarsu takafu akan soyayyar shi" dady ya lumshe idanunshi yana  tuna can wani zamani daya shude baya da abinda mahaifinsa ke yawan gaya masa yace ishaq Allah ya albarkace ka kai ma Allah  yabaka me Yi maka yadda kayimin dady ya bude Ido yayi murmushin ya shiga yiwa iyayensa addu'a ..

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now