57

1.8K 74 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO

  Wow  masoyan arziki , yan biyu masu  tsananin shiga rai ,hakika  kun shiga Ran bagudo   ba karya .kuna ina 🗣🗣🗣🗣🗣  blessing twince ,hasana danlarabawa & huseena danlarabawa ku matso kusa wannan shafin naku ne ku kadai, kuyi duk yadda kuke so dashi,  ina matukar  sonku har cikin nan ❤ , ina kyawun yi daku irin sosai din nan, ana kyawun tare 🤝🤝🤝🤝nima ina addu'a r Allah yabani  blessing twince guda bibbiyu sau goma... 😃😃😃

Page 77-78


Aisha dake labe a bayan Abdullah itama ta dan matso  jiki a sanyaye tana gaishe ta...
  mami ta amsa tana kallonsu a bazatan da suka yi mata  ,da turanci Abdullah yake gayawa su affan su gaishe da mami Amma kememe  suka ki  matsa daga jikin Abdullah"ko  jikinsa basu bari ba suka sake mannewa babansu .

mami ta zubawa sarautar Allah ido ga Abdullah lokacin yana yaro har guda biyu a gabanta  abin ma tsoro yashiga bata .
Abdullah ya fahimci yanayin da maminsa  tashiga dan haka  ya sunkuyar da kansa kasa yayinda yaran suka sake  mannewa jikinsa.
tsawon lokacin mami tana zaune takasa magana ,ahankali murya cike santsar ladabi da biyayya  Abdullah ya dago yace kiyi hakuri mami ' jiya dare yayi  bamu  ba Muzo dasu ba yau kuma tun safe ake shirinsu ".
Mami ta girgiza kai kawai tayi shr "Abdullah yashiga waige waige yace su teema sunje school ne" aHankali mami ta amsa" ya dube su affan cikin harshen turanci yace kuje gurin mami kusha tea " Amman kememe suka ki sakinta sai da kyar yasamu ya bambaresu ya fita ai kuwa suna ganin haka suka koma byn mamansu  .

Aisha kuwa ko motse bata iyayi sosai ,saboda barinta da Abdullah  yayi da mami .
shima kuma tun fitarsa yake tunanin yanayin dazata shiga, Amman ba yadda zaiyi gara komai yazo karshe  .

Mami takasa dauke idanunta akan yaran ,ta kasa magana wani abun kunya duk goce gocen cikin Aisha da take.
sai gashi ta haifo irin abinda ta haifa sak ita har guda biyu ma" data tashi haifar nata , gashi su kansu yaran basu santa ba, gudunta ma suke, taji bazata iya zaman falon ba ga Aisha a gurin" ta Mike cikin sanyi ta shige ciki ,tamkar ta zubda hawaye take ji,.
Aisha na nan   takure a zaune "gashi su affan sunki yarda da kowa" ita a zatonta ko mami wani fushin tayi , shine duk  ta kara tsorata ,tana nan zaune su minal suka shigo da ihu suka karaso kanta itama sai a lokacin dan  taji dadi "da wayo da calculate suka samu suka dauki yaran , dukkansu kamar su cinye yaran  suke ji . Aisha ta kallesu byn sun hau da ita samansu "Tace teema kunbar mami ita kadai teema Tace ina jin bacci take yi" Amman bari na koma na Gani "ta dauki Adnan da karfin tsiya suka sauka .

To yinin ranar  mami tasa aka canza abinci ,saboda su ,da kyar yaran suka yarda suka zauna kusa daita sai da aka baza kayan wasa da calculate iri iri a gabanta "sannan suka zauna ta zuba musu ido tana kallonsu  hannuta   ta daura saman kan su  affan tana shafawa tana dauke numfashi,  wani abu daya kara girgizata yadda  taga kmr pampers din jikinsu ,ce ta damesu tasa teema ta cirewa adnan anan bathroom din mami " ta ajiyeshi ta tafi ta gyara affan.
mami ta lura da dan tabon dake cinyar Adnan dan duhu gurin yayi kadan wanda hausawanmu suke cewa rowa to yadda yake a jikin yaron haka yake ajikinta "shima a bangaren dama kmr nata.
wannan tashin hankali har ina ga Aya ta koina tana zuwa mata" har kara dubawa take .anan aka sake shirya su da abincinsu" duk akawa mami kaca kaca da daki" sannan teema ta hau sama kai affan dan yana son mamansa.
Byn fitarta  mami ta kamo adnan ta dinga kallonsa tana hawaye taci kukanta sosai ita kadai ba wanda yasani  .
  tunani kawai take   mama hafsa ta kusan kasheta a da , take fada a ranta.
ita batama san kowaye daga cikin  yaran ba a gabanta tunda yaran duk kamaninsu ta baci  ta jawo shi jikinta sosai ta rungume ganin datayi yana gyangyadi saboda a can Ma affan din bacci  ya fara .

Dady kuwa dayaga yaran rudewa yayi ,yana dariya ya cewa Abdullah kada fa dawowarsu nan canjin abinci ,yasa sukiyin kiba da girma" irin haka. Abdullah kuwa dariya yayi yana sunkuyar da kai kasa dady sai sake jinjinawa yake "yana Allah kennan me yin yadda ya so" to yanzu wanene babban acikin su ?
Abdullah ya kallesu ya kirawo sunan affan dan  sun rigada sun san sunansu .
dan haka shi din ne yayi saurin waigowa "sannan ya nuna wa dady shi' dan shima da haka yake  ganesu "musamman mami ta canza musu ma'aikata raliyya  kadai ta amincewa ta dinga kula da yaran .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now