ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Wow tawan nagode kwarai da yadda kike matukar son novel din nan ,ina kike my khadeey pinky🗣🗣🗣 this page belongs to you Only ,kiyi duk yadda kike so dashi kina Raina yaruwa love you so much dear muna mugun tare 🤝🤝🤝🤝💗💗💗
Page 36-37
Washegari sai karfe biyar na yamma agogon Nigeria a sannan suka sauka a Abuja wanda tun karfe uku direban da zai kai su kebbi .
yake zaune zaman jiransu saboda rashin isowarsu da wuri daga can mami ta roki dady da yace su bari sai da safe su taho saboda tafiyar dare ga hazo anayi a ranar .Shima dady yaga dacewar haka .
dan haka tafiya zuwa kebbi dole ta tashi sai washegari Amman dady yace su taho da wuri saboda shima jibi zai tashi sai da suka gama naganarsu dashi sukai sallama Abdullah ya'ajiye waya.
A tsohon gidan su na Abuja byn Abdullah ya fito wanka duk sanyi da ake tsulawa basasa Abdullah sanya kaya ajikinsa ba .
daga shi sai short niker zuwa cinya kana kallon Yadda gashin jikinsa ke kwance ya dauko system ya daura kan table yana karkadewa ya zube sannan ya kunna yashiga neman sakonni da dady ke son ya tura England .Har Aisha zata shiga wanka itama ta dubi agogo karfe takwas dan haka tafasa ta koma kicin ta hado masa fresh miki a cup ta nufe falo inda yake .
ya dukufa a internet jikinta nannade da towel iya cinyarta ta karoso .
ta ajiye masa a gefe ta kalleshi daga shi sai gajeren wando ta danyi murmushin shi dai ta nakalci weather sanyi na birgeshi ko ya shawa cikinsa ko Kuma yajishi ajikinsa ya dan jiyo ya kalleta yace me kike yiwa dariya ? Yasake bata dariya tace bakomai har ta juya yace dawo ki dauki abinki haka nan kizo ki ajiye wa mutum abu kiyi gaba .
ta tsaya tana kallonsa tace to kuma me zanyi yanzu "ya dauki cup din fresh milk ya ajiye gefe. ya daura yatsansa kan lip's dinshi sannan ta gane abinda yake nufi in ba haka ba in bar miki abinki .
ahankali take tafiyar nan nata da tasan yana madaukar hankali Abdullah takaraso tana sakar masa murmushi ta daidaici daidai dimple dinsa ta sumbace shi a gurin .
sannan ta juya da sauri yayi murmushin yasan abinda take maitar so kennan a fuskarsa shiyasa takiyi masa a bakin da ya nuna mata ya kai cup bakinsa ya shanye yana murmushi .Sai da tashirya jikinta cikin short trouser dark black da riga pinky colour tawa jikinta wanka ruwan da turaren invitation sannan ta dawo inda yake ta iske shi yana waya bata san ko dawa suke waya ba cikin harshen nasara yake ta magana.
ta zauna kan kujera ahankali take kallonsa Abdullah ya iya turanci sosai tamkar wanda aka sarrafushi daga bakinsa. take fada aranta kyakkyawa ne nashiga kowace duniya sannan kuma fist class ne ,ita sai a yau ta taba karemasa kallo duk jikinsa lungu da sako gashi ne kwance luf luf bbu wani Alamun daya taba kwarzane shi. ta Lumshe tsumammu idanunta tana jin wani irin sauyi na daban ajikinta "Abdullah daya Kare waya .
ya zuba mata mayun idanunshi sai dai bai ce mata komai ba.
hannushi yasa ya janyo wata takarda da yayi printing a gurin ya dunkuleta ya jeho mata ta zabura tana ware ido alamun tsoro yace uhm ..haka ake kallon miji idan wani abu ne ya birgeki ajikin mijinki ba sai kizo gareshi ba.
inyaso azarce da komai ya dage mata girasa daya hade da kashe mata Ido.
Aisha tasake kallonsa tana jin wani irin sanyi aranta ahankali zuciyarta ke beating ...yace yes ba sai ki zo abaki kome kike da bukata ba Amman yarinya kin tsaya kina wani tunani .
taji kunyarsa sosai dan ita batasan yagane tana kallonsa ba.
kawai sai ta rufe fuskarta da tafin hannuta.
yace idan baza ki zo ba ni zan zo da kaina da sauri ta Mike ta shige ciki ta barshi yana mata dariya.
ya jima yana kallon inda tashiga ahankali yace Aisha kennan komai nata mai kyau ne,Kuma kowani irin shiga tayi saiya mata kyau shigar tayi ta birgeshi matuka. ta kayan tsanyi "duk da shi bai cika sasu ba Amman da kansa ya daukar mata da sukaje American .
sai gashi da tasa kmr dan ita akayi yana mamakinta matuka dresses girl ce and she knows how to dress wanda baza ka taba cewa cikin hausa gurumada aka haifeta ba.
idan tayi maka wani dressing din baza kace inna da mlm abu ne suka kawo ta duniya ba.
ko zani daya bbu akayan data tarar sun sai mata Amman bata wani damu ba .
ta iya sa kowanne daga cikinsu Allah ka azurtani da soyayyar ki Aisha ya fada akasan ranshi yana ta sauri ya kammala da aikin dady kafin su isa gobe haka ne yasa yaki bi takanta dan yasa dayaje gareta bazai kuma tunawa da wani aiki ba.
dan haka' ya sake dukufa dan aikin dady na da mahimmanci a tare dashi .
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......