ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 66-67
Aunty Maryam da Dr sagir ne.
suka tsara duk yadda za'a yi tafiyar " musamman da kowa yaji inda dan'uwansa ke aiki akwai wanda yasani a gun .washegari da yamma sai da suka sake zuwa gidan Amman ko kadan bata bari Aisha tagane ba.
dan aunty Maryam ta kagu taga Aisha ta koma gidan Abdullah ko dan saboda wancan jarababben salim din yadda idan yata shi balbalinsa ya kone shi kadai .Da daddare tana dakin aunty kwance Aisha tana kan gado sun gama wasa da diyar aunty Maryam har tayi bacci a jikinta.
aunty tace ni ko Aisha ina ganin yanzu yadace ki fara zuwa awo asibiti tunda kinga watan cikinki yanzu yashiga wata na hudu kennan.
Aisha tayi shr bata ce komai ba.
Aunty tace Amman yadda kika gani fa.
wai saboda lafiyar abinda ke jikinki ne dan akwai magunguna na musamman da'ake son mai ciki ta dinga amfani dasu" domin ta haifi yaronka cikin koshin lafiya .
da yake cikin na ranta dan haka ta tsaya sosai tana saurara auntyn.
Amman in kin fi son sai kin kusan haihuwa ne shikenan aunty Maryam ta fada batare da ta takura mata ba .Aisha ta dan mike ta jingina da jikin gadon" ahankali tace ni aunty kawai sai a ganni na tafi wani asibiti kowa ya dinga" kallon ina da ciki.
aunty tasa dariya tace to ke meyasa kikayi abinda yasa kika samu cikin?
Aisha ta turo baki tana cewa haba aunty haba aunty da kanki .
Aunty Maryam ta sake fashewa dariya sai da tayi mai isarta sosai "sannan tace ai bangaren daza kije asibitin ko wacce ta kalleki itama abinda yakawota kennan .
Amman yanzu kina komawa ka'oje bbu wani zance zuwa asibiti akai akai.Aisha Tace ai can din ma akwai asibiti sai ba sai naje ba .
aunty Maryam tace ki ajeye komai kizo na kaiki asibiti malam ki kwantar da hankalinki bama asibitin mu ,zan kaiki ba nasan saboda Dr salim baki son zuwa .
wani zan kaiki duk da akwai wadan da nasani acan za'a yi miki komai ko ba nan.
Aisha ta girgiza kai alamun ta amince .
aunty tace to kishiriya gobe in Allah ya kaimu sai muje a yankar miki card daga nan zasu gaya miki randa zaki dawo ahankali tace shikenan.
aunty kuwa har godewa Allah tayi da taga ta fada tarkon farko .Tun shigarsu asibiti Aisha ta gane tabbas sun taba zuwa asibitin ita da sister dinta dubiya .
Wata nurse ce ta karbesu hannu bibbiyu da fara'ata sosai" inda ta dada birge Aisha taji dadi Sosai har cikin ranta kuma ta rike sunanta sister din kafin su baro asibitin.
komai akayi mata shi cikin sauki ba yadda ta zata ba .
A dan lokacin ma har taji tana sha'awar irin aikinta sister din.
Tama awo duk a lokaci sannan tace dole zata dawo jibi da akwai gwaje gwaje da za'a yi mata .To hakan kuwa komai akan idonsu Dr sagir da uban tafiya Abdullah ya faru .
ta gabansu "su aunty Maryam suka wuce "tun shigowarsu Abdullah ya kura mata idanunshi ta canza sosai ta kara kyau matuka fiye da lokacin da Suke tare.
ko Kuma a lokacin dan yana ganinta ne koda yaushe ne .
yanzu kuma ya dan jima bai ganta ba sanda suka zo daf da inda suke da sauri Abdullah ya juya bayan wani ginin.
ya dafe kirjinsa ya rufe idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin dokawa da sauri da sauri.
ita kanta Aishar data zo daidai gurin da Abdullah yake a boye sai da taji jikinta yayi alamun wani abu dan itama hakance takasance daita .
Amman bayanta kawai ta dan juya sannan sukayi gaba itada Aunty Maryam shi kuwa Dr sagir bayansa kawai ya juya musu .Ganin irin karbar da akayi musu yasa har suka baro gurin fuskarta a sake take Sosai .
Har aunty Maryam tarinka tsokanarta tace A'a kaga masu cikin fari ana murna dan ance zaki haifi da Kato .
Aisha tasa dariya tace kai aunty" har suka sake wuce wa su Abdullah na gun ya zubawa bayanta ido shigewar da tayi tana murmushi kawai Abdullah yaji gabadaya hankalinsa tashi .
garama yabita koma me zai faru gara ya faru wato ita rashinsa bai dameta ba ta sake abunta tana walwala har ya fito zai rufa musu baya da sauri Dr sagir ya fizgo hannushi yaja shi ciki sosai yace haba friend ka natsu mana.
zafa ka bata mana shiri idan ta ganka me yuwa baza kuma yarda ta dawo ba .
Abdullah ya tsaya kawai yana kallon Dr sagir hade da sakin naunauyen hadiyar zuciya sanda salis yakaraso da sauri ya tsaya yana duban Abdullah hade jin wani irin tausayinsa .

YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......