48

1.2K 64 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Nagode da yadda kuke matukar sona da kaunar novel din nan  ,Kuma  kuna Raina domin kuwa KAUNACE SILA komai dan kuna cikin kololuwar zuciyar Bagudo.
kuna ina 🗣🗣🗣🗣🗣yan ZUCIYAR MASOYI FANS ku matso kusa this page belongs to you ol na bakushi free of charge kuyi duk yadda kuke so dashi.  na kune, haka ma Bagudo takuce har abada ana mugun tare irin sosai din nan 🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝

Page 61-62

Abdullah yayi shr  ya jima zaune a bedroom dinsa ya gane mama hafsa  duk yadda yaso ya kauce mata  sai ta kure shi.
ta  wani koma kmr itace ta haife shi .
ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa Amman nasan yadda zan bullo  musu ya fada aransa.
ga dukkanin alamun rashin Aisha yana nema ya zama gaske  .
shi Kuma ya rike alkwarin byn Aisha bbu wata ya maccen da yake ganin zai kuma kusanta .
dan haka ya gano wata tafiya  a gabansa a tun safe .
ya samu sako ajikin system dinsa cewar company da suke son budewa a South Korea wanda har suka kirasu interview kwanakin baya Denmark.
suna bukatar wani wakili daya wanda zai je ya zauna a can har tsawon watanni bakwai zuwa tara ko shekara har sai komai  akammala  .

Dan haka bbu wani bata lokacin  ko jin wani abu kawai  Abdullah ya wakilta kansa .
dan haka ya tura sunansa da komai nasa akan shi zai yi tafiyar .
byn dawowar dady kennan" a yadda yake ganin al'amarin sai wani ikon Allah yasake rayuwa da Aisha.
jikinsa har ya  fara  hakura da rashin ta.
dan haka ko anyi aurensa da faiza bazai bari su san da zancen tafiyar ba sai dai su shafa Suji shr .
kuma muddin yashi tafiya .
Ko duk duniya zata hade ba zai tafi shi kadai ba .
  kafarsa kafar  Aisharsa sawa zaiyi a sato masa ita kawai .
Ba zai yarda yayi wani rayuwar aure da wata byn Aisha ba .
dan haka yana tafiya zai manta da wani auren faiza dake kansa.
in tagaji da jira tasan yadda zatayi da kanta .
in baya ga iyaye ma da idan yayi gaba.
ya tafi kennan sai dai idan yaso lekowa.

Tunanisa ya dawo kan kujerar sa ta office idan yayi tafiyar nan .
tunaninsa wanda zai riketa da amana yayi shr yasan dady zai iya hadawa   har  nasa kujerar.
Amman yasan ayyuka zasu yi masa yawa sosai Dr sagir yake dubawa a yanzu shima yana da aikinsa.
Amman yana da kyau yayi wa Dr sagir wani abu mai mahimmanci a rayuwa.
saboda Allah  shi ya hada shi Aisha Amman ta  dalilinsa  .

Faiza ta kankane komai nata da duk wani abu da akayi oder sa ta juye shi a part din Abdullah .
kayan  gado dana kitchen iyakar tsaruwa komai part din ya tsaru yadda ake so matuka gaske.
cikin abinda yabawa mutane mamaki gabadaya ta tare a part din tun ba a daura auren ba.
tun dawowarta daga kasar waje sau biyu ta taka sokoto.
shima direba ne yakaita kuma a ranar ta juyo hatta kawanyenta na can daidaiku ta gayyata .
dan haka duk bikin da'ake a sokoto bbu amarya suke gudanar da  komai.
amarya tana  can gidan mijin nata.
dan Abdullah yabar part dinsa acan take kwana mutane kuwa suka samu abin fadi sai surutu ake ..

Wata yayar baban faiza ce tace kai jama'a ai sai a zage mu koma ana kan zaginmu .
ace amarya ana biki a gidan ubanta ita kuma tana ca.  
har takai kanta tana can gidan iyayen miji ai ba zai yiwu ba wlh.
dan haka  sauran kwana biyu a daura auren  tun asuba suka baro sokoto zuwa kebbi tace dole su tafi da faiza a kalla dai ta bari ko daura auren ne  ayi tana can.
idan yaso ta biyo yan daurin auren.
da kyar da sudin goshi dai aka lallaba faiza ta biyosu duk da tayi  ta bata musu lokacin "tana zumbire zumbire don da basu sameta ba a gidan taji labari zuwansu.
bazata dawo ba ,sai dai suka raci zaman su .
, su koma byn ta hada komai nata ta kulle part din Abdullah ta bawa  teema ajiyar keys din saboda kada ta tafi dasu can a faki idanunta a dauka a dawo a taba mata wani abu .
sai byn sallah azahar sannan suka bar kebbi daga ita sai kaya kala biyar


Tun. Karfe uku ,na ranar har biyar Abdullah yana tare da Dr sagir .
Dr sagir ya kalleshi yace haba friend har yanzu baka saduda ba  kennan  jibi ne za'a daura yakamata ace  ka dan ajiye wani abu .
tunda dai shi aure yarigada ya zama dole kawai ka saki jikinka , a dan yi wani abu kada ma ka sake ka fito da damuwarka a gane .
,tunda duk aure sunansa aure .

Abdullah ya kalleshi ya girgiza kai yace wani aure sunan sa ne kawai aure Amman ba aure bane , yanzu zaka hadashi da auren Aisha koda nake cikin damuwa a lokacin .
Amman wlh Allah Allah nake a mallakamin ita na ganta  a kusa dani.
    wannan kuwa baka ji yadda nake jin zuciyata ba kmr zata buga haka nake ji.
sannan kace na daina damuwa ina... Doctor nayi asara fa sosai dana rasa Aisha ,.
ina sonta ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan gaya maka ba .
ina jinta a cikin naman jikina , .
doctor ban san haka so yake ba sai yanzu kullum na tuna yaya zataji lokacin da aka bata takardar sakina ..
sai naji wani daci ya tsayamin a makogaro. Sai danayi kwana uku bana jin test din komai Idan naci.
why why da zan dauki aurenta dana wata daidai ai kai ma kasan fada kawai kayi.
Dr Aisha yarinya ce bata san komai ba na rayuwar duniya ,baya ga zama gaban innarta .
,sai da Allah ya hadamu ni koyawa Aisha koma ciki harda yadda zata soni .
baka ga yadda nayi rayuwa daita ba komai a nutse take yinsa .
Ta yaya zan iya manta ta haka .
Abdullah ya runtse idanunshi sosai.
hakan ne yasa Dr sagir yaji  kwalla  ta yakawo a idonsa .
nan da nan ya wayance dan kada Abdullah ya Ganshi.
Shi  kuwa Abdullah samma bai ma lura dashi ba.
yace Amman yaya zanyi doctor dole ne ma na hakura daita .
gobe ko jibi iyanzu an daura aure na da wata ko daga baya Aisha ta dawo  min cewa za'a yi  duk abinda nayi daita dole ne nayi da faiza .
ni Kuma wlh bazan taba iya rayuwar aure da wata ba bayan Aisha .
sai dai wani ikon Allah shine naga da haka gara nasawa Raina hakuri shi zai fi min sauki.
tunda safe yau dana tashi  jikina yake bani komai ya kusan zuwa  Karshe .
na sawa Raina ba zan iya yi komai da wata macce ba .
to Aisha ma na hakura zanyi rayuwata a haka bbu ita ballanantana wannan .
kawai ba komai ba ko.....
    Wayarsa ce ta katse shi tana  kida .
Sai da tayi kara sau biyu yana ji .
sai daga baya Abdullah yasa hannu ya dauka ya kara a kunne.
daga can daya bangaren dady na saukowa daga matattakalar jirgi yace Abdullah kana ina ne?
Jin muryar dady tasa Abdullah ya dan natsu yace ina nan gida .
dady yace to ai mun iso yanzu ko kai ko wani a samu mai zuwa dauko ni yanzu  .

Bye bye faiza👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻

MMN SUDAIS

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now