38

1.4K 59 0
                                    

[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 41-42

Jikinasa yaji   a lokacin ya daina rawa sai babban dan yatsan kafarsa kadai ke motse .
ya dubi takardar gabansa  ya dinga kallonta tamkar ma ba takarda ba.
yana jin hayaniyya akansa Amman baya gane abinda ake fada ba.
ya dauki Biro ya daura akan pepper sai ya tsaya  shi kwata kwata bai san yadda ake rubuta saki ba .
Mama hafsa da ta fahimci haka tace sawa zakayi kai Abdullah ka saki matarka Aisha saki uku shikenan.
  ka huta da jaraba .

Minal ce ta fado falon ta tana kallon inda yake zaune kmr gunki.
Byn tagama jin duk abinda su mami ke cewa.
ta tuna da maganar malamin dayake zuwa yana koyar dasu har gida a fannin addini yabata yi musu bayani game da babin aure da saki .
yace Allah da kansa ya halicci saki Amman baya sonsa mafi kysunsa    ne ayi  saki daya .
dan haka ranta dake   mugun bace " ta isa gurinsa tace yaya ance ba kyau a saki macce saki uku .
saki daya ma yaisa dan haka ka rubuta   saki daya .

Mami ta daka mata wata irin tsawa da frigita  gabadayansu, dole ta bar falon .
da yake itace magana ta karshe da minal tai masa dan haka ya rubuta saki daya ya turawa mami takardar  kusa da kafarta.
ya dafe goshinsa da kirjinsa lokacin daya ya fita haiyacinsa  wani juwa yaki kansa nayi Amman yana nan a gurin bashi da niyar barin gurin .

Mami ta dauki pepper ta duba ta Gani tace ko rabin saki kamata nagode balle odindin daya.
Tace  kana iya fita .
ta Mike tsaye itama mama hafsa ta karba ta Gani tace an dai rubuta sakin .
yanzu nan za'a kai mata mami tace yanzu kuwa tun dare bai mata ba aje akwana cikin duhu a gidan gyatumi  tace eh .

Aisha na   nan kwance yadda Abdullah yabarta Amman kmr anyi mata duka haka tarinka ji ajikinta da zuciyarta tamkar yadda ta ji a dazu.
  ahankali taji karar mota bbu wanda ta bawa ranta sai Abdullanta ne .
ta danyi murmushin ta sake kudindinewa.
wai idan yashigo ya dauka tayi bacci ,.
Amman a yadda ta jiyo ana bude kofar cikin gidan ana shigowa da hargowa tasan bashi bane.
tayi sauri tashi ta zira rigar baccinta yayinda  tarinka jiyo maganganu a falo ana hade kiran  sunanta.
Yasa ta juya tana  duduba gefe da gefenta ta wawuri wani zani da tayi wanka dashi dazu ta daura ta sanyo hijabin sallah ta fito .
Karo na farko kennan da mami ta taba ganinta .
a lokacin mami kmr ma  ba a cikin haiyacinta take ba.
saboda tana son taga wacce mayyar yarinya ce ta kama mata ZUCIYAR Abdullah.
kawai taga fitowar  AISHA.
ba haka taso ta ganita ba.
Yar yarinya Yar cikinta sai da suka kalli juna ita da mama hafsa .
akwai wani sirri dake jikin suruka da uwar miji wanda  dukkansu sai da suka ji shi ajikinsu saboda shi dama namiji adan aka  halicce shi daga jikin mahaifiyarsa byn wani lokacin   sai ya koma  jikin matarsa ..
to wannan sinadarin ma  yayi matukar tasiri azuciyar kowanne su dan daga mami har Aishar  haka sukaji .

Mama hafsa ma kanta saida ta Raina yarinyar tace ,"ho ni hafsa yanzu Abdullah kan wannan abar  yake wani hauka da tashin kai .
ko me zai ci ajikin wannan "oho".

Mama hafsa Tace kinga ungo wannan kinji.
mijinki ne ya sake ki.
   AISHA ta tsaya tana kallonta tana son manna mata hauka ta gane matar tun farko zuwan  da suka yi gidansu.
mama hafsa tace karba  ki duba mana kin tsaya kina bina da idannu .
idan kinga zaki iya tafiya yanzu to ga hanya nan a bude take  idan kuma sai gobe ne ma duk daya.
Dan za'a kulle musu gida mami dake zaune kasa magana tayi.
AISHA tasa hannu ta karba takardar  jikinta na rawa.
bata bude ba kmr yadda matar ta umarceta  dan tasan haka din ne .
tunda ga mahaifiyar mijinta nan zaune  .
Tana tsaye ta rasa abin yi ta sake ce mata ciki zaki shiga ki dauki abinda zaki dauka .
dan nasan kina fita zaki samu bus din zata kai ki wannan banzan lungun naku .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now