14

1.2K 62 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 14

Murya mama hafsa ce ta doki kunneta tana cewa A'a mu ba zama muka zoYi ba" mama hafsa tadan juya ta kalli sashin gidan duk ba kowa sai yaya umar dayashigo zai  dibi ruwa a botiki sannan ta juya takalli Inna tace ke kadai ce a gidan  kece  uwar yarinyar  kennan to ina uban nata yake ?  Gaban inna ya fadi ita bata fahimce ta ba sosai domin idanunta nakan dayar matar dake tsaye wacce tun shigowasu suke bin juna da kallon sani  "sai da tace iyayen Abdullah ne wanda kuke son manna masa yarku  ita kuwa mami karewa gidan kallo take tun daga sama har kasa tana girgiza kai tana gudun Kar ma wani abu yafado mata aka.
Mlm abu yana titi inda suke zama inna tasa yaya umar yaje ya kirawo sa suka taho atare ,tunshigowarsu shima da kalmomin mami yagane daga inda bakin suke da saurin jiki mlm  abu yakaraso Amman daga kallon da mami tai masa yasa jikinsa ya danyi sanyi ,zai Yi magana mama hafsa tace dakata malam ba maganar ka muka zo ji ba ,kasan ko daga ina muke ?
Mlm abu ya tsareta da Ido shima duk da tarin talaucinsa bai san wulakancin , tacigaba mu iyayen Abdullah ne wanda tsiya tasa kuka masa kiranye mlm abu yace tsaya kiyi  magana da kyau ki fuskanci abunda kike fada "mami ce tayi magana ba tsari ne yakawo mu ba Abdullah ya taka ya burma an kulle shi saboda haka nake son dan Allah abar mana dashi , ma'ana karaba banzar yarinyar ka da dana zan mallaka maka duk abunda kake so tun daga kan naira daya zuwa million goma nasan bakasan ni ko wacce ba Amman ita wannan tasanni ta nuna inna da yatsanta ,ke kuma kin xubamin idananu kmr zaki cinye ni ki masa bayanin ko Wace ce ok saboda   kinkasa shawo kan ishaq da asiri shine zaki bi takan " dana" to  wlh bazai yuwa ba ,mlm abu tsaye ke yana bin inna da wannan matar wato mahaifiyar Abdullah da kallon saboda maganganun ta suyi masa kama da mai  tabin hankali , mami tace ka tsare ni da Ido ka tambayi matarka zata maka bayanin koni wacce ,mama hafsa ta karba  idan karaba atsakaninsu yarka da Abdullah kaga kunyi hannu riga da talaucin kennan.

Yaya umar ya dago zai mayar mata mlm abu ya hanashi cikin matsanancin bacin rai yake dubanta shi kam ba girmansa bane ya tsaya yana sainsa da mata ,ya dubi mami tana da wani nasibi atare da ita tamkar yadda Abdullah din nata yake  uwa uba daraja da kimar da mijin nata  yake dashi wato mahaifin Abdullah ,taci albarkacin hakan da ya mayar mata da wacce tafi nata na zafi, yace  duk abunda aka fara shi cikin  arziki ya kamata a kareshi a hakan saboda haka za'a barmu ku danku , koma ince an bar muku , Amman ku bakuda abunda da zaku bamu wanda zai wadatamu da mutunci a idanunmu ,"mama hafsa tayi sauri ta cafe ai magana takare in dai kun rabar mana da Abdullah , Amman banda haka  uhmm taja numfashi , kuje kutako daidai ku mana ko wanda yadan gota ku Amman dan tsiya sai ku tabo kuloluwarku .
Anan inna zatayi magana mlm abu ya sake hanata mami tana kallonta tana girgiza kai ita duk yadda ta tsani abu sai taga bai kai iyanzu da take tsakar gidan ba, ta dubi zogale dake gaban inna ita dai wlh  sun gama da ita yanzu haka irin abinda suke bugawa Abdullah kennan a cikinsa ta fada a ranta ,.

Mlm abu ya numfasa yace ina fatan idan kun koma zaku sanar da kafar data zo neman diyata tazo ta karbi duk wani abu da aka kawo da sunan neman aure domin yanzu bama bukata .
Mami tace shiyasa nace idan kuna bukatar Kari kuzo zan kara muku duk wani abu da aka kawo muku na Abdullah ko ninkinsu ku tattara kurike abarmuku  Abdullah din kawai muke so ku rabu dashi. Mama hafsa tace kun samawa kanku lfy idan kuka rabu da Abdullah  haba to da angaya muku tsiya ko talauci hauka ne ,da zai sa duk ku rufe idanuwanku ku kasa duba abunda zai yuwu  kuyi ta hauka tamkar masu karfi .

Maganar tayi tsaye a ZUCIYAR  duk  wanda yake gurin hatta mami da suka zo tare tana ganin kamar maman na nema kauce hanya Amman da yake itama zuciya na zugata nan da nan Kuma abin ya mata dadi ,mlm abu yayi sai da ransa yana yimata kallon wanda ta fisu hauka da talauci ,Killa ita ce dukiyar ta ruda take neman haukacewa dan da ganinta ko kadan ba jinin arziki bace .

Inna kuwa bakin ciki ne kawai ya turnuketa har bata sanda take  zubda  hawaye ba ,gashi mlm abu ya hanata yin magana ,yaya umar dake tsaye shima ganin inna na hawaye kawai shima yasoma kuka  yanaji aransa da Ali ne  daya fi kowa zuciya haka tafaru a gabansa baba ya hanashi magana Killa da tuni zuciyarsa tayi bindiga .

Mami tace magana ta karshe kuma ina fatan zaku hanzarta aurar da diyarka ga gajeyaye irinku .
Mlm abu yace wannan abunda ya shafemu ne gargadi kuma ki koma kiyiwa danki ,domin duk randa ya kara tako harabar gidana hukumace zata raba mu dashi..

Mama hafsa tace idan har  ba tune abinda aka binne masa ba ai kuwa  dole zaku ganshi .ta dubi inna hade da mata kallon banza tace dan Allah akoma riga a tone sirkulle da akayiwa yaro ko yasamu ya huta ,a daina mana   haukan karya,sai da suka Yi rashin mutunci son ransu sannan   suka tattara suka bar gidan  .

Ko a mata ma haka mama hafsa tayi ta tsenewa Aisha da  danginta, ta juyo tadan  kalli  mami tace naji kmr kina wani zance ishaq da ita wacen banzar matar  manene a tsakaninsu" mami tayi shr tana kallon gefen titi  yayin da tashin hankalinta ka sake nun kuwa,tabbas tasan da dadyn Abdullah yasan inda yar'uwarsa take da tuni ya sauya mata rayuwa kuma tanaji ajikin baisan wacece yarinyar da Abdullah ke nema ba" Mama hafsa ta maimaita maganarta ta kai sau uku Amman shr takeji  akaro na hudu ne mami ta juyo ta zuba mata Ido tace kanwar dadynsu Abdullah ne uwa daya uba daya .....daga haka bata sake cewa komai ba  ta dauke kanta tamayar gefe ,banda gume bbu abunda ke fita daga jikin mama hafsa hankalinta har yafi na mami tashi surutai kawai take acikin ranta lallai zama bai ganta ba .

Washegari mama hafsa tabar kebbi bbu yadda mami batayi da ita ba akan ta zauna Amman taki ita kwata-kwata hankali har yanzu a tashe yake gara taje tayi da jikinta tunda tayi da baki dole mami ta hakura ta barta , Amman  tace cikin satin zata dawo .

Cikin yardar Allah jirginsu Abdullah ya sauka a Nigeria karfe shabiyun rana cike da kwarin gwiwa da farinciki Abdullah din yake ,tare dimbin nasarori daya samu fiyye da yadda dadynsa ya zata ,har byn karfe hudu suna tare da dady sai karfe biyar na yamma yashiga part din mami anan ma mami rikeshi tayi da girke girkenta tana tattalinsa har zuwa dare tafi kaunar yasamu natsuwa sosai  kafin tayi masa zance yarinyar dayake so ,tana kallonsa tare da yan'uwasa tana sake Jin kaunar dan nata fiyye da komai da ta mallaka kallon shi take tana tausaya masa "  teema tace bros what do you buy for me?
     Abdullah yayi murmushin  i will tell you letter bana son minal taji suka Yi dariya gabadayansu teema tace banda ni  kennan yace kowa da nasa ..mami ta zuba masa Ido har yanzu ZUCIYAR ta tana damuwa da inda yaje neman aure  Abdullah ya lura da yanayin kallon da mami ke Yi masa Amman bai kawo komai a ranta ba .

Sai byn sallar ishai yashiga part dinsa,ya furta sunanta  Aisha.....akasan ransa ita din  wani part ce na rayuwar sa  dan haka dukkan wani abu da yakeyi tunaninta yana makale dashi dan haka yanashiga part dinsa tasake zuwar masa daman sai dai in bai kadaita ba "har ya fito daga  wanka yanajinta sosai aranshi ,ya fito da system dinsa ya bude a tsakiyar gadonshi ya danno hotonta daya dauka da school uniform a jikinta  tana dariya ,ya kura mata idanunshi yana tuna murmushin da tamasa daren da zai tafi hatta dasashinta da wushiryarta sai da yagani ,kusan duk sanda ya rufe idanunshi sai yaga hakan yatafi da yanayin fatarta chocolate sosai colour dinta  tadace da ita, wanda bai sani ba kai tsaye zaikirata da farar fata ,yaja numfashi black American kennan ya fada a ransa jikinsa yabashi tayi masa addu'a r da tace zata masa a daren ranar da zai yi tafiya kuma yana da yakinin Allah ya amsa gashi yayi nasara fiyye da zatonsa dan idan aka cire mami da dady itace uku da zata masa addu'a ta sameshi. shi yasa yake son itama takasance wajen raba farinciki sa , Amman hakan bai samu ba saboda shi kansa bai samu kansa ba har dare.......

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now