ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 45 -46
"Oh,oh ni hafsa ,Allah baki ga Yar yarinyar da Abdullah ya aura ba duka bata fi rahma ba ,inji cewar mama hafsa faiza tace Allah mama .
Yo ina takai cikar rahma sai kayan nonuwa da shegen idanu suna narai narai sai kace wata macijiya .
Faiza tace wayasani ma ko macijiyar ce,
Tarikide ta manne masa kinsa fa suna yin haka .Mama hafsa Tace Ko daya, kinsa fa asalinsu fulanin dajin nan ne.
mama hafsa ta rage sautin muryata tace to komai fa ya gamu tun shekaranjiya yarinyar tana gidansu .
Faiza ta daka wani irin tsalle murna hade da rungume mama hafsa. Cikin rawar murya tace mama gaske kike ?
kina nufin Abdullah ya saki banzar yarinyar nan .
Zauna nan an gaya miki ni din ta wasa ce , ai tuni rauhanai sun gano sakin tun wajen duba gashi Kuma an yi shi,. Dan haka kishirya gobe gobe nan.
ki tafi dan nafison ayi abin da gaggawa tun kafin kinibabben wancan uban nasa ya dawo .Haka kawai muda shan wahala wasu da jin dadi ai wannan ma bazai taba yuwa ba .
ai tun da mami ta lasamun zuma a baki naji nakasa hakurin kirasa Abdullah .
gara komai zai faru ya faru wlh.
da dai kirashi dadi yasake kama faiza .
Faiza ta tashi bbu kunya ta dinga tikar rawa tana juyi a gaban mama hafsa.
tace jaira tunkuna dai kibari kishiga daular Abdullah sai ki cashe yadda ranki ke so .
faiza tace ai wlh kodan kyansa kadai zan'iya aure shi ,
gashi namijin duniya tana magana tana girgiza jiki .
Ke matsa can wawiya banza ana maganar masu nauyi kina magana wani kyau.
ai idan bbu kudi ai ko shi kansa kyan baya wani tasiri ,.
faiza tace ai wlh dan dare yayi ne da yanzu zan tafi tunda kince ( boka dan ina da Kare) yace wuyarta a raba su ,idan aka rabasu komai zai daidaita .Mama hafsa Tace haka yace Kuma bakisani ba har uwar ma a yadda ta nuna min sai yadda nace .
, dan haka banason abin yawuce wata daya ke Kuma kina shiga sai ki san yadda zaki mallaki dukiyar kinsa gidajen wannan ubanku nasa a market na siyar .
kinga sai amaida masa batare da ya ankare ba .sannan takara rage sauti sosai tace duk cikinku kece nake ganin zaki biyo ni, kinsa Allah banki ace wannan kanjamammen uban naku ya mutu ba nima in koma in aure uban Abdullah.
tunda an yarda da halacci haka ,faiza tace kai mama babanmu Kuma tace shifa.
to meyake tsinana muku ,shege mutun sai dan banzan son abin duniya tsiya.
mai kan goruba kawai faiza ta saki wata uwar dariya har da rike ciki ,.
mama hafsa tace ai wallahi bari kiga mugama da naki .
ko yaya naga waje fadawa zanyi mutaru ayi ta damawa damu.faiza sake kecewa da wata dariyar tace kinga munkasa mun tsare kennan mun hana gaba mun hana baya komai yadawo hannunmu tabawa uwar hannu duka tafa .. .
Mama hafsa Tace uhmmmm ana magana ma shiyasa nake sonki dan nasan duk abinda na tsara bakya kii..
sai dai kinsan Allah ina tsoron alhj ishaq har cikin Raina.
faiza tace dady ko tace shifa ,kina ganin ko irin dan wasan nan na dagin mata bai so.
bayan gaisawa ba yarda wani abu ya gilma. Amman nasan ta yadda zanyi ai duk wani taurinkai akwai maganinsa .Faiza ta Mike tace bari kiga mama naje nasoma shirina tun yanzu kinsa da zazafi ake buga karfe .
mama hafsa tayi murmushi tabi diyartata da kallo tana rayawa a ranta ai ba zaki sha dadin ke kadai ba.
har dani za'a.
yadda nayi sintiri a gidajen bokaye da makabartu ne zan zauna sai kin mikomin ahankali ta Mike itama .Duniya gabadaya ta cukede ta tsayawa Abdullah waje daya ,.
yarasa wacce irin rayuwa mahaifinsa take son yayi byn taraba shi da tsanyin idanunshi .
Tun yana kuka da idonshi har yadawo yin kukan zuci ..Gabadaya wayoyinsa ma a kulle suke komai ya tsaya cak rabonsa da zuwa office tun ranar da dady yabar kasar.
ya gwammaci yacigaba da zama a mataccensa har ran da za'a kaishi kabari da dai ya fida
koina ,kwanansa uku duk wata al'ada ta rayuwarsa ya barta inka dauke sallah . Ko magana bayason yi idan mami ta turo yazo haka zai zauna a gabanta bai fahimtar komai, ko fada take har tagama bai jin abinda tace ,.
shi a lokacin ko mami yankashi zatayi bazai damu ba .
Dr sagir ne yake buga kofar part din Abdullah da karfi gaske,
yana kiran sunanshi Abdullah Abdullah jin muryarce yasa Abdullah ya zubawa kofar ido yana jin Yadda kirjin ke radadi da ciwo mara misaltuwa.
jin an cigaba da bugun kofar ne yasa ya Mike da kyar ya bude yana budewa yayo gaba abinsa.
Dr sagir yashigo yana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun..ganin yanayin abokin nasa .. friend meyye haka kana da lfy kuwa five days kana cikin daki a kulle.
ko ma'aikatanka , ka hana su , shigowa su gyara maka guri,
Abdullah dubi yadda kadawo ya zauna agabansa yana nuna shi da yatsa .
salis ma yace ko shi kaki yarda ka Gani why..Abdullah yayi kwanciyarsa akan kujera bai ce komai ba domin zuciyarsa ke wani dokawa yasa hannunsa duka ya dafe kirjinsa dashi .
cikin mamaki Dr sagir yake kara kallon koina sannan yace ina matar gidan take.
ina Aisha nace, sunanta dayaji ne yasa ya dan ya kalleshi ,Dr sagir ya sake maimaitawa Abdullah tambayar , Abdullah ya dubishi yace na saketa da sauri Dr sagir yace what .
Abdullah ya amsa da kansa alamun haka ne.
why ar you talking rubbish Dr sagir ya fada a fusace ,.
Abdullah ya dan yi murmushin takaici ya sake kollonshi , Dr sagir ya sake dafashi cikin sanyi murya yace my friend meyake damunka ne na nemi wayar ka bansamu ba ,na dauka ko baka kasar ne jiya naje office ance baka zuwa, .
anjima zan wuce sokoto shine nabiyo nayi checking din ka .
ance baka ganin kowa salis nasamu sannan nashigo friend meyasa Meka haka kasan abunda kafada min kuwa.
Abdullah ya dan Mike zaune ya kalleshi ido jajur murya a raunane yace Dr sagir lafiya ta kalau .
da gaske na rubu da mamata, mami ce ta zabi haka ,dan haka na saketa.
Dr tunda na auri Aisha duk abinda zai sani farinciki shi take min to yanzu bata nan mun rabu me zai sani farinciki kuma ? kawai ya koma ya kwanta yana sakin numfashi sama sama tamkar mai cutar asma.
ya rufe idanunshi gam yana tuno Aisharsa bai sake yin magana ba sai wasu zafafan hawaye dake gefen idanunshi can kuma jikinsa ya dauki kirma ya kamo lip's dinshi gabadaya ya tura abaki ya datse da hakoranshi wannan lokacin yazo masa da abubuwa munana masu wuyar mantawa ko awani hali Aisharsa take ..a kasan rashi yace killama tana can cikin jin dadinta tunda daman ba sonshi take ba shi kadai yake shan wahala akanta mamina maye yasa ...meyasa kikawa Abdullanki haka baki san bazan iya rayuwa ba muddin kika rabani da ruhina ,.
Aisha zuciyata ita bugun zuciyata sosai jikinsa ke rawa yayinda idanunshi ke runtse ahankali fizgo numfashi yana sake dafe zuciyar.....MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......