ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
Mmn sadeeq (hauwas)AISHA A BAGUDO
Page 38-39
Washegari karfe biyu suka sauka" ko cikakken minti talatin basu yi ba. Abdullah suka fita shi da salis " sai ita kadai a gidan an gyara koina tamkar suna gidan .
sai a ranar ta soma gane kan gidan nata.domin bata fahimci koina ba suka bar kasar. ta cika da dokin gobe iwar haka tana can gaban innarta" da usman dinta .
tasan bawanda yasan sun dawo dukiyar da ta samo na gwalagwalai da sutura acan dangin Abdullah ta raya a ranta duk yawanci inna zata bawa ta kwashe wadanda take sawa ta zubar ko ta bayar .
sai wanda zata kai wa diyar aunty Maryam sai ko sister dinta .
har karfe shadaya na daren ranar manager Abdullah yana can tare da dady suna tattaunawa game da tashin dady gobe ga wani miliyoyin kudi da ake zargin kunsan mutun shida dake company sun danne .
dan haka ne ma gobe kafin tafiyar dady Abdullah zai shiga meeting da manyan maaikatan.
wanda yake aiki dama wadanda zasu koma hutun next week yayinda sauran ma'aikata kuma sai zuwa jibi zasu yi meeting din .Hankalinsa ya rabu kashi biyu yasan Aisha tana can baza ta iya bacci ba sai ya dawo.
kusan awa takwas kennan bai ji dumin jikin matarsa ba.
dady ya dan lura da yanayin shi dan haka yace su rufe ragowar sai da safe .A gurguje Abdullah yashiga gidan ya sameta a takure kwance a falo duk a tsorace take .
bai tsaya wata wata ba ya dauke cak sai dire ta a koina ba sai tsakiyar bed dinsu ya kwantar daita tareda kai bakinsa cikin kunneta ya
Rada mata .. am so.. sorry dear na barki ke kadai .
ta turo masa baki alamun fushi ya matso sosai ya capko bakin sai daya tsotsa son ranshi danna ya rungumeta gabadaya numfasawa yayi sannan yace nadawo kebbi tarar da Aiki kaca kaca a cikinta. yanzu ma katsewa mukayi da har ina tunanin in sa a daukomin ke sai mu kwana a part dina.
dady ne yace in taho batayi magana ba ya dago fuskarta yace please... Kice min wani abu mana still tana jinsa yayi masa banza ya gane fushi tayi sosai dan haka ya zage wajen rarrasheta.
Ganin takin sakin fuskarta yasa yasoma tafiya tsusa abayanta tasoma mutsumutsun kwacewa cikin sanyi muryata tace ni kasaki yace ina yarinya ba wani sakin da zanyi.
cukulkuli yasoma mata cikin dariya dariya take turtujrwa har tasoma kyalkyala dariya iya karfinta .
yace oya kice kin huce sannan nabarki cikin matsanancin dariya tace na huce dan Allah kabar ni sanna ya barta ya jawota jikinshi ya rungume ahankali yayi kasa kasa da murya yakira sunanta Aisha.... bata iya dagowa ba saboda rungumar da Abdullah yayi mata tayi over sai dai ta narke masa yace me kika tanadar min kinsa ina matukar son kasancewa kuma ni maye ne akan kaunarki .
ahankali tace to ni ka sausauta min yace da me fa ,tayi shr yace talk to me now ya danyi murmushi dan fahimci abinda take nufi .
Ina cikin damuwa wlh jiya ban samu isheshen bacci ba .
gashi yau ma da kyar zanyi tunda sai na karasa aikin.
ana son shigar dashi kafin tafiyar dady .
Yayi kasa da hannushi yana taba cikinta kin ci abinci kuwa cike shagwaba tace naci sauran kai yace munci tare da dady duk su teema suna gaishe dake ta sake narke masa ajiki yadda take mutsu mutsu ajikinsa yarinka jin tamkar tana tsokonusa ne .tayi murmushin tace na godewa su teema
yace irin wannan shagwabar da wannan idanuwanaki .su kesake birkitamin brain fa su barinka jina a duniyar sama
please...Ina neman wata alfarma ta dan kalleshi hade da gyara kwanciyarta ajikinsa alamun tana jinsa yace kice kina sona koda kuwa sau daya zan ji dadi .. kuma bazan Raina ba .
Amman tayi shr buris dashi taki cewa koma. Ya sake cewa yace please now ... still taki magana da yake yasan halinta Yar ra,ayi ce haka yagaji ya hakaru ya watsar da zance . ahankali ta Mike zaune daga jikinsa saboda sakinta dayayi.
Tace muje kayi wanka yayi shr shima ya dauko system dinshi ya fara shigar da ragowar aikin
tace ni dazu dama gida ka kaini naga su inna.
shiru ba kowa sai ni kadai fa .
Amman gobe zaka barni naje ko ?
bai kalleta ba yacigaba da abinda yake .
yace ki bari na kammala da tafiyar dady sai na kai ki da kaina .
ta dan kalleshi tayi murmushin tace Amman kwana zanyi idan naje ko ?
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......