29

1.9K 87 1
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO

Page 29


Da sauri Abdullah ya dago idanunshi yana kallon mami ,ta daga masa kai alamun haka take nufi "tuni hawaye ya fara zubo masa a karo na biyun daya zubo masa a jin abinda ya danganci farincikinsa" na game da auren sa da Aisha ahankali yace thank you mami thank you mamina  ..... tacigaba da murmushi ,su  teema ma gabadaya suka hau murna ita kanta mami taso su bar tafiyar sai zuwa  gobe domin su dan kara sakewa, minal tace bros idan kuntafi Kuma sai yaushe zaka dawo mana da aunty mu. yace ba dadewa zamuyi ba zamu dawo, mami ta karfa Allah ya dawo da ku lafiya ya tsareku...

Teema ta zagayo daga bayan mami  tana dariya tace Ameen maminmu..
Mun gode ,Nan Abdullah ya kwanta a gabanta ji yake tamkar ya dauko Aisha itama ta zauna a cikinsu ,anan yayi sallar la'asar har kusan biyar suna tare" duk da rabin zuciyarsa na gurin Aisha bai san a halin da take ciki ba itama, sai da dady ya yo masa waya sannan ya fito ya iske dady a bakin get ya shiga part dinsa agurguuje sannan ya fito ya samu dady tare da direver da zai kai su airport har bakin get su minal suka biyoshi yayin da mami ke makale can jikin Window dakin ta tana hangensa ..

Sai karfe shida suka bar kebbi shi da Aisha da RK .

Kwanan su biyu a tsohon gidan su, na Abuja inda anan ne taga ainihin hotunansu na family shi. dady da mami sai kannensa tun ma yana teenage  dinsa kafin Tafiyarsa oxford anan taga inda Abdullah ya samo kyau har gidan wani friend dinsa ya nema suka je wanda sukayi secondary school tare alokaci suna matasa shima ya dade da yin aure har da ya'yansa biyu .
Ranar laraba  suka bar Abuja da  daddare suka isa Germany karfe shadaya agogon can gabadaya su a gajiye suke duk da sun dan sami bacci ,a abuja har kusan shabiyu basu yi bacci ba har Abdullah ya fito daga wanka da rigar wanka ajikinsa tana zaune har yanzu a gefen gado "ya dubeta yayi murmushi ya dauki  fam dinsa yace idan kinshirya  ina falo   kisame ni sannan ya fita ya barta .

Ta dan jima zaune tana karewa yanayin dakin kallo daga can Kuma ta tashi ta bude toilet din dataga ya fito ta shiga ta danno key data Gani ajikin kofar "ta tsaya tsai tana kallon tsaruwar bathroom din tamkar acikin wani dakin ta dinga kallon kanta a madubi sannan ahankali ta soma fidda kayan jikinta,hankali kwance  ta sake tayi wanka sosai, ta nade jikinta da irin rigar dataga Abdullah ya saka ta fito sai kuma tayi sororo bata san wani kaya zata saba ,haka suka zo daga ita sai kayan jikinta" Abdullah yasa tabar yan wanda ta debo daga gida  a Abuja. ta jima nan a zaune daga baya tayi tunanin kawai ta mayar da kayanta. Kuma har zuwa lokacin basake jin motsen Abdullah ba, kicicikin sanya kayan take sai gashi ya shigo tana ganinsa ta matse jikinta waje daya makale dakayan  ita bata sa  kayan ba sannan Kuma bata cire ba "sai idanu da ta zuba masa Alamun tsoro , yadda yaga  tayi  shi yanemi sa shi dariya ,yayi murmushi yace am sorry sannan ya juya bayansa yace akwai kayan da zakisa  a cikin wardrobe ,sannan ya fita .
Ta tashi ta bude da kyar ta sami daguwar riga ta saka dan ma dai ba zata iya kwana da nata bane. sannan ta bishi falo  a hanya sukai suka ci karo yayi saurin jawota jikinsa ya hade jikinta da bango yace gaskiya ni bazan yarda arinka barina ni kadai ba, ana ta gyaran jiki ni anshareni .
  Zatayi magana ya hade bakinsu waje daya  wanda yake yawan mafarkin faruwar haka yasoma tsotsa bakinta har sai da yaji ta saki kara sannan yadan sausauta rikonta hannushi rike da kafadarta ya zubawa fuskarta Idanunshi  tsorace take kallonsa shima ita yake kallo ahankali ya hura mata iska ,tayi saurin lumshe idanunta yana  murmushin ya kamo hannuta suka dawo falo tanason yin mishi kuka suka zube a gaban kayan ciye ciye duk da  tana jin yunwa Amman kasa cin wani abun kirki tayi sosai. Saboda irin kallon da Abdullah ke binta dashi ya kamo hannuta cikin nasa  yana mammatsawa ahankali  yace Aisha baki ci komai ba fa ,yasa  dayan hannun nasa yana shafo cikinta yace yanzu kinkoshi kennan yadda yake mata wasa da cikinta zuwa mararta har yasa ta buge masa hannun, ta fara mishi kuka ya jawota jikinsa sosai yasoma rarrashinta. yana dariya mikewa yayi ya ciccibota  ya shige da ita dakinsu ya kwantar daita tsakiyar gado   shima ya kwanta abayanta ya gyara masu rufa yace muyi bacci gobe ina da ganin doctor .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now