45

1.2K 61 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 56-57

Da farko Kamar bazatayi  laulayi ba, Amman kwanaki kadan laulayi yazo ya sata a gaba ko  ruwa tasha baya zama acikinta.
gashi duk nisan abu idan ta kafa ranta shi zata dole taci dan idan bata ci ba sai taji duk cutar duniya kanta ta dawo ,.

kuma har dare bazata iya cin komai ba idan ba shi din ta samu ba wani lokaci har kuka take yi  .

Gashi duk kinta da tunanin Abdullah sai da maraicinsa ya taba ta.
duk ta rame ta dashe tayi fari fat.
idan ta fara kakarin amai  kuwa tamkar hanjinta zai fito.
magana ma wani lokacin da kyar take iya yin sa .
  da kafar  ta ma tafiya take dan yawancin duk unguwar an san da a yanzu tana gidan maganganu kuma  iri iri bbu wanda baya tar dasu.

Ita sai daga bayan nan taji bayan tafiyar su da Abdullah.
dadinsa ya dauki nauyin  hidimar makarantarsu yaya yusif  da duk abinda zasu bukata.
akwai mutun na musamman da aka daura akan haka .
a yanzu  haka  akarkashin I M sidi magaji yaya Ali ya tafi NDA Kaduna ,.

sai gidanjenta wanda aka mallaka mata cikin sadakinta wanda tun bata dade da dawowa gida  ba, da mlm abu yamata maganarsu .
Amman tace ita wlh gabadaya tabar musu Amman suna nan a rufe har yanzu ba abinda akayi dasu .
takardun ma  suna gun alhaji aminu .
motoci kuwa ko yau suke so za'a kawo musu daga company dan haka duk wannan a idanun mutane suke har yau surutai ake a gari ballanantana da yanzu aka ga tana gida .

Aunty Maryam tazo da yammacin wata lahadi suna gaisawa da inna daga kitchen inna ta fito sai da ta samu gurin zama sannan take mata bayanin .
yawan zuwan da Doctor  nan yake yi.
inna yayi shr tana sauraronta hade da kallonta aunty Maryam.
cikin tuhunna  inna tace nifa abin har tsoro yake bani kullum ne sai yazo wai yazo dubiya ai ina jin kalla yazo   gidan nan ya kai  kusan sau  talatin. Mlm  ma da kansa abin ya dame shi .

Aunty Maryam ta dan langwabar da kai tace to inna yaya zanyi.
na rasa yadda zanyiwa doctor "can ma idan kinga yadda yake yi min sai kiyi mamaki "tun bana bi ta kansa har na hakura.
  shi  inna wai ita yake so da aure har cikin dake jikinta .
inna tayi murmushi kawai dan ita har yanzu ranta Abdullah take so da diyarta ,aunty tace baki ga abinda abun ya zame masa kmr wani ibada yazo kullum ya tambayi lfyr ta  a gurina kafin ya fara aiki.
,har na rasa yadda zanyi da nacinsa .
inna tace haba nasan za ai haka abin yayi yawa fa da idan zaizo fa ke baki ga abinda yake tahowa dashi ba .
  daga baya da muka fara fahimtar haka aka daina karba, aunty Maryam tace wlh ni kaina basan ya za a bullo abin ba ,.
gashi da bin diddigi maseefa ni fa kawai zuwa ya yi yace min wai kuna gaishe ni .
ban san ya'akayi  yasan gidan nan  ba ..

Inna tace a to rayuwa kuma iri iri kowa da irin tasa  Amman shi yana daukar abu tamkar yanzu  ne ,.
dan wani lokacin idan yazo ma bai ga  kowa a kofar gida ba .
sai yafi awa  bai tafi ba aunty Maryam tace ai shi bai ki da cikin a daura musu aure ba ko ayau ,inna ta rike baki.

Aisha na daga daki tana jiyo su ita dama ta dade da gane hakan .
tun a ranar zuwansa na farko da inna ta matsa ta je tsoro wai yazo ganin jikinta.
yana mata yan tambayoyi akan jikin Amman ta fahimci sarai me yake nufi .
ta Kare masa kallo tsab ,bai da laifi  sai dai  Abdullah dinta ya fishi komai nisa ba kusa ba ,shi Abdullah ma  dazakaga jikinsa tamkar na bby sabon haihuwa sabo tsabar kyau gashi gentle man .
Amman shi wannan sai tsari da iya magana kmr wani lauya.
haka ta karaci kallonsa ta bar shi nan tsaye .
daga ranar ko magunguna ya aiko tasha na masu ciki bata sha  sai dai tayi wasi dasu dan ita basu take so ba tafin so ta jita karkashin Abdullah dinta ta lumshe  idanu sakamakon yadda  tarinka jinsa  yana yawo  ajinin jikinta .

Aunty Maryam ce ta shigo ta katse mata tunani .
ta zuba mata ido tace kai Aisha haka kika kara zama dubi idanki fa .
Ta riko hannuta tana dubuwa .
tace har kin fi da dashewa fa duba kmr mara jini a jiki.
inna takaraso da kunun tsamiya data dama mata tace nima dai kallon haka nake mata aunty tace wlh ma haka ne inna ai sai muce
tare kawai an jima in yaso da safe muje asibiti a dubata.
cikin muryar kuka tace ni aunty ki barni kawai ba inda zan je wani dube dube  .
Aunty Maryam tace ji ikon Allah kina cuta kina cewa a barki .
kinsan ma ko ba haka ba yana da kyau ki dinga zuwa asibiti saboda abinda ke jikinki .
Aisha  ta bata rai tayi sosai tace nifa bazani ko ina ba a barni.
har aunty Maryam tayi fushi daita.

Washegari  ne su  gwaggo laure da matar  mlm dahiru ne    suka zo  dubata yadda matar mlm dahiru taga jikin gabadaya cewa tayi  zata wuce daita can ka'oje saboda yinin ranar cur ciwon ciki ya dawo sabo ko iya tashi batayi.
ga bala'in yinkurin amai tamkar dan zai fito ta baki .
dan ita gwaggo laure dan tausayi har  kuka tayiwa Aisha.
ranar da zasu Wuce da safe takin cin komai ga yunwa tana ji kmr tayi hauka komai wari yake mata in dai a gidan aka dafa shi .
a sa'a sai ga aunty ta turo mata da dafaffen wake da kawai da ganye shi ta dan samu taci tana murmushi tace  aunty ta huce kennan .
inna matar mlm dahiru kuwa da taga taci sosai  sai kawai ta juye mata sauran acikin Leda suka wuce.
Amman kafin su kai ka'oje  duk sai da bata ina motar   da amai saboda warin man mota da yake cika mata ciki .
a motar har wasu na jin haushin yadda take bata musu guri.
yayinda wasu kuma ke tausaya mata .

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now