43

1.2K 60 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 53-54

Aunty Maryam ta dubeshi da kyau ta gano yadda ya nuna mata tsantsar wayo tun farko. taji haushin kanta na Subul da bakan datayi.

nan da nan ta sake bata fuska tace eh da gaske ne, Aisha sun rabu da mijinta "Amman doctor ina tabbatar maka bazaka taba samunta ba.
garama ma tun wuri kabawa zuciyarka hakuri ta  hakura da abinda baza taba samu ba .
tana shirin mikewa Dr salim ya dakatar daita murya a sanyaye  yace yi hakuri sister Maryam.
ni ban dauki abin da zafi haka  ba ,kmr yadda kika dauka .
nasan Aisha kanwarki ce Kuma abin ikon kice .
na gane koma ya akayi akwai wani abu da kike gudu .
shiyasa kika yi saurin fadar haka a kaina.
  Amman ki sani sister a yadda naje jina a yanzu dana rasa yarinyar nan na gwammace na  rasa wannan ya Nuna farar rigar aikin dake jikinsa .
     ya numfasa sannan yace dan nasan duk me mace irin wannan Kuma yayi gangancin  sakinta  komai daren dadewa zai waiwaye ta .

Auty ta kalleshi tace doctor duk kimarka da nake Gani  ba  zan hana  na  shaida maka cewa kana shirin sa kanka a uku  muddin bakayi gaggawa cire son Aisha aranka ba .
Mike  ko gezau baiyi ba sai ma murmushin  samun nasara dayayi .

Ahankali yace afuwa dai sister  Maryam ai ni nariga naga abinda yayi daidai da tsarin zuciyata dan karfin hali irin naki zaki tauyeni ina bazai yuwu ba wlh , a zafaffe tace to Allah yabada sa'a.
da karfin shi ya amsa mata da Ameen dan har da gaske kike .  ta wuce shi har gabanta na  dan faduwa uhm ba za'a  fara jin mutuwar sarki a bakinta .shima yajima zaune a wajen yana saka da warwara  hade jin haushin aunty Maryam .

Faiza tace dan Allah ni mama  ki kyaleni  na ci kaniyar wannan Yar iskar da bata gaji iskanci ba.
sai dai ta ara ta yafa.
kibarni  nacasata na gurje bakin rashin mutunci  shegiya Mar kirjin a gwagwa  itama Sami kokarin rama zagin take Amman faiza dam ke bakin ta murde .
        mama hafsa dake kokarin shiga tsakanin faiza da aminiyarta Sami.
Amman ina  faiza taki sakinta sai jibgar Sami take kmr Allah ya aikota da kyar da sidin goshi  mama hafsa tasamu ta rabu su .
Faiza ta bude baki zata lailayo wani a shar din mama ta  katseta  ke Ke ke tana nuna da dan  yatsa.
ya isa haka nace  sannan ta tura keyar Sami tana bata hakuri   tanuna faiza ke dai akwai Yar jarabar yarinya ana yaki kina ga kura  Tjeey din cin durin uwarki.
duk yawon danayi a kigajen bokaye da yan tsubu kenan zai tashi a banza.
ki wuce kebbi ga wanda ya fi Tjeey da komai ta koina can Amman kin tsaya kina asarar yawun bakin akan wannan mai sololon kan kmr na miciji.
Da wuya awa marakin lema .
faiza tace ai mama nasha gaya miki kece dai baki da fahinmta ina son  Abdullah kodan kyaunsa Kuma wlh dole ne na aure shi tako wani hali  na kanannade shi ta koina.
na dai tsaya ne naga ta karyar iskancin Sami wai daga naje mata sallama na tar daita da Tjeey.
dan na tsaya muna gaisawa dashi kawai tashiga bace bacen rai ni Kuma dana ga haka sai na dada shishige masa ni daman can yayi min. shima Kuma ya nuna yanayi dani shikenan take ta balain  shine yanzu tabiyoni  har gida dayake jakace .
ba dole nazage dantse na nuna mata karyar iskancin takeyi ba  .

Mama hafsa ta rike baki tana jujjuya  kai .
a ranta tace dole ma ayi tafiyar nan kebbi tare da ita  zai fi  ma'ana. Sannan cikin yin kasa da murya
tace nasan halinki da rawar jiki  sauran kije kina zubda aji agunsa  .

nasan  duk yadda wannan banzan yaron yake bai kama kafar masu wankin Abdullah ba balle matsayi .

dan haka kibarwa Sami shi suje can sukarata idan mulke shi zatayi da mai kullum wannan ba  ruwanki bane.
  ke dai ki duba cigaban ya zo miki .

yanzu kije ki hada inaki inaki anjima nan zamu tafi  har ni sai naga zaman naku ya daidaita sannan zan dawo.
dama naso  kifara yin  gaba ne.
saboda ni ma nan akwai abunda nasa ayi min saboda Abdullah din ya dinga rawar kafa akanki.
daya dinga yiwa waccen Yar matsiyatan masu tasan nono ,gara yadinga miki  .

Sai yanzu hankali faiza ya dawo kan maganar mama hafsa tace wlh kuwa mama .
Dan yana  daya daga cikin abinda nake tunani kennan akan auren Abdullah .
nifa    ko kallona yayi  nan duniya  ji yake kmr ya kashe ni.
Ko cikin farinciki   ko nishadi yake danazo gurin yanzu nan zaiyi kicin kicin yarinka cin magani .
mama hafsa tace kinga abinda yakama ki nutsu kiyi .
kisamu yadda zaki  kwatowa kanki martaba  a gunshi .
shine kika zauna kina fada da wannan cima kwance.
faiza ta kwashe da dariya tana Miko mama hannu wai sukashe .
Ai kuwa mama taba suka kashe suna tuntsira dariya .
Faiza tace  nida  nake da burin  indan na  aure shi  na samu na sake dashi sosai.
to yana haka yaya za'ayi abu abubuwa su kasance .

Mama hafsa Tace ina..
wane shi dan ubansa dan  baki san kullaliyar dana sake kullowa bane kai arziki ma idan  ba a gurinka yake ba aikin banza ne.
Ko kana sa wutsiyar ido ka hango shi a wani guri ya zame maka balain ka kasa tsugunne da duwawunka duba ki ganni  har Yar rama nayi saboda ganin auren  naku ya yuwu..

faiza ta katse mama da cewa  ni yanzu  nafi so ayi abinda Abdullah zai dinga lashe ni tamkar dawisu saboda so  shine kan gaba.
dan wannan jikin nasa  idan ya kasance yana  son mutun  nasan zai sakaka ka more kuruciyyarka  ka manta da kowa .
Mama ta zaro Idanu waje  ka manta kowa fa najikince har dani ciki  .
Faiza ta dan Susa  kai ganin  saba saiti .  wayancewa tayi  tace haba mama ai banda ai kece kan gaba in bake ai duniya zata min warbar kuno mama ta sauke ajiyar zuciya hade cewa abinda nake  so naki kennan.
to kinga dama yau za'a gama abinda nasa ayi to kinga ko zuwa da  yamma ne sai mutafi.
sai dai kuma idan duhu ne  yayi .
sai mu bari sai gobe idan Allah ya kai mu .
ai baza mu  tsaya kallon ruwa ba  yanzu masha Kaye a gurin kwado suka sake kashewa faiza har jijiga jiki take

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now