7

1.4K 85 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 7

A rude take kallon babanta idanunta cike da kwalla , shikenan Abdullah zai sa babanta ya tsine mata ta fada a ranta ,baban yace kinji dai abunda na gaya miki, sai dai idan bai dawo ba shikenan ,ni tashi ki bani guri cikin tashin hankali tamike a rikice tabar dakin baban.

Innarsu kuwa tana can kaoje gaban kawunta  Malam tahiru  hakan lamarin Aisha yasoma damunta tarasa wacce irin ZUCIYA ce da ita kamar inna zata zubda hawaye ,malam dahiru yace a kul kika zubda mata da hawaye zaki ja mata masifa a rayuwa, inna ta numfasa sannan tace ni ina tunanin ma ko dai tana da makarai ne don da anan ne da yanzu tayi haihuwa biyu Amman ace har yanzu yarinya ta tsani ayi mata zance namiji .malam dahiru yace dole kibar tafiyar ki zuwa jibi domin har istahara zanyi yau inshallahu , gobe Kuma akwai magungunan  da zan hada mata kitafi mata dashi .da yammar washegari ne malam dahiru yasake Kiran inna  yace shi kam iya bincikensa bbu abunda dake damun Aisha illa miskilanci shine kawai yake damunta"yace daman Kuma kusan  duk yawanci masu  irin wannan hali ,zaki samu suna  bawa Maza tsoro da frigitasu,yace Amman ga magungunanan kitafi mata dasu a sata ta shanye "byn sati biyu ki turomin ita akwai taimakon daza'amata na tsawon kwana uku,inna tayi godiya tace ni daman nagane miskilanci ne ,dan wata rana idan ya motsa daki take shigewa ta rufe koina tayi kwanciyar ta ,irin haka idan tabani haushi sai in hanata abinci sai danuwanta usman yasani a gaba da magiya in bata wani lokacin har da kukansa Kuma duk wannan abun idan bata gadama ba  kona bata sai tace ta koshi . malam dahiru yayi dariya wlh shine kawai Allah yashirya mana.inna tace Ameen.

washegari tabaro kaoje ita da umar  .
A dawowar da inna tayi ne ta riski Aisha cikin damuwa bata kawo komai ba illa miskilanci tane ko Kuma bata ji  dadi bane byn tafiyar ta,dan haka ta dinga rarrashin ta har ta samu ta Sha magungunana da inna tazo dasu.

washegari sai gashi inna tacanza mata tasan tabbas taji abunda ya faru bayan bata nan ,ita kam tashiga uku ina zata ga Abdullah ta roke shi ya yafe mata ko tasamu sauki gurin iyayenta , byn sunanshi bbu abunda zatakarar game dashi ,sai dai ko "dan" kamaninsa.

Kwance take a dakinta duk abun duniya ya dameta ga usman ma bayanan kusan duk wani aiki datakeyi sai taga Inna  tayi sauri tayi abunta ,shiru tayi tana tunanin koda yammar nan daga gidan su sakina take domin itama fushi take Yi da ita tun kwana biyu kafin rabuwarsu da Abdullah tazo duk dai akan maganar Abdullah dine yataso  ,dan Abdullah yaje  har gidansu sakina da matsalar Aisha ,ya rasa yadda zai bulo mata ta fahimce sa  Aisha tayi murmushi tace lallai ashe babbar magana ce takawo ki dan yadda naga kin hade fuskar nan taki idan banyi da gaske ba lallasani zakiyi .sakina ta sake bata rai  be serious sister Abdullah fa ba irin mutane da za'a dauki maganar su  joking bane , Abdullah yakai wani yanayi da yaka mata kibashi hadin kai na tabbatar Abdullah da gaske sonki yake so Kuma na gaskiya "
Aisha tasake yin murmushin tace ke har kin gano son gaskiya yake min kennan ,to mai zai hana ki bashi asiya ko ummu tunda ke nasan karatu zakiyi .

Sakina ta sake mata kallon bacin rai wanda ita kanta Aisha ta gane ranta ya baci ,tayi murmushi tace ai Abdullah basu ya gani yace yana  so ba ni din ma badani yadace ba dake yafi dacewa shiya kikaga an Dame ki Amman zan rabu dake shima in Allah yaso Allah zai cire masa son naki ,Kuma ina tabbatar miki baza ki taba gane gatan da ubangiji yayi miki ba sai kin rasa  Abdullah ,inna kawai tayiwa sallama ta fice .

Aisha tadawo daga tunanin da ta Lula ita kam kowa haushinta yake ji yanzu gabadaya jikinta yayi mugun sanyi,.

Shigowar su saifu ne ya katse ta suka shigo da gudunsu har alamen yana faduwa aunty Maryam dake bayan su tace ai ga irinta nan ance kutafi ahankali kunki Aisha ta fito da saurinta tana dariya ta taro su anan tsakar gida ta shimfida musu tabarma  , Aunty ta zauna da ciki a gaba Aisha ta gaishe ta tace aunty har yau kinki kiranmu Aunty Maryam tace kedai bari nima cikin duk ya ishe ni ina zaune agida nace kai gara in taho nan ko na dan ji dadi ,sai naga kmr kin rame ko ba Kya jin dadi ne .
Aisha tayi murmushi karfin hali ta sunkuyar da kai , Inna ta fito daga bandaki suna gaisawa Aisha taja hannu alamin tace zo muje in baka chocolate suka shige dakinta tana jiyo aunty na tambayar inna wai ko Aisha bata jin dadi ne naga kmr ta rame daga dakin ta jiyo Inna tana gaya mata abunda ya faru ,tana Yi tana aiki ta , aunty tayi salati tace zance usman dai ya tabbata  ke inna wlh irin Aisha fa  inbasu bi ahankali ba Maza ke asirce su suga karya wulakancin , Allah ya kiyaye.

    Inna tace A to  gatanan dai sai ki gaya mata ko taji , yayyafin daaka fara Yi ne ya tashi aunty daga tsakar gida ta shigo dakin Aisha yayin da inna tacigaba da aikin abinci dare , adaki aunty kece mata ke Aisha yanzu saboda Allah haka zakiyi taki rayuwar da wulakanta Maza kina ganin kin kyauta kennan ? Aisha tayi raurau da idanu kmr zata Yi kuka tace wallahi Aunty ni ba wulakantashi nayi ba .  To me kika Yi masa inji aunty mutun yatako yazo har inda kike Kiki fita ki watsa masa abunda yakawo miki Amman kice ba wulakantashi kikayi ba   ,me ya miki ?aunty ta zuba mata idanu tana sauraranta hawaye suka zubo mata tasa bayan hannuta ta goge kawai sai ta tsinci kanta da kasa sanarwa  aunty  har cikin gida Abdullah yashigo mata da yanayin shigarta  da ke jikinta  dan haka kawai ta bar laifin a kanta tace aunty wallahi ba da gaske yake so na ba,.
Saboda me kika ce haka ?aunty baki ga Abdullah bane fa ta yaya ma  zai soni ?ni wacce da zai so ni me nake dashi da zai so ni me muka ajiye ,kawai sai sa kuka  mai ratsa ZUCIYAR mai sauroro tana kukan tace wallahi akwai abunda ya kawoshi ,ko nataba masa laifi ne ban sani ba shi ne yazo ya rama . aunty tayi murmushi takaici iya naki tunanin kennan kina ganin baki da abunda namiji zai so a wajen ki, to bari kiji ingaya miki baki ajiye komai ba Amman kina tattare da abinda duk namijin duniya mai ji da kanshi zai soki "ke da  kanki  kinsa kin da kina da kanwa  mace zata so ace ke din ya'yarta ce ,in kuma yaya  mace itama zata so ace ke kanwa ce gareta" idan yarinya ce zata so tayi alfahari ina ma ke kika haife ta" aunty ta dan numfasa sannan tace to a mu mata kenan nike tabbatar miki da wannan in Kuma bangaren maza ne kinga shi  namiji zai so ya mallake ki,tabbas baki San kanki bane shi yasa kike tsammanin bada gaske Abdullah yake ba ,.
   Abdullah cikakken haif cast ne ko gurin uwa ko uba tun randa ya fara zuwa gurin baban saifu yayi masa kwatance nan ya yaba da hankali sa . Aisha ta dago kai tana duban aunty sai yau ta gano ta tsanin da Abdullah yabi yazo inda take ta runtse idanunta tana mai zubda hawaye dana sani gashi batasan inda zata ga Abdullah ........

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now