ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 26
A hankali ya shiga dakin ya dan jima tsaye yana binta da kallo kmr wanda yarasa abinyi daga bisani ya tura wayarsa cikin aljihun wandonsa na baya "yasa hannu ya kamo nata ya dago ta kai tsaye gaban madubin dake manne cikin dakin ya kaita ,a tsorace take binsa wanda har mayafin dake lullube a kanta ya zame daga jikinta ya fadi kasa yasa hannunsa ya cire yayi cilli dashi gefe ya matso da ita gabansa cikin sanyi murya yace Aisha see ur face tsawon watanni biyu da kwanaki rabon da su ga juna" tun daren da zai tafi Denmark sai yau din da idanuwansa suka hadu ta cikin madubi "sunyi shiru suna kallon juna daga bisani ta janye idanunta ta sunkuyar da kanta "ya juyo da ita suna fuskantar juna ya rike duka kafadunta a hankali yake magana yace Aisha kuka kuka har yanzu dai please ...stop crying ya kamo hannuta cikin nasa yana murzawa daga can kasa yace haba Aisha ki tausayawa Abdullah yana cikin wani hali na barazana gaf yake da rasa numfashinsa ya maida hannushi ya dago habarta ya zuba mata narkakun idanunshi cikin nata suna fuskantar juna take
. idanuwansu suka sarke waje daya wasu abubuwa masu wuyar fassara ke fitowa daga idanunshi suna shiga nata " tayi saurin rufe idonta ahankali wayyo meyye wannan Kuma ? yayin da hawaye suka cigaba da biyo fuskarta. gabadaya jikinta ya dauki kirma lokacin daya wani tsoro yayi barazanar neman kai ta kasa '" tun kafin takai ga zubewa kasa ya taro abarsa ya manta da jikinsa "Abdullah ya sake zuba mata manya idanunsa dasuka gama rikicewa . akasan ransa ya iya furta rayuwa! rayuwa!! rayuwa!!! AISHA itace rayuwarsa Kuma Mafi soyuwa halitta acikin zuciyarsa" duk tsowan lokacin daya dauka batare da sanyata a idanunshi babu wani abu da yaragu game daita. sai ma kyaun data kara yi masa Sosai.. hancina yakai gefen wuyanta ya manna mata rikitattaccen kiss wanda wanda gabadaya ya susutawa Aisha tunani. tarinkajin tsigar jikinta natashi kadan kadan har suka Mike tsaye cak . , tana jin wani yanayi daban ajikinta ,wanda dabasan da zamansa ba, yahade jikinsu waje daya ya fara mata fushin bakinsa kamshin jikinta yana ta ratsa jikinsa yasa hannushi duka biyu yana share mata hawayen sannan ya janyo ta suka dawo kan gado ya zaunar daita yayinda shi ya zame ya dan tsgunno gabanta ya kai nasa hannayen akan nata dake zube kan cinyoyinta. ya kira sunanta ta dago ta kalli cikin idonsa ya runtse idonshi ,kallon da take masa yarinka rudashi daman can haka idanunta suke tsumashi duk lokacin da ta kalleshi ballanantana a yanzu da ya hadu da tsabar gajiya bacci ga kukan da tasha" tsigar jikinsa suka Mike yarinka jin wani sanyi nabin ajikinsa yayi saurin dauke idanunshi daga kanta "dan bai son hakan ya rude shi har ya rikita masa lisafin da zai manta da yanayin daya baro maminsa a dazu kafin su taho "ya jima bai ce komai ba ,sai da ya saisaita kansa sannan yasake kiran sunanta batare da ya kalleta ba yace Aisha ba kuka yakamata kiyi ba yanzu. duk kan wani abu daya faru ya wuce ina so dan Allah ki manta dashi a yanzu" gabanmu kawai zamu duba , abinda ya faru yarigada ya faru sai dai mu tsaya mu rungumi rayuwarmu ta gaba Allah ya nufemu da zama maaurata sai murike juna da amana. yana magana yana kara matse hannayenta cikin nasa nufi shi su rike hakan sosai ,ya koma ya zauna kusa da ita akan gado jikinsu manne da juna, yana son nuna mata yadda matsayin yake cikin zuciyarsa Amman bazai iyayin haka yanzu ba ,sake tuni maminsa dayayi ya aiyana aransa ko tasamu runtsawa " yasan daidai wannan lokacin indai bawani tashin hankali take ciki ba yakamata tayi bacci"ya runtse idonsa yana Jin yadda zuciyarsa ke dogawa dum...dum..kusan minti goma sannan ya bude su
ya kalli agogo dake daure da tsintsiyar hannunsa Shabiyu ke neman wucewa" yace Aisha mugabatar da nafila sai mu kwanta ko batayi musu tare suka Mike yayi gaba tabisa kamar yadda yaja hannuta zuwa toilet din dake manne da dakin ..Sun idar da sallar nafila yayi musu addu'oi sosai kmr yadda dady yace suyi ko kadan yaki yarda su sake hada Ido da ita 'dan kallonta nasake riketashi ya maida ita kan gado ya jawo hannuta ya sumbata yace Aisha zanje in kwanta kiyi baccinki anan "kar ki sake yin kuka idan kika sake zandawo mu kwana tare ..
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
عاطفيةzuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......