16

1.2K 73 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 16

Alhj ishaq ya isa asibitin tare da securities dinsa yayin da police suke tare dashi har cikin dakin da aka kwantar da Abdullah   yakarasa kan gadon " Abdullah dinsa ne kwance bbu inda ke motse ajikinsa da oxygen a hancinsa  sai bandejin dake daure a tsakanin kafadarsa da hannunsa sai kansa daure shima da bandage har yanzu jinin dake zuba a wajen kansa  bai dai na zuba ba... ,...

    Dady ya runtse ido sannan ya sake budewa tabbas Abdullah din nasa ya sake gani acikin wannan halin" kwance rai hannun Allah ya juyo yana tambayar doctor daya karbe shi
      Likita ya soma masa bayani yadda abun yake Abdullah ya bugu sosai ga kariyya a kafadarsa sakamakon kokarin fitowa daga motar bayan  ya bude kofar lokacin da abin ya faru sai raunikan dake kansa da kafadarsa sai buguwa da kirjinsa yayi har ya janyo masa matsalar fitar numfashinsa ,.. dady ya sake zubewa a gefen Abdullah har yanzu baisan ida kan sa yake ba "dady yace Abdullah dina ne da duk wayan rauninkan ya runtse idanunshi yana karanto duk wata  addu'ar  samun natsuwa ,ya Mike ya fito police suka biyo shi abaya suna sake mishi bayanin yadda al'amarin ya faru...

A ranar  dady yasa aka masu visa zasu fita Germany dashi domin can ne kadai dady yake ganin zasufi duba masa Abdullah dinsa da karayar daaka ce yayi ,,, har daren ranar yana tare da Abdullah Amman bai farfado ba Mami ma takasa hakuri sai da taganta asibiti su duka ,sanin idan suka wuce da Abdullah damuwa zatasa mami ita ma  kamuwa da wata cutar yasa dady ya shirya visa har da ita washegari ranar da safe suka bar Nigeria yayin da akabar su teema a gida .....

Koda mlm yashigo  Aisha na tare da inna ta Mike shi kuma mlm abu ya zauna yana wa innarsu bayanin zuwan Abdullah da maganar da suka tsayar kan gobe za'a mai da musu da komai nasu na aure inna tayi shiru tayi tagumi da hannuta daya yayin idanunta ke kan mlm abu tashiga matukar tashin hankali wai Abdullah dan dan uwanta kennan danta ne halak malak ita ko yaushe zata bari a ayi auren  nan gara dai ayi hakuri da abun kawai "wata zuciyar tace to in kuma  wani abu yasame shi tasadin haka tasan dole zai shafe dan uwanta ita kuma batasan ganin   tashin  hankalinsa,alahakikanin gaskiya ita me son yanuwa ce balle shi kadai gareta duk da bai damu da ita ba tasake Jin sukar wani wasu hawayen da duka fi na dazu ciwo"" Amman takan mai uziri saboda rashin bai dace da macen kwarai ba, mlm abu ya jijjiga kai yace narasa gane kan ki tun  zuwan iyayen Abdullah gidan nan ,kinki  sanar dani damuwarki. munsaba raba farincikinmu tare haka ma akasin haka to meyasa zaki boye ?"duk da cikin duhu ne hakan bai hanasa ganin hawayen dake bin fuskarta ba, sannan cikin yin kasa da murya dan batason Aisha tajo mai zata ce dan tasan idanunta ta biyu "  nan dai inna tayiwa mlm bayanin komai tun daga zuwan ta gidan alhj ishaq din bayan wani zuwa da sukayi ka'oje , mlm abu shima yashiga rudani matukar maganar ta jijjiga sa kwarai kasa cewa komai yayi sai ma shigewa daki da yayi yana mamaki da alajabi wannan hadin sai yanzu ya iya cewa ikon Allah kennan ....

Tun bayan shigowar mlm abu da kmr awa daya har yanzu idanunta biyu hakan nan duk da tana kwance bata da wani  cikakken kuzari ajikinta tun byn faruwar abun har zuwa yanzu takasa raba kanta da dogon tunani ,komai akan idonta da kunneta aka fara aka gama  dan haka duk wani tashin hankali da iyayenta suka shiga sai dai ta bawa wani labari "abin  yaki wuce mata arai ko dai dai da second daya zubar hawayen inna a dalilin aurenta ,wanda tun randa tazo duniya bata taba ganin ba ,ta yarda idan tashin hankali yayi yawa hawaye ma basa zuwa dan haka ta gwammace da ma kukan tai tayi da abunda ke damunta a zuciya,ita daman tun zuwan Abdullah gurinta ta gane wani karan tsaye ne a rayuwarta duk wannan maseefar da yawan tunane tunanen da take Yi bai hana bacci lallaba idonta ba ya fige ta na mintina uku ....wata mumunar faduwar gaba ce ta farkar da ita ta Mike zaune ta dafe kirjinta hade da mai da numfashi sama sama gabadaya jikinta rawa yake  Amman duk da haka gabanta bai dai na harbawa ba "a hankali ta dinga karonto innalillahi wainna ilaihi rajiun...ta jima tana maimaita wa sannan ta dan samu sauki da natsuwar zuciya. iya tunaninta  batasan me yasa gabanta yayi irin wannan faduwar ba , haka  nan jikinta baya bata wani abu na shirin faruwa da ita tunda bbu wanda tayiwa laifi sai dai ko daga Allah ne tashi tayi ta fito a hankali ta dau buta tayi alwala taxo ta shimfida pray,mat tafara nafila....

Duk motsinta akan idon innarta ne ,tana Jin tausayinta dan tasa damuwa sosai aranta ,har  ramewa tayi  inna tasawa ranta hakuri da dangana dan ko ba komai Abdullah bata ba yadda zatayi  kallon da inna  take wa Aisha yanzu yasake sawa ranta kiyyayar maza fiyye da da  dama can tana kukan targade sai ga Karaya....
.

aunty Maryam takan aiko Aisha  taje Amman da ta lura idan taje tana yawan mata zance Abdullah sai ta daina zuwa ko ta aiko saboda ita yanzu haka kawai taji ko sunanshi bata kaunar a ambata a gabanta ....

Su mlm abu basu samu damar zuwa gidan alhj ishaq ba a washegari da Abdullah yazo kmr yadda mlm abu ya shedawa Abdullah sai bayan sati daya saboda zuwan da mlm dahiru zai yi daga ka'oje ...

Tun a get din gidan abin yasake kwancewa mlm dahiru kai  yayinda mlm abu yake sakawa ransa yanzu duk wannan tambatse tsen gidan  na yayar matarsa ne Killa daman can wata manufa da yaudara ce akazo neman diyarsa dashi ....

masu gadi suka tare su ko ciki ba'abarsu sun leka ba bare su hangi  cikin gidan byn gaisuwa mlm dahiru yayi bayanin suzo neman mai gidan ne , to Amman tun daga yanayi kallon da masu gadi suka yi musu Jin cewa me gidan gabadaya da kansa suka zo gani suka sha jinin jikinsu bbu wani cikakken bayani da masu gadi suka musu daya daga ciki yace to kujira zaku ganshi sannan yayi shigewarsa ya rufo  get dayan ne ma yamusu bayanin yace gaskiya zan sanar daku ba'a zuwa ganin me gida kai tsaye sai tare da wata sheida ,ko da shidar ma sai anyi waya an sanar da mu in yaso idan kunzo  sai musanar aciki ,a halin yanzu da ake ciki mai gidan baya ma kasar sabida haka dan Allah kuyi hakuri ku canza wani bangaren ....

Su mlm abu sukayi masa godiya suka wuce  kowane zuciyarsa da abin da take sakawa...

Magana dai akan  bbu me sake taka gidan  ,ko ba dade dai   sun zo neman kayan aurensu sai dai idan suka ji shirun yayi yawa ,abida mlm dahiru ya yanke kennan duk da mlm abu bai sanar masa da kowaye mahaifin Abdullah ba yafi son sai komai ya warware tukun  ....

To shima dai alhj aminu a dawowar dayayi ya riske yadda al'amarin yakasance  mamaki ne yacika shi,shi kam cewa yayi kada abiyewa al'amarin mata kawai ajira daga uban yaro dan ko ba dade zai waiwaye su .........

Manage please may be ku sake jina anjima

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 17

Likitoci sun rufa akan Abdullah tun saukar su Germany,hankalin da

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now