ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 12
Yana matukar tsoron mami yadda ta nuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna kin mutun a fili bbu wanda ya isa yasata dole ,ya kalleta idanunshi suka Yi ja yace Aisha idan aka ce za'a daura mana auren cikin satin nan zaki amince ? A frigice take kallonsa tana girgiza kai gabadaya tagama rikecewa tace nidai kayi hakuri ba dai yanzu ba ,ta zuba masa idanunta shima ita yake kallo yace yes na matsu A ce kinzama matata " tace nidai kayi hakuri idan Kuma ka damu sai yanzu to kana iya samun wata ni sai zuwa wani lokacin "yaji haushi maganarta Amman yadda tayi maganar yagane yarinyarta ta a fili ya zabga mata harara yana mai jan tsaki yace ai ba sai kin gayamin ni kadai nike haukana akanki ba nasan bakya sona , takalleshi kamar zatayi kuka kayi hakuri dan Allah ba haka nike nufi ba" bai sake ce mata komai ba ya juya ya barta anan . Sai taji ba dadi aranta daman Kuma ta lura tun zuwansa ta fuskanci kmr yana tare da damuwa .
To har zuwa kwana biyu da maganar su da mami bata sake tada zance ba a iya nasa tunanin ko mami ta hakura ne" wani satin mami take sa ran tafiyar ta zuwa Egypt dubo mahaifinta dake kwance ba lafiya shine dalilin dayasa ta ajiye komai tabari sai ta dawo Amman a wayewar garin jumma'a labarin rasuwarsa ta same su dan haka cikin rashin shiri tayi tafiyar ita da su teema yayin da dady da Abdullah sai rana Saturday suka bi jirgin yamma suka isa, washegari uku dady yadawo Abdullah kuwa kwanansa goma suka juyo tare da su teema da minal saboda makaranta mami ta zauna saboda tafiyar bata kusa bace dole ta zauna har ayi arbain .
Ko sanda ya dawo da washegari sai da yaje yaga Aisha ya rinka nuna mata yadda yayi missing dinta na kwana biyu da bai banga ta ba Aisha taringa kallonsa yanabata mamaki ko kadan baya da riko iya tunanin ta fushi da yayi ranar da yayi zuwan sa na karshe shi ya hanashi dawowa ,sai da yasanar mata da rasuwar da akayi musu. Tayi masa gaisuwa yace idan mami tadawo zaizo ya dauketa ya kaita tayi mata gaisuwa ta amsa da to "Amman ita kam sai ta tsinci kanta tana mai tsoron shiga cikin family dinsu,
Sun sake zama na musamman da dady akan maganar sa da Aisha ya shidawa dady ya sanar da iyayenta cikin satin nan zaizo bai dai samu mlm abu a gida ba Amman yagaya mata ta sanar da inna, ko gwaggo Laure da tazo haka tasa Aisha gaba da zance Abdullah shiyasa har daren ranar da dady zaizo din da Abdullah yazo sai da yasake tuna mata akan tasanar saboda yasan halin kayansa, sai a wayewar garin ranar lahadi mlm abu yafito zai fita suna sallama da gwaggo laure domin itama a ranar zata wuce sannan tashiga rumfar inna da Kyar take gaya mata inna ta hau salati ta fito tana sanar da mlm abu yakira Aisha yana Kuma tambayarta ta amsa da yau da yamma karfe hudu .
Gwaggo laure tace ma'aiki anmabi Muhammad ke yanzu dan iskanci gidan sirikan naki zasu zo shine kika kiyin magana ?
Inna zata kuma yin magana usman dakatar da inna yace ai mun godewa Allah ma da aka samu Allah ya matsi bakinta ta fada ,ai da sai dai anjima kawai Kuga baki, inna tace zata aika ai wannan yarinyar bansa halinwa ta dauko ba gwaggo laure ta rike baki tace miskili kafi mahaukaci ban haushi yarinyar kin zama sai kace harsashi acikin gida Aisha ta hade rai hade shigewa daki mlm abu yace aiko bai ga tafi ba nan da nan akashiga gyara gida ,dakinsu yaya yusif dake soro aka bude aka gyara da yake daya kofar ta fita waje gwaggo laure ma fasa tafiyar tayi yayin da inna tabawa usman kudin machine yaje yagayowa aunty Maryam ,tayi musu dan abun da zata tare su dashi mlm abu da kansa yabar komai ya tafi yagayawa alhj aminu domin a ranar zai Yi tafiya to haka nan alhj aminu yaji maganar daga sama dole dashi za'a karbi baki to shima din sai barin tafiyar yayi yana jinjina al'amarin Allah yadda ya kwallafa ransa akan yahada jininsa da yarinyar Allah bai nufa ba har sapani sukai ta samu da maidakinsa .Karfe uku aunty Maryam ta iso da kulolin snacks iri iri da juice dakinsu yaya yusif yasha gyara aka shimfida katuwar dadduma Aisha kuwa barin gidan ma tayi gabadaya .
Dady yacika alkawari ya dangana ga iyayen Aisha anyi barkwanci musamman ga alhj aminu to duk yadda dady yayi tunaninsu sai yatarar basu kai haka ba ,sai dai karfin hali da rufin asirin ubangiji Amman ta ko ina bbu, sai dai yaji dadin ganin mahaifin Aisha dagani zai Yi datako shidai mlm abu zaune yake yana bin alhaji ishaq da kallo tsabar kamamani dayake hangowa a fuskarsa tayi masa kama da wata fuskar a haka akayi abunda za'a Yi dady ya tambayar ma dansa kuma Mafi soyuwa acikin yayansa auren Aisha alhj
Aminu ne yaba da Aishar ga Abdullah cikin murna da farin ciki suka rabu .Bayan dady yadawo Abdullah zaune agaban mahaifinsa yayi shiru yana jiran daga dadynsa yaji mai zaice dangane da zuwansa dan gabadaya baya cikin natsuwarsa burinsa Bai wuce yaji mai dady zai ce ba .
Dady ya yadan Nisa sannan yadago Ido yana kallon Abdullah sosai yaron nasa ke bashi tausayi ganin yadda soyayya tamai dashi cikin kankanin lokacin, wajen yadauki shiru zuwa na wani lokaci sannan dady ya iya Kiran sunanshi Abdullah ya dago yana duban dady ,dady yace Abdullah Aisha dai tayi Maka ko ? ya sunkuyar da kansa kasa yanajin yadda gumi ke bin jikinsa dady yasake numfasawa ya girgiza kai yace shikenan yanzu a yadda nike ganin a aika musu da dukiyar aure da duk wani abinda ya kamata Amman abari sai zuwa hutun karshen shekara sai ayi bikin ta yadda zaka samu hutun ka gabadaya .
Abdullah yajin jina kai dady yacigaba sannan yace akwai bukatar a sai musu gida babba mai wadatar guri musamman saboda taron daurin auri sai mota Hawa ina ganin biyu ko uku zata musu sai maaikatan da zasu taimaka musu da gyara koina ,Abdullah ya dago idanunshi yana wa dady kallon murna yana sakewa dady godiya. dady ya girgiza kai yana lumshe idanunshi shi awajen sa Abdullah ya cancanci fiyye da komai agunsa domin Samar masa farinciki.Tun safiyar ranar litinin dady yasamu sakon da yake Jira daga South Korea suna neman su domin yin interview anan reshen su dake Denmark dan haka dady yasa hannu akan Abdullah ne zaiyi tafiyar wayewar garin talata kennan zai bi jirgin Lagos domin ta Lagos zai zasu tashi , yakasance Abdullah cikin uzuri yake har gurin magriba da Kyar ya samu bayan sallar ishai ya tafi gurin Aisha shi da salis yaya yusif ne ya fito yake masa baya ai tana can gidan aunty Maryam Abdullah ya duba agogon sa yana da sauran lokacin ,yayi sallama da Yaya yusif suka wuce.
Tun yamma taje gidan aunty Maryam ita kuma tarike ta sai ta kwana dan haka sallar ishai kadai tayi ta nade a gado har ta fara bacci Aunty Maryam ta taba ta taje inji Abdullah ta Mike tana kallon aunty Maryam sannan ta dubi agogo tara saura kwata sannan ta Mike a hankali ta canza kayan jikinta .
Da sallama tashiga falon bakin yana tsaye daidai kofar da zata sadashi da ita hannayensa rungume a kirjinsa ya langwabar da kai a jikin bango ,bata ji amsawar tasa ba Amman ta lura da yanayin kallon da yake binta dashi ta dauke idanunta dan tarigada tasaba da wannan mayataccen kallon nasa a hankali yazo daf da ita ya zauna suka hada Ido ya gane har tafara bacci ,ya lumshe idanunshi yana mai tabbatar wa kansa muddin yasameta zai ji dadin rayuwa da ita ya fada a kasan ransa komai nata bata cika daukarsa me wuya ba , hasalima ita ba komai yada meta ba,duka Bai fi rabin awa da mintina da idar da sallar ishai ba Amman har tayi bacci takan sauka kawa rayuwar ta akan abubuwa da dama ,hakan yasa take sake shiga ransa Sosai da sosai , yanayin kallon yake mata yasa kirjinta yarinka bugawa , Abdullah yakira sunanta yace Aisha I love you ,I really love you please tell me do you love me? ........
MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......