ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 83-84
Yadda mami ta lura da yanayin Aisha .
kawai tacewa Abdullah su kara kwana biyu idan ta kara warwarewa sa koma gidansu dan kmr kar maganar cikin ya bulo" sai tasoma laulayi gadan gadan .
dan haka part dinsa suka dawo duk yadda take jin jikinta ba kwari Amman Abdullah baya daga mata kafa .
duk nacin laulayin da manager Abdullah yasoma aikawa da sakwannisa" yake kama gabansa sai kura ta lafa yake dawowa .
a dan wannan zaman da suka yi ne "mami ta kara fahimtar halin Aisha da kyau .
ahankali taji kaunar yarinyar nashigarta kaunar Abdullah ita ta gogawa ya'yansa su affan .
to gashi itama tana neman ta jone dasu mami .
ahalin yanzu tana jin kunya hada idanu da innarsu Aisha kwarai da gaske har batasan yaya zatayi ta hada idanu da maimuna ba .
arziki daga Allah ne kuma arzikin haihuwa shine arziki gashi yarinyar tazo da arziki a jikinta.
dan ga wani ma tana tare dashi ya'yanta masu kyau da lafiya.
yarinyar har tana neman tafita da arzikin ya'ya mami take fada a ranta gashi ga dukkan alamun bata da wata fitina a tare daita ta lumshe idanunta tana yi musu addu'a a ranta .Ita kanta Aisha ta gane wannan cikin dan gatan mami ne.
dan tana ji dashi sosai .
a kanta sai a shirya abinci yafi kala bakwai a yinin rana guda sai wanda take so zata ci motsi kadan mami ta tambaye ta koda wani abu .
hakan kuwa yana yiwa Abdullah dadi Sosai har yasa ya dinga yi musu addu'a Allah yabasu mai sunan mami sai tayi ta masa dariya.
Aisha ta fara kullewa aranta macce zata haifa .Sai da teema ta gama service dinta sannan aka soma shirya shiryen bikinsu .
sun dace da juna matuka ita da Mansir dinta .
ga dukkan alamun kuma shima yana ji daita .Cikin ummu affan na da wata biyar .
aka sha bikin teema tun lokacin bikin teema ke rokon zata tafi dasu affan madina .
saboda shi kansa Mansir din ya amince dan farkon ganinsa daita tare su ya gansu ta rigada ta shaku da yaran .
mami ce tace ta taimaketa ta barmata yaran dan minal kadai ta rage itama wata rana dole ta tafi dakinta sai su Adnan din kawai.
dole ta hakura da hakan a can madina suka zauna inda iyayen mansir suke ,shi kuma yana koyarwa a university dake kasar .Aisha ta kalli inna tace innarmu dubi har sister ta gama karatunta Amman ni dadinsu affan nayi nayi yaki wai me zanyi da karatu?
a kalla dai inna mutun yasan matakin illiminsa Amman kememe yaki ko zance baya so yaji anyi .
ga maseefar kulle tsiya a gurin dadin affan. innarmu ni har rasa yadda zanyi dashi nake baya bari akai mu unguwa .
sai yace lallai sai dai shi da kansa .
To kuwa idan ina san zani wani guri to dole na fada tun kafin wata ya kama" idan Allah ya taimakeni idan ya kama kafin ya kai karshe in dai ina rokonsa zai kai ni. wai baya samun lokaci ne .Inna tayi murmushi sosai tace to menene ai haka shine miji?
Kuma haka wani namijin yake.
bayason yawan fita Amman idan kika yi hakuri sai kiga wata rana ya wuce karatu ma tunda baya so ki hakura .Tace ni inna fa ba wani guri da nake yawan zuwa Amman sai kiga da na masa zance fita zai bata rai .yace shi bayason yawo .
inna tace wasu mazan kuma kishi yake damunsu sai kiga daga haka ya zama kulle.
Aisha tayi shr ta tabbatar da akwai kishin ma dan hatta wayar hannu Abdullah yaki amincewa ta rike .
saboda azababben kishinsa usman yashigo ya zauna kusa daita yadda taga yayi shr yace menene ta kalleshi kawai tace bbu komai .To haihuwa tazo matav da wahala wannan karon saboda girman jinjirin Amman duk wahalar data sha .
bata kai tasu affan ba da kyar ta haihu da kanta a yadda ta kwalafa rai akan haihuwar mace har sanda suka je gurin teema a madina.
sai da ta siyo tsarabar kayan Yar bby mace.
to tana ganin namiji ne ta kudure a ranta zata roki Abdullah yasa mata sunan babanta .
sai gashi Abdullah yace tunda ba a samu mai sunan mami ba.
mami ta roki a saka mata sunan mahaifinta tayi shr batace masa komai ba.har sai daya manna mata kiss a lip's dinta sannan tace Allah ya raya taufik yayi murmushi dan yasan ba haka taso ba Amman ya zai yi umarnin mami ne .
.
Gabanin zata raka Abdullah interview England ne .
akasa ranar bikin sakina taso kwarai Abdullah ya barta a gida ayi bikin daita Amman yaki yace sai dai ta hakura su tafi tare .
Ganin har ranta ya baci ne yasa ya kara ninka mata abinda zata bawa sakina gudunmuwa akan yadda yabata da. dole ta hakura.
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......