50

1.8K 72 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 65

Gabadaya ya rike hannuwan Dr sagir yana dariya.
yace doctor na taba gaya maka nayi mafarkin ni da Aisha muna tsakiyar macizai sun kewayemu" har wani me kyalli a cikinsu ya howa kaina ya sauka ya koma jikin Aisha daga nan na farka.
sau uku ana gaya min wadannan macizan dana Gani ya'ya ne..
gashi nafara jin kamshin  cikin sananin farinciki yace  doctor doctor doctor Aisha ciki gareta tunda muka rabu ban sani ba.

   Dr sagir ya kalleshi da kyau yace friend waya gaya maka hakan?
yace dady bai je min daurin auren faiza ba.

  sai yaje min bikon Aisha ya tarar ashe tana dauke da cikina .
Gabadaya shima Dr sagir  hannuwansa ya jawo suka rungume juna suna murna.
Abdullah yace doctor kaima kana farinciki ko?
Dr sagir ya kasa magana sai dai yarinka girgiza masa kai .
sai da suka saki juna sannan Dr sagir ya sake miko hannu yace congrat...

Abdullah yace thank you doctor muje nayi sallar isha'i ka rakani gurinta yanzu zanje "bazan bari na kwana ban ganta ba
Dr sagir ya sake kallon.

  Sai Abdullah  ya idar da sallah ne Dr sagir  yace friend ka bari zuwa  gobe mana ,sai aje da manya Abdullah yace in mutu kennan.
Dr sagir yasa dariya yace baza ka mutu ba baban bby .
Abdullah ya mike ai maganar manya takare nima yanzu babba ne  tunda zan zama uba.

Suka yi dariya ,Abdullah na kokarin fitowa Dr sagir yace are you serious friend zuwa zakayi .
   ko ka manta sakin Aisha kayi  Abdullah ya dago da sauri ya kalleshi Dr sagir ya amsa masa da haka ne ,"sannan ya Kuma cewa tsawon watanni kun rabu ka barta da ciki baka nemeta ba sannan yanzu kaje mata karfe tara na dare  nasan abune mawuyaci ta kalleka.
idan da manya aciki sai a hadu a sulhunta.
a sake sabon aure jikin Abdullah ya danyi sanyi Dr sagir yace  wlh gara ka kwana yau kana addu'a Allah yasa ba tayi fushi da kai mai tsanani ba .
,kaga gobe sai ka lallaba kuje da dady ma zaifi.

Har Dr sagir ya bar shi zuciyarsa natayi masa wasi wasi 'sau Tari idan wani abu na farinciki zai same shi sai garin ya daure masa" daga baya ya tsinke masa da alkhari.
tsawon watanni  da yayi cikin ukubar rashinta har zuwa yau din .
daya zamanto  inda zaije ya huta ma ya rasa a karshe gashi ya juye masa alkhari "zai zama  uba nan da dan wani lokacin .
dan haka yasan koyaje da kyar in zai ji ko yaga wani abu na   bacin zuciya .
dan haka ya murza sitiyarin motar sa shi kadai dan salis yariga yatashi daga aiki.

Amman har yashiga lungun gidansu shi kadai a kafa "ya tuna da wani ido zai kalli mlm abu" sai yau yake zuwa garesu cak yaja ya tsaya ya kasa karasawa .
gara zuwa da dadinsa zai fi har ya juya yaji yakasa tafiya ,nan yasamu jikin bango ya rabe" yana hango kofar gidan .
yana tuna akwai kadararsa a ciki "yana nan tsaye har yayyenta guda biyu suka zo suka shige gidan .
sannan ya hakura ya tafi duk da bai ganta ba Amman  zuciyarsa ta masa dadi .
Yau ko ba komai zaiyi kwanan farinciki .
bayan yayi sallolin da ba zai iya   kayyadewa ba .

Karfe shida wayar dady ta sameshi  yana jiransa Abdullah yaisa cikin bedroom dinsa ya sameshi har zuwa lokacin yana kan  abun sallar sa .
,cikin farinciki kmr yadda yaga dady ya karasa ya gaisheshi "dady ya karasa jan carbi sannan ya amsa "ya nuna masa nan kusa dashi da hannushi.

Abdullah ya matso ya zauna inda ya nuna masa cikin fara'a dady yace Abdullah Amman kayiwa Allah godeya da zai azurtaka da zuria ko Abdullah ya girgiza kai yana murmushi shima dadin dariya yayi .
yace a to dan nima tun jiya nake godiya ga Allah zai kara mu zuria a cikin gidana .
Abdullah baice komai ba illa murmushi daya sake. dady ya numfasa yace abinda yasa na nemeka tun yanzu nasan zakayi mamaki akan wannan Batun kuma ne yuwa zakaji wani bakon abu.
wanda ba mamaki bazai maka dadi ba .
kada ka taba sanya damuwa ko shakku a game da abinda ke jikin yarinyar nan Aisha .
ni dai na amince tabbas cikin dake jikinta na cikin gidan ne.
tun rabuwarku akwai wanda nayi waya na dora akan lamarin, to har likitan  daya dubata na kwana uku da rabuwarku sai daya yayi min.
bayanin adadin kwanakin cikin dake tare daita a jiya.
dan haka komai maminka zata ce maka ka saurareta ne kawai ka amsa mata .
Amman kar ka bari maganar ta tayi tasiri agunka .
Abdullah ya daga kai dady yace Allah yayi muku albarka Amin Abdullah yakasa tashi daga gurin, dady ya fahimci yana son wani abu ne" yace uhm ina jinka da kyar Abdullah yace dady ita Aisha fa .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now