18

1.3K 78 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 18

Ran dady yayi matukar bacci sosai game da bayanin da mami keyi masa ,shi duk bai san abinda ya faru ba Amman shi duk ba wannan ya Dame shi ba, lafiyar dan nasa ,kansa a caji yake ga rashin lafiyar Abdullah ga zirga zirga ta sha'anini kafa company dinsu da suka samu nasara a Denmark ga rashin Abdullah da gurbinsa daya bari domin wani abun dole sai Abdullah hakan bai hana dady tsallalakewa ya dubo lafiyar Abdullah din nasa ba bayan kwana   biyu da dawowar mami...

A sa'a dady ya sauka a Germany domin a ranar ake warwarewa Abdullah bandejin karayar dake kafadar Abdullah din hakan ne yasa dady  ya sawa ransa Abdullah yana samun cigaba a lafiyarsa har ma yaji dadi sosai da yadda ake kula da shi dan haka kwanansa uku ya juyo tare da minal bayan ya kara sakin kudi sosai akan maaikatan asibiti akan lura da Abdullah ,dama dai bbu wani mai jiyya dake zama dan Abdullah kadai sai securities guda biyu RK da salis...

Washegarin da dady yadawo daga Germany mama hafsa ta iso ita da faiza  tare da shiryayen shirinsu duk akan Abdullah a rashin  sa'a suka tarar Abdullah din ma na can gadon asibiti a wata uwa  duniya ..

To duk yadda mami tayi da dady akan tana san sake komawa dubo Abdullah dady yaki , Mama hafsa kawai ya sanyawa hannu akan taje duboshi , Amman faiza ta zauna ,faiza kuwa a yadda tazo a shiryenta taci alwashi bata kara komawa sokoto sai tare da auren Abdullah a kanta ,dan haka ko ba dade tana nan tana jiran warkewar Abdullah da dawowar sa....

Tun bayan gaisawa da Abdullah yayi wa mama hafsa bai sake tanka mata ba tun zuwanta ,komai tace sai dai yayi shiru koda maganar ta na bukatar amsa , saboda a ganin shi kamar yadda yaji daga bakin mami ita mama hafsa tana daya daga cikin wadan da suka haifar da rikicen dake kwalkwalwarsa ,dan haka tana barin gurin yabada umarnin bai san sake ganin wani yashigo dakin da yake idan kacire maaikatan sai dai ko daga cikin mahaifansa  ....

Bbu yadda mama hafsa batayi na san ganinsa  Amman fur aka hanata ance yana bukatar hutu ta ciza yatsa na ba adadi. daganin wautarta tun farkon xuwanta saboda a yadda taga Abdullah laga laga a kwance shi yasa take son ta fara aiwatar da shirinsu , kmr yadda sukayi da faiza , Amman sai gashi daga gani daya tun bata fara aiwatar da komai ba ,an datse sake ganin Abdullah din ta buga ta buga Amman sam aka hanata ganin Abdullah" haka ta hakura domin visa dinta ya cika na dawowa dole ta taho batare da tayi komai ba daga cikin abunda taje da niyyar Yi.....

Watan Abdullah biyu da kwanaki dady yasake biyo jirgi ya ganshi yadda yaga Abdullah yayi matukar razanashi ya tsorata tamkar ba'a asibiti yake ba , Abdullah ya rame sosai ta yadda har kwayar Idanunshi sun nuna haka , sannan ga wata muguwar kasunba daya tara ,dan ya  hana a gyara masa tamkar ba Abdullah din dayasani   ba mai matukar son tsafta da kyamkyami...

Aranar dady ya gana da babban likitan dake kula da lafiyar Abdullah a office din doctor  jack suke a zaune dady ke tambayar yadda yaga jikin Abdullah  yakasance doctor jack kwararen likita ne da ya nakalci cututtuka da dama ,yayi gyaran murya yace shi duk wata cuta da Abdullah yazo da ita iya bincikensu ya samu saukinta koma ya warke musamman daakayi saa Abdullah din bai da kyan jiki  to abinda yake damunsa a yanxun kirjinsa Amman akwai magunguna a yanxun daake son Yi masa amfani da su.

Sai dai Abdullah ya hana zuciyarsa sakat da yawan tunane tunane,wanda  iya bincikenmu Abdullah yana tattare da damuwa aransa wanda sakamakon yawan damuwar da zuciyarsa take har yasa ZUCIYAR ke barazanar kamuwa da wani ciwon na daban .,kirjin dady ya buga da karfi doctor jack yacigaba munyi kokarin ganin ya'ajiye duk wani damuwa saboda ganin yadda lafiyar sa take yin kasa ni kaina na zauna dashi ya kai sai hudu Amman har yanzu bbu wani canji ,shi yasa muka dakatar da shan maganinsa mai karfi dan gudun faruwar wani abu. doctor ya numfasa yace Amman yanzu abinda naga za'afarayi wanda zai ceto shi daga hakan a binciki abunda ke damunsa a kawar masa da damuwarsa dake damun zuciyarsa , Allah sarki dady kasa ko motse kasayi yayi akan kujera yace to doctor kmr yaya kake ganin za',ayi ciki harshe turancin duka suke magana doctor yace abunda yafi a bincika idan wani abu yake bukata ayi masa idan Kuma damuwa ce yake tare da ita a kawar masa da ita yin haka kadai zaisa yacigaba da karfan magani na karasa samun lafiyar sa ,domin duk kan masu yi masa hidima na bincike su bayani guda daya ne , kawai yake cewa  abinda ya  dame shi, ko yake bukata wanda Kuma bbu naganin sa asibiti  ..

Hankali dady a tashe yabaro office din doctor Abdullah ciwon zuciya INA..... yana ta nanata hakan a ransa to a dare sai da Abdullah yadawo tsaf da shi komai yayi neet a jikinsa , dady yana kallonsa yana cin abinci yana sake nazari akansa yana Jin tautsayi dansa har washegari suna manne tare duk wani zirga zirga ta sha'anini aiki bai kai mahimmanci zama da Abdullah ba a wajen dady ,Abdullah yasamu natsuwa kadan yaji dadin zuwan dady ,wanda har da kansa dady ya fahimci hakan ba kamar farkon da yasame shi ba ahankali dady ke bincikawa me  ya sawa ransa har da yake son jefa shi cikin wani hali,ka tausayawa dadynka  kasanar dani damuwarka bakada sama dani duk duniyar nan nima haka na jure abubuwan da dayawa game da rayuwa Amman bazan iya jurar rashinka atare dani  ba ya kamo hannushi cikin nasa yana masa duban ina sauraronka  Abdullah dai yasan dady yana da fahimta  abu yana da Kuma  saurin ganewa dan haka  baiyi shakkan  komai ba yadda yagayawa maminsa haka ya gayawa dady har zuwa jenyewar da yayi na auren Aisha dan ba yadda ya iya ....da kuma fushin da mami tayi dashi ... Dady ya zubawa dan nasa Ido sosai yake kallonsa ya damu da fushin da mahaifiyarsa tayi dashi , Amman bai sani ba itama mami tana can hankalinta da ranta suna kan Abdullah kullun cikin maganarsa take.. matsalar dai can gurin yarinyar da iyayenta da akaje aka ciwa mutunci ....

a fili dady ya kira sunnansa yace Abdullahi...
kana son yarinyar nan Aisha har yanzu?
      "A firgice Abdullah ya dago da sauri yana kallon dady hade da mummunar faduwar gaba, ZUCIYAR sa ce tashiga dokawa da sauri da sauri yadan jigina da gadon da yake zaune akai yayin da har yanzu hannushi na cikin na mahaifinsa ,yasake  kallon dady da kyau yana son karanto wani abu yadda yaga idonsa bbu wata zolaya ko wasa a cikinsu kuma kusan koda yaushe a hakan yake ,ya kau  da kai gefe ya fara inda indar magana yace da..dy mami bata son.....that is not the answer to my question I said do you still love her ....cikin tsanyin jiki Abdullah yace ina...ina sonta sai dai ma...hannu dady ya daga masa ya isa shikenan abinda nike son ji daga gareka yacigaba da yi masa wata maganar a hankali yake sake nazarinsa..
     Tun yinin biyu nan da sukayi da dady  sai ya kasance kullun cikin zirga zirga dady yake a nan cikin Germany sai dare zai kasance tare Abdullah wanda har Abdullah din yadinga mamaki ,kwanan Dady takwas tare dashi a daren da zai baro shi ya kara nuna masa barcin ransa Sosai akan wayan tunanin dayake yawanyi ,da bakinsa Abdullah yayi wa dady alkwarin ba zai sake ba domin yasan barcin ran dadyn nasa ,a hakan ya baro shi da cewar next week zai dawo...

Ta zubawa takardunta na makaranta da aka karbo mata idanu tana Jin daya daga cikin abunda ke sanyata farinciki kennan a Yan kwanakin nan, Amman kuma tun a jiya da safe da yaya umar ya shigo yana yiwa inna bayanin zuwan mahaifin Abdullah abin ya tsaya mata a rai dan tasan dai koma meye magana ce a kanta ..inna kasa zaune tayi  kmr tayi tsuntsuwa taganta alhj ishaq taji tana son taga danuwanta har gashi  bakin basu tadda mlm abu a gida ba kasancewar da wuri suka zo gashi duk an tura koina bayanan dan haka dady yabar sakon a yau zasu dawo  shi yasa ta natsu a daki haka nan Kuma shima mlm abu yau tun safe yana gida sannan Kuma tun safen ya tura yusif yaje ka'oje yazo da mlm dahiru to har yanzu sai dai bbu yusif din bbu baki daga bangaren Abdullah duk inna tabi  tadamu dan tana son sake ganin danuwanta ita dai banda mlm da kuma tana da  cikakken karfin  iko akan Aisha  zata so ayi .....

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now