ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 71-72
Watannisu biyu kennan a Denmark har a lokacin Abdullah yana cikin tsantsar farinciki dan kullum sunayi waya dady kuma yana nuna masa mami tana samun sauki sosai akan da .
To har kusan awa daya suna maganar ta a halin yanzu mami ba sallah ba har azumi tana yi koda yaushe.
dady yace Abdullah ka kara addu'a komai yazo karshe inshallahu koma ya Kare za'ace .. .
Abdullah dake kwance kasa kan kafet inda Aisha ke zaune turus da ciki tana tacin soyayyiyar plantain.
yayi murmushi a filli ya kalleta yace Aisha shi fa dady duk ya damu da zance haihuwar nan cewa yayi shi dabadan zan jima anan ba da can zan baroki .Aisha kuwa murmushi tayi dan duk abinda zai sako dady ko mami ciki sai dai tayi murmushi ta sunkuyar da kanta .
hakan yasa itama ta tuna da innarta .
Lokacin da sukaje musu sallama haka tace Abdullah ya kallonta kunyar dadinsa take ji sai da ya kalli cikin gabanta sannan ya ahankali ya mike zaune yace kai madam ina ga lallai idan baki haifa min Yar bby mai kiba ba to zaki haifa min super man a gidan nan .
ta kalli plate din tayi dariya tasan abinda ta cinye yakewa shima ya dinga yi mata dariya saboda ta birgeshi.
yana matukar son ya dinga ganin dariyarta domin wushiryarta da dasashinta mai duhu suna karamata kyau .
suna dariya yace dakata naji motsen bby na "ya dan yaye rigar jikinta ya kara kunnenshi a jikin cikinta ya dan yi Jim .. sannan ya dago yana kallonta "yace ke
Aisha cikin ma ya kara girma tayi murmushi tana Ture hannushi ta rufe cikinta cikin yana shan budewa" a gurinsa yace da gaske fa ' yayi girma kuma nan gaba sauran kusan wata biyu ki haihu" ko daman haka cikin yake .
Batace komai ba ya dan hade fuska yace dole ne fa muje asibiti gobe ko zuwa Monday har scanning za'a yi miki.
Aisha kin ki zuwa asibiti tunda muka zo rabonki da asibiti tun na Dr sagir yana kallonta itama shi take kallo can ya tuna da abinda ta taba ce masa yasa dariya sosai .
yace koda yake kince baki kara zuwa asibiti kada a kara miki wani rufa ido "itama dariya ta dinga tana harararsa ya dinga dariya shima daya tuna yadda sukayi mata wayo" yace wlh shiyasa nake son Dr sagir yana matukar kaunanata sosai .
ya sake daga rigarta ya sumbaci cikin sannan ya mike bari nayi wanka Amman inshallahu gobe muna asibiti dan naga wannan cikin yanzu in ki ka zauna sai a kirga dari kafin ki Mike tsaye.
yacigaba dayi mata dariya har ya bar wajen tana kallon inda ya bari tace Allah yasa ta haifi Yar bby da zata yo dimple din Abdullah yana kara masa kyau sosai idan yana dariya.Bai fi minti biyar da shiga wanka ba tana nan zaune inda ya barta cikin wayoyinsa dake zube kan kujera daya ta hau kida a hankali ta shafa saman kan kujera ta dauko me yin karar.
takara a kunne tace hello daga dayan bangaren mami tace hello wacce ?
jin murya mami yasa gabanta yayi wani irin mugun faduwa.
kwata kwata bata san ita bace da bata daga wayar ba.
Aisha tayi shr mami tace maman Abdullah ke magana wacce ke ina Abdullah din?
idan har ta kashe wayar zai zama kmr tayi raini wayo ne ga mahaifiyar Abdullah "a ganinta .
dan haka ta dage iya karfinta tace ni.....ni..ce. .tace kece wa inji mami ?
numfashi Aisha kmr zai dauke har wani sama sama numfashinta yake saboda tsabar tsoro da take ji a yadda taji tana tambayar ta tace ai...sha...
daga can bangaren mami ta maimaita sunan tace daman dake ya tafi . abinda Aisha taji alokacin hatta abinda ke cikinta sai da ya motsa dif taji an kashe wayar hade jan tsaki mai tsawo.
taji jikinta ya dau zafi da maganar karshe da mami tayi "ahankali ta ajiye wayar har yanzu kirjinta yana bugawa da sauri "cikinta na juyi tamkar ana yamutsa bbyn ciki.
Ahankali ta mike da kyar ta shiga dayan dakin dake nan falo ta kwanta tana jan numfashi sama sama abinka game tsohon ciki .
koda Abdullah ya fito wanka yana goge kansa da karamin towel bai ganta ba ahankali ya tsaya yana kalle kalle daga can ya kwala mata kira ya nufi inda ya jiyo ta dan amsa masa da kyar.
yana tura kofar ya ganta kwance tayi lamo akan gado .
ya sauke numfashi ya karasa ya zauna kusa daita sannan ya lalubo tafin hannuta yace ya kika zo nan kika kwanta da kyar tace nan yafi min kusa.
kuma bacci nake ji ya kwaikayi yadda tayi magana yana shafota.
ta rufe idanunta batace komai ba yace ko nazo muyi baccin tare.
ta girgiza kai so nake na dan huta yayi murmushi yace ba kya son nazo na dameki na gane ai ya sake yin murmushi ya mike idan kin tashi ina falo ya sumbaci lip's dinta yayi waje .Fitarsa tayi tamkar wacce aka kara mata wani abu akan yadda take ji' har kusan awa guda tana nan kwance ciwo take ji a kasan mararta sosai kmr zata mutu "can ta mike da sauri ta shige toilet din dake manne a cikin "dakin tana shiga ta duba ba sai taga jini ke biyo kafarta ba.
gabanta ya sake wani irin faduwa akan na da yaushe rabon da taga hakan tun suna American sau biyu Abdullah yana shigowa tana ban daki data ji ciwon ya fara damunta kawai sai tasa kuka" tana nan ciki bathroom taki fitowa har Abdullah ya hau buga kofar da karfi sannan ta rarrafa ta bude yana ganinta haka ya shiga tambayar ta a rikice ta nuna masa kafarta ya kalla ganin jini da yayi ya kara tayar masa da hankali .
a gigice ya kamota yana kara dubawa yace kinga ni ko Aisha kinga ni ko shiyasa nace muje asibiti duk yabi ya agigice gashi nan kina shirin jamin asara saboda bakya sona Amman ba komai " da sauri ya gyara mata jiki shima jikinsa na rawa ya sa kaya ya fita daita .Allah sarki ciwo kmr jira yake akai inda magani yake "cikin lokacin kadan Aisha ta fara fita haiyacinta..
gashi babban abinda ya hana ma a rufu sosai akanta "saboda basu da kati ma kwata kwata wanda ta taba zuwa ma a Nigeria duk har shi ya hadawa dady da takardun .
cikin ikon Allah har wayewar garin asuba Aisha bbu wani sauki sai na ubangiji .
Allah ya taimaka saboda matsayin aikin daya kawo Abdullah din aka basu card din ganin likita Aisha na kwance da kyar take magana Abdullah dake kusa daita hannushi makale da nata ya sake matsowa daf daita "ahankali take sake magana "da kyar ya gane abinda take fada' Amman yaki kulata.
Dan tun safiyar ranar ta dame shi da maganar ita dai a maidaita gida taga iyayenta" kada ta mutu ko Kuma ya kawo mata su ta gansu" kar ta tafi bata gansu ba" maganar tana neman takarasa kasheshi .
dan sau biyu da suka yi waya da dady yagaya masa halin da ake ciki da abinda take cewa sai gashi dady ya sake bugowa .
yace gara yasa akawo mata iyayenta dan idan bata gansu ba wani abu ya faru daita daga baya sai yaji ba dadi .
To har dare lahadi magana ma sai ta gagari Aisha" sai idanuwa datake wulwullawa.
Abdullah ma ya kasa tsaye ya kasa zaune ballanantana magana .
sai dai kallon kallo ciwon a duka jikinsu su biyu yake "abinda doctor ya gaya masa da suka isa office cewar Aisha ta Sami wata razana ce ko wani abin tsoro da ya frigitata.
ko ta dauki wani abu mai nauyi wanda hakan yasa shi kansa abinda ke cikin ya juye zaune..
shi ke tokare mata numfashi Amman suna kokarin ganin ya koma yadda yake .
Da yammacin ranar abun ya bawa Abdullah tsoro sosai jikinsa ya dinga rawa ganin Aisha numfashi ma sai da aka sa mata oxygen saboda kan yaron ya sake yowa saman kirjinta" yana yiwa dady waya Amman shima kirjinsa ya rike gam.
dole ya amince dady ya sakowa Aisha iyayenta a jirgi ta gansu "yayi addu'a har bai san irin wacce yake kamawa ba Allah shi ya bashi Aisha kuma yana tare dashi .
idan ya dauketa ba yadda zaiyi wanda a lokacin ko shi kansa Aisha bata ganewa .
doctor yace dole a cire abinda ke cikin tunda ta riga ta galabaita.
ko "dan " ya koma yadda yake ma bazata iya haihuwa da kanta ba .
Tunda Abdullah yaji iya nan bai kuma gane abinda doctor yake cewa ba, ya dai zubawa bakinsa ido yaga yana ta motsi har sanda yata bashi yace be a patient .. please.
Abdullah ya dan girgiza masa kai sannan da kyar yace to doctor ai cikin bai isa haihuwa ba.
doctor yace eh dama koda ya rayu sai dai yazo a bakwaini da kyar dasa bakin babban ogansu Abdullah sannan yasa hannu akan za'a yi aikin.
dan gabadaya yagama fita haiyacinsa sai zare idanu yake Amman bakinsa bai bar ambaton sunan Allah ba .
Yana kallo aka shiga daita dakin yin operation ko a samu ko a rasa .
One hour batayi ba aka fitar mata da identical twince din ta masu matukar kama da juna .
komai nasu iri daya hatta mahaifa guda daya ce shiyasa ba fahimci biyu ne a cikin ba .
Sun sha wahala kmr mamansu dan daya ya zaune kan daya sai a sannan Abdullah ya dan samu kwarin jiki yana tambayar uwar dan shi ta matarsa yake yasan ko ya rasa bby "muddin suna tare zata sake haifo masa wasu.
idan kuma ya rasata wa zai kama.
doctor yace ana sa ran farfadowarta itama ..
dan har lokacin batasan inda rayuwarta take ba ..MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......