ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 60
Faiza tace kai mama mutane nan fa sun wuce duk yadda muke zato fa.
ta koina abin arziki a jike yake .
ba ga mami ba ba ga uban ba hatta shi kansa Abdullah din mai tsansar abun duniya ne .Mama hafsa Tace ke sai yanzu kika san haka kennan .
ai shiyasa na tsarawa uwar duk yadda zasu bada sadakin kmr dai yadda suka bada na waccan Yar masu tatsan nono gidaje shida da motoci kinga ai an nininka kennan .Faiza tace kai mama kina wuta ina binki da fetir wlh ta Mika uwar hannu suka kashe. sannan tace ke in banda bana so abin ya wuce wannan lokacin ai da watar kasar za'a kaimu mu zabo kayan gado kinsan su masu fita ne .
Sun fi sanin inda za'a samu na garari .
Faiza tace dakata mama bangane maganar ki ba .. ai a hakan ma dole ne kayan kitchen lefe da sauran kayan duk a waje za'a siyo su.
ai ba wani batun dan za'a yi biki wani a kurarren lokacin.
tunda dai ba'ariga an soma raba AV ba.
me zai faru abinda ance shi dady sai yayi kusan wata hudu kafin ya dawo.
ko ana sauran sati ne ya dawo aka daura ai dai an daura.
kuma komai kwakwa da nacin sa dole ya hakura .
Mama hafsa Tace haka ne fa .
kinibabbe banza kawai , ai ni nafi son kisamu kmr wata daya da aure Abdullah akanki kafin yadawo.
sannan nasan mun dan fara tatsan abinda muka tatsa kafin yazo ya hanamu rawar gaban hantsi.
akwai abubuwa na musamman dana zan tsumaki dasu.
saboda Abdullah din dan haka ana daurawa ,zaki lillike masa ajikinsa sai yadda kikayi dashi .
idan ya dandana zumarki kuwa.
zai mannemiki har sai kindinga korarsa.Faiza ta saki shewa dan murna hade girgiza nonuwa irin dai yadda manyan yan iska keyi .
tace A'a haba dai mama bawani korarsa da zanyi ai sai dai na kwashi da....... can Kuma tayi shiru jikin faiza yayi mugun tsanyi tuno halin Abdullah datayi.
mama hafsa Tace karki taba damuwa naga kin wani canza kisha sha'aniki diyata .
idai Abdullah ne muna nan zaki zo har nan kibani labari komai.
kema ai yanzu kinzama babbar yarinya .
Faiza ta mike tana dariya har zata fita kuma ta dawo tace uhm mama kigayawa mami fa ni nafi son mu zauna acikin gidan nan a part din Abdullah bazan zauna a wani guri baMama hafsa ta kalleta a bazance tace meyasa ke tsamiyace .
ga gida can ke kadai bbu wani dan sa idon da zai dami rayuwarki da takuran yan'uwan miji.
komai kuma yayi a gidan sai abinda kike so zaki canza .Faiza ta dan sake rage murya sosai tace uhmmmm ke Abdullah din nan fa da kike Gani bai da kyau fa .
ni na fi son ko meza'ayi Gani ga uwarsa .
mai sashi yayi mai hana shi ya hanu .
yanzu kina ganin duk abinda aka sha wahalar yi a kansa idan ranar da aka kaini ma yaki zuwa fa gidan fa! .
kinga tun anan ma wani abun zai karye idan kuma anan ne fa.
nasan karyashi tasha karya dole mu kwana tare .Mama hafsa Tace kuma fa haka ne .
faiza tace ke dai kice mata ana zamu zauna kawai naga part din nasa ma wata aljannar duniya ce .Mama tace to ni ina zan wani san hakan tunda bashiga na taba yi ba. Kinga haka ma za'a yi bari kiga na koma gunta .
Kwana takwas kennan dayin maganar a maimakon ranakun bikin faiza .
mama hafsa da faiza da kanwar faiza rahma suka Lula waje hado kayan amarya mami ta bude musu account dinta sosai suyi yadda suke so .Abdullah Yayi shr kansa a sunkuye byn ya gama jin abinda mami ta fada cewar ya rubuta takardun gidaje gudu shida da motoci hawa guda shida a matsayin sadakin faiza.
kansa har ciwo ya farayi saboda girman al'amarin Amman ko dagowa bai yi ba yace shikenan mami za'a yi yadda kike so.Fita zai yi Amman ya kasa dole ya dawo part dinsa ya kwanta.
yayi shr kullum abin ma gaba yake yi bbu wani sauki acikin al'amarin.
sai randa Allah ya kawo .
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......