ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 63-64
Da sauri Abdullah ya mike zumbur jikinsa har rawa yake yana kiran dady....
dady kuwa tuni ya kashe wayar da gudu Abdullah ya fito Dr sagir ma ya biyo shi yana tambayar sa abinda ke faruwa.A airport ma haka yarinka yi gudu gudu sauri sauri suna yin arba da dadinsa kuwa ya kankame shi sosai .
tun sanda wannan tashin hankali ya faru sai yanzu Abdullah yaji hawaye sannan Dr sagir ya karaso shima da murnarsa ya risina yana gaisar da dady .
da kyar dady ya bambare Abdullah daga jikinsa saboda hawayen da yake bayason mutane su Gani.
Dady yayi mugun kaduwa da irin ramar da yaga Abdullah yayi .
koma yace ya lalace ,yayi duhu tamkar majinyaci shekara guda .
Abdullah bai iya jan su ba sai Dr sagir ne yayi tukin shi da suna baya .Bbu wanda yasan da dawowar dady a yau hatta shi kansa Abdullah bai sani ba sai da dadin ya nemishi a waya .
dan haka tun daga bakin get masu gadi gidan kowa ya fara yashiga taitayinsa .
duk da ita kanta mamin bata cikin cikakken haiyacinta Amman sai da dawowar dady ya dan tsorata .
bbu wani abu daya nuna na cewar yasan abinda ake ciki to sannan ne yake tambayar Abdullah ya nuna masa shi baya shiga part din kwata kwata .
ya dubi mami da ta shigo yana son karin haske cikin dakewa zuciya mami tayi masa bayanin halin da ake ciki har da bayanin a yau faiza ta tafi sokoto Amman jibi idan aka daura aure zata dawo.
ga mamakin dukkansu har ita har Abdullah din dady bai ce komai ba illa yace ai yayi kyau zumunci zaki hada .Ya dubi Abdullah kai yanzu ina kake kwana kennan Abdullah yace a gidan baki dady ya sake maimaitawa Abdullah ya amsa haka ne .
mami tace ai key din part dinsa sunan hannu teema faiza ta bata ajiya dazata wuce abin ya sake bashi mamaki .Dady yayi shr yana kallon mami ita kuwa ko gezau batayi ba .
sai ma ta tashi tayi ficewarta ,dady bai yi mata magana ba Abdullaha ma ya mike ,zai fita dady yace ya koma ya zauna sannan dady yanemi wayar side din su teema ya kirawo bayan yan mintina kadan sai gata ta sake shigowa a tun dazu da suka zo yi masa sannu da zuwa.
bai ce mata komai ba. Baya ga tambayar ta key part din Abdullah da akace yana gunta .
taje ta dauko ta dawo nan falon dady Abdullah yasa hannu zai karba Amman dady yace A'a .
ta Miko masa ya karba yace shikenan teema gud nig .
tana fita ya dawo da kallonsa kan Abdullah yace yashiga nan part dinsa ai akwai dakuna ya zabi duk wanda yayi masa ya kwanta a ciki.
Abdullah bai gane yadda Dady yake nufi ba iya tunaninsa shi dady zai bawa key part din nasa ya tafi can ya kwanta.
Amman sai yaga zura su cikin aljihun gaban doguwar rigar dake jikinsa.
Abdullah ya mike jiki a sanyaye yabi dakunan dake bangaren hagu da part din dady yake kwana ya shige ciki.Har gari ya waye dady bai runtsa ba .
ita kanta mamin bata sake neman sa ba a daren tunda tabar part din nasa .
da safe abubuwa suka cigaba da daurewa dady kai a game da mami .
ita dai kawai hidimar biki take gobe daurin auren.har Abdullah yazo ya gaishe shi ya sake ficewa gidan baki bai ce masa komai ba baya ga amsa gaisuwar da yayi.
Dama can ya kan dan zazzaga ma'aikatan gida lokacin zuwa lokacin to yau ma haka ce takasance tin karfe goma ya fito daga part dinsa .
gabadaya environment din gidan yayi clear.
tun asuban fari dan haka daga nan gidan baki ya wuce .Har yammaci ranar bai shigo gidan ba mami kuma bata nemeshi ba shi .
kansa Abdullah bai ji wani abu daga dad din nasa ba.
dan haka shima office yayi wucewarsa yayi zamansa dan yadda yaga fuskar dady yau ko magana baya son yayi.
shi ma acan ya yini duk da anan hutu gobe daurin auren manager koda Dr sagir yazo nenanshi shima sai can ya sameshi .
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......