[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Bismillahirramanirrahim
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai :GAISUWA
Gaisuwa gareku kawayenaHauwa musa mai kaji
Faiza Muhammad (bsbs)
Jamila ismail madubi
Hadiza lawan (MMN 2)
Fatima lawan (MMN illima)
Saudatu bello ambursa
Saadatu aminu (MMN fadil)
Alherin Allah ya kai garekuPage 1
Kwance take cikin dakinta ,wanda asalin nan mahaifinta ke Tara abinci idan ya noma , yanzu girman da tayi hade da rashin Tara abinci ya sanya ta gyara shi yazama dakinta ,babu komai cikin dakin idan ka dauke karamar katifa datake kwana akai kwatankwacin ta yan makarantar kwana ,sai akwatin kayan sawarta ,sai karamin tablet wanda yawancin text book dinta ne na makaranta da novel zube a kai.karkashinsa kayan shafawartane cikin dan karamin basket can gafe Kuma sai ghana must go da ta zuba littafanta da abubuwa ta masu mahimmanci bayanta ta zuba takalman ta nasawa sai ROG shinfide a tsakar dakin a gyare yake fas .yayin da dukufa nazarin wani novel 2 friend tana mai tausayawa dayan abokin ciki yadda aminnsa yaci amanarsa murya sakina kawarta tajiyo a tsakar gida suna gaisawa da innarta ,bata motsa ba har sanda sakina ta shigo dakin ,kayan da ta rungumo a hannunta su ta zuba mata ajiki , kai A bahindi ba kyau ke indai fita zaayi sai kinyiwa mutane delay sakina ta fada .batace komai ba kayan tabi da kallo sannan a hankali ta tashi zaune ta jingina da bango dakin sakina tace dan girman Allah ki Mike kada ki sake kwanciyar nan kmr ruwa 💗💗💗💗
Aisha wacce sai yanzu ta kalli sakina tun shigowarta tare da fadin "ya Allah duka biyar saura Amman jikinki har rawa yake .
Harara ta buga mata kinmata bori nike Hawa murmushin tayi har wushiryarta ta fito tace am sorry please 4 give me 20 minutes Yi hakuri dan Allah har tashiga wanka ta fito sakina bata bar mita sanyi jiki irin na Aisha ba , Aisha ko murmushin kawai take mata sai byn tagama shiri tana fida da kayan dazata sa ne sakina tace ganaki anko shi zaki sa AISHA tajawo ledar da Aisha tashigo da ita ta bude kananan kaya ne sakina tace tsarabar abbana ce Aisha tace Abba har yadawo ai mun gode sosai sannan dago ankon bikin dikin yayi kyau sosai sai dai rigar zata dan kamani ai fa inji sakina ko mama sai da tayaba Amman ke kinkushe sai kace matar ustaz ko me yasa kike son sanya Kannan kaya ?
Ai wannan a gida ne ,inji Aisha tacigaba yayin da bata sake tanka mata ba ta sanya kayan Amman sai da ta daura after dress akai saboda ita arayuwar ta tsani kaya ya matse mata jiki tafi son a fito mata da Shep din jiki .
Sakina ta dan tabe bakinta it's ok hakan ma yayi kinyi kyau kmr nazama ke .jakarta ta bude ta fito da dan karamin glass fari ta manna mata tare da fadin wlh da shi zaki murmushin Aisha tayi saboda ta tuna rayuwarsu ta boarding idan daya ya rantse akan Abu dole ne dayan ya hakura yayi abun koda bayaso saboda gudun sanya shi kaffara a hankalinta tace tsammaninki bazan iya fita da shi ba kennan ,Jira mu bar gaban inna ko ina ne zan je dashi .
Byn Moto direban gidansu sakina kejansu sakina tace dan biya da mu hospital gun mama hauwa ,mama tabani sako Aisha tace har yanzu tana hospital ne ? Sakina tace Eh Amman naji ance gobe suke saran za'a sallameta .
Dayake asabar ce kowa da kowa yana da yanzu shiga shiga tun safe har dare , shiyasa suka tarar da yan dubiyar sosai hannunta sakina taja har bakin gadon mama hauwa suka gaishe ta tare da ajiye kula da suka zo mata daita ,Amman ke tambayar ta yadda su mamanta sukaje gida dazu sakina tace lfy ta dafa kan Aisha dake kasa tace ya sunan kawar ki ?Aisha sundan jima kadan sannan sakina ta Mike tare da fadin zo mutafi mm hauwa tace wani waje zaku ne sakina tace Eh wlh bikin Yar kawar mama Ake Aisha tace munce Allah yakara sauki to na gode Aisha agaida mutun gida .
Aisha tayi gaba dan ta tsani kallon da mutumin dake kusa da ita yake aiko mata dan yana daya daga cikin abinda ya sanya wani lokacin bata son fita saboda kallo ,idan namiji zai dinga kallonta sai taji ta duk ata kure .
Doguwar baranda da zata sauke ka har gaban harabar hospital ita suke kai ,sakina dan Allah kiyo sauri kinga fa shida tayi .
Har takusan bige mutumin sannan ya tsaya ta shige , Aisha kuwa sai ta dan dakata alamun tana jiran ya wuce bata kalli ko su waye ba ,ta dai gane Maza ne su uku biyu a gaba yayin da dayan yake biye da su ,sai da suka wuce sannan ta rufe sakina baya suka shiga mota direba ya hadu zuwa gidan biki .
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......