42

1.2K 63 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 51-52

Aunty Maryam na can bangaren aikinta ,inna ke sanarwa   zance ciki da abinda ya kawo ciwon  yayi tsanani , ta bar abunda take ta zubawa inna ido sosai , ahankali cikin mamaki tace innarmu cikin me Kuma har gabanta yana faduwa  .
Inna bata bi takan tambayar da Aisha  tayi mata ba tacigaba dayi mata bayanin  yadda ake samun lalura iri iri na laulayin idan macce ta samu  ciki ,
  tayi shr tana ji Amman ba abinda inna take fada take fahimta ba , tunanin ta yana can wani guri. tashiga uku Kar dai Abdullah ciki ya bankamata ,sannan ya sakota.
tasan inna bata fadar abinda bata da tabbacin a kansa  aunty ce tashigo tana surutai kai nima fa yau dole a daga min kafa nima mara lafiya ce dani .
Aisha ta kalli aunty Maryam ,inna tasan maganar zata mata dan Allah ta kwashe kwanuka ta fita wankewa har aunty ta zauna  Aisha nabinta da idanu ahankali murya adashe  tace aunty wai ciki dani ?   
Aunty ta kalli yadda tayi maganar tace au ke tun jiya baki sani ba.
cewa nake kinji ne shiya bangaya miki ba.
to ciki ne dake  bai kai wata daya ba .
nace ke Kuma irin naki laulayin kennan ciwon ciki da zazzabi ".
  Kwalla ta cika a idanunta kafin kace me sai hawaye shar ...shar... aunt tace to mayye  haka Kuma ke me son kananan  yara.
gashi Allah ya kawo miki shine zakiyi kuka  Aisha kuwa da zaune tamkar an dasata , bata sake cewa komai  sai  cigaba da kukanta take ita kadai tasan abinda ta tuna .
aunty ta matso kusa daita sosai tace A'a ai yanzu ba kuka zakiyi  ba  abinda ya faru yarigada ya faru,.
ta lafiyarki zakiyi da dan dake cikinki tunda ....Dr salim ne yashigo ya katse su ganin Aisha na kuka yasa ya ja ya tsaya yana kallonta can Kuma ya matso kusa da su yace yaya jikin ne ?
Aunty Maryam tayi dariya tana girgiza masa kai tace ko daya .
wai dan an gaya mata ciki ne daita ,shine take kukan dadi .
Dr salim ya kura mata Ido baya son har baya so  daukewa daga kanta ,dama takasance matarsa aka Kuma sanar masa tana dauke da cikinsa da bai san irin gatan da zai nuna mata.
   ba har sai shagwaba ta isheta," har sai da aunty takira shi sannan ya dauke idanunshi daga gareta".
da sauri ya kalli aunty yace ina tunanin irin su  abinda dariya ne dasu. haka nake da wata kanwa itama ko bacci zatayi yara suka hanata duk girmanta sai kiga hawaye.
aunty tasake kwashewa da dariya tace kusan duk jirgi daya ya kwasosu kmr wasu kawaye shima dariya yayi sannan yace excuse me sister inason na  dan ganki na mintina kadan "
aunty tace ba komai ta tashi tabishi sanda inna ta dawo itama.

Dr salim yace mijin Aisha ya jima da tafiya ne ko kuwa daman tafiye tafiye yake  aunty tace A'a ai... Daman ba tafiye tafiye yake ba ..sai Kuma tayi shr .

Dr salim ya dan nakalci wani abu ,.
yace sorry ina son nasani ne saboda irinsu da yanayin da take ciki yanzu tana bukatar kulawa ma'ana dole takasance tana da wani a kusa daita da zai dinga lura da ita sosai.
musamman ita da  cikin yazo mata  a haka.
duk lokacin dataji ciwon ciki tana iya shan duk wani abu datasan zataji ya daina.
ya numfasa sannan yace to idan kuwa mijinta yana kusa shi zamu bawa matakan da zata kiyaye da irin abin dazata dinga Sha.
har zuwa lokacin dazata daina jin ciwon cikin .
  Aunty Maryam tace ai da yake yanzu ma tana gida ne Amman  ko ni ko inna duk wanda ka yiwa bayani ma za'a san abinda za'a dinga yi .
dr salim ya furzar da iska hade kurawa aunty Maryam ido  dan ba abunda yaso ji ba kennan Kuma maganisa a kawai alamomin tambaya sosai  a tare da bayaninta ,Amman bai son ya fiyye shishigi da binkice akan komai.
yana son yabi komai  cikin tsari dan haka ya sake numfasawa yace shikenan .

Har byn kwana biyu  bata saki ranta ba kullum sai tayi kukanta .
Itama haka kawai tarasa dalili  yin kukanta .
mlm abu yashigo inna ke sanar dashi gabadaya yau taki ma cin komai.
tasa damuwa aranta shi kansa mlm abu lallabata yake  wannan lokacin.
ya dauko ledar yalon da yashigo  dashi ya wanke ya ajiye mata.
yace yaya zakiyi da kaddara Aisha duk yadda mutun yaso sai ki ga Allah ne kawai zai tsara masa yadda yaso.
inda mlm abu ya godewa Allah ma .
allah ya nufa  cikin ta hanyar  aure zaa  same shi .
gashi anyi auren ba a dade ba.
  Allah yakawo rabuwar an rabu da rabo atsakanin .
Ahankali ya furta ba komai haka Allah yaso .
yana jinjina kai .
Usman ne ya matso kusa da inna  ya zabga tagumi yana ji abinda mlm abu kecewa gabadaya tausayin yaruwarsa yake .
  gobe in Allah yakaimu sati guda kennan da sakin .
Amman har yanzu bbu wani bayani daga garesu abinda mlm abu yace kennan yana tsare inna da idanu.
  inna tace muma kada a nemesu in dai basu suka nema ba.
abar abun haka komai daren dadewa ai  shi cikin zai nemi ubanshi .

  Dr salim ya kalli aunty Maryam da suke zaune a wani ward su biyu yace abinda yasa na sameki anan sister domin na fayyace miki bala'in dana afka ,hakika Maryam kanwar nan taki nake maseefar so kai tsaye.
dan haka na kagu komai zai faru dani gara ma ya faru akan narasa  .
Aunty Maryam ta zazzaro ido "wa kennan kake nufi ?ya  gimtse fuska yace wace kike daita. aunty ta sake kallonsa sosai,  .
tace wai Aisha kake nufi ?yace yes ita fa sister bbu yadda zanyi shiyasa na sanar dake ki taimakmin dan Allah.
"aunty Maryam tashiga rudani da frigice dan haka ta soma girgiza kai tana  cewa doctor kasan abinda kake fada kuwa  . kai ya kada mata  ,. Amman ai
Nace maka Aisha matar aure ce .
gama ciki nan ya nuna maka hujja.
Dr salim ya dubeta dakyau yace sister Maryam tunda kanwarki ta Tako asibiti nan naganta nake addu'a r idan har ba alkharina bace Allah ya fidda min ita daga Raina .
Amman wlh kullum kmr ziga zuciyata ake akan soyayyarta . addu'ar dana dage dayi ne da Kuma hujjojin dana samu sune suka sa na tunkare ki kai tsaye da maganar .
Ban taba jin wani tashin hankalin daya sameni na farat daya ba kmr soyayyar yarinyar nan.
tunda na ganta na rikice narasa gane kaina.
kiyi hakuri sister Aisha tana gida a yanzu sun rabu da mijinta.
aunty taja numfashi tace kai ko wani me balain bincike ne ya gano maka haka .
Dr salim yace that's very good abinda nake son ji kennan .

aunty Maryam bata gane nufin shi ba sosai dan haka  ta sake  cewa  maganar gaskiya doctor a ina kaji wannan labarin?dan nasan maganar nan ko makota basu sani ba ..

Dr salim yayi dariyar murna sosai har cikin ransa yaji dadi tarkonsa yace sister kennan ni bbu wanda ya gaya min hasalima ban san wanda zan tambaya wanda yasan Aisha ba sai ke.
Nina na gano hakan da kaina .
aunty tayi sororo tana kallon doctor .
tace doctor bbu maganar wasa a nan fa .
Shima yadan nutsu yace da gaske nake sister ina son kanwarki.
Kuma aurenta zanyi.
ta sake zaro Ido waje ina wannan maganar ba mai yuwa bace .
A cikin lokacin daya ta canza fuska   tace doctor ba fa son irin wadannan magangunun an gaya maka Aisha tana da aurenta duk ma wanda yace maka bata da aure ya gaya maka gaibu .

Dr salim yace wallahi azim ke kika sanar dani yanzu .
sannan nasan zatona ya zamo gaskiya ..

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now