11

1.4K 85 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 11

Washegari ma yazo sai dai bai wani  dade ba ya tafi ,byn ya matsa mata akan me take bukata koda tace ba komai ya daure fuska gabadaya sai taga yanayi sa ya canza ,yace dan bata damu da shi bane shi yasa bata son wani abu daga gareshi ,da Kyar ta iya ce masa ko menene sannan ta samu lafiyarsa ya tafi Amman  duk da haka bai saki ransa ba, dan shi ji yake tunda ta amincewa aurenshi duk wani nauyi nata yakoma kansa .ranar sunan aunty Maryam bby ta amshi sunan maimuna wato sunan innarsu tun alokacin ake kiranta da khairat .

Tun wajen goma sakina tazo Aisha ko wanka batayi ba saboda bakin da suka agidan  bandakin  tashiga  ta fito da ruwan wanka  bayan gida  tajata suka zauna akan kujera ta kawo mata dan abinda aka gama cikin jin dadi da murna tace sister Amman sai dare zaki tafi ko ? sakina tace nan da zuwa Shabiyu zan tafi shi yasa nazo da wuri zan raka mama unguwa ne tace kai sister sakina tace Allah kuwa namazo miki da albishir din result ya fito Aisha ta dafe kirjin ta ce dan Allah  tace da gaske can kuma jikin Aisha yayi sanyi sakina ta tambayeta yana ga jikinki yayi sanyi" taja tsaki ni wallahi wannan Abdullah din shi zai takurani da Kyar  zan Yi ma karatun.sakina ta kalleta kawai tacigaba da wata maganar daban dan batason jin zance Aisha ta lura da yadda Aisha tadan sauya akan Abdullah yanzu ,Amman itama sai tashare tacigaba dayi mata wata hirar sakina ta zuba mata Ido ,wani haka yake da sa'a a rayuwar sa ta tuna jiya gurmin da aka sha agidan su akan ita Aisha a dalilin abbansu ya sanarwa da mama cewa shi Aisha  yake so ya hada da yasir ,mama tayi tsalle ta dire tace sai dai byn ranta Amman baza a hada" da" da wannan yarinyar mai kama da karuwai ba ,Abba yaji haushi har yamayar mata  ai shiryuwar dan naki shine a hada shi da ita dan bakinsa abinda yake aikata acan ba, ai ko ta hau shi da maseefa yana zagin danta yace inkinga bai aure ba daman can ba matarsa bace aurensu shine kawai zai sa yadawo ya zauna ya daina tara matan banza a can ,ina dawowa zan sami mahaifinta kan maganar Aisha ta bugi cinyar sakina ta ce kai sister ina aka tafi ne tunanin kuma fa suka dariya ?
Ta kalli Aisha ko wanka batayi ba Amma tamkar wanda ta tsala kwalliya kullun kmr sake kara mata kyau akeyi ,jiya da yamma sunka je salon ita da aunty Maryam itama an gyara mata gashinta sosai kanta bbu dankwali ta rataya dan guntun towel a wuyanta sakina tace dan Allah sister ki tsaya ahaka ta fito da Yar karamar camera tace zakiyi wallahi sai kin tsaya na miki hoto Aisha dan bata fuska tayi  kai sister a haka zaki wan.... bata gama magana ba har ta dauka  da yamma  tashiga dakin Aunty dake cike da kawayenta yawanci duk Yan wajen aikin sune ta gaishesu,aunty tace ga sako nan Abdullah ya aiko miki zata dauko mata tace barshi kawai aunty sai zuwa anjima ,ta fita wata daga cikin kawayen aunty tace kai wannan kanwar taki zaayi yanga Maryam kinga da Kyar take magana  tayi dariya tace wallahi ba yanga bane nature dinta ne kawai haka  wata tace ai idan ma tayi yangarma zata ci riba tunda tana da kyau da abubuwan yin yangar.

Alhj ishaq ya kalli dan nashi ya kira sunansa cikin sanyi  yace Abdullah daman abinda ake so hali na gari ga kowane dan Adam to ALHAMDULILLAH anyi shedar yarinyar da iyayenta tun daga kan makwaftansu har zuwa can  ka'oje inda aka haifin  mahaifiyarta  , mahaifiyarta itace kawai Diya sai dan uwanta wanda daba'asan inda yake ba  wasu Fulani rigar dake can "sidi magaji )ne  Amman duk da kakaninta na wajen uba ba'anan suke a ka'oje ba Killa ma da iyaye da kakanni suna nan  raye da zasu San juna dan nima da kaganni asalin tushena kennan ka'oje cikin kauyen (sidi magaji) kmr dai yadda kasani  sana'ace takawo mahaifinta nan mlm abu
Shedarsa itace talaka ne mai godiyar Allah suna  zaune da matarsa uwar yayansa itama kuma Anyaba mata sai yarinyar data Kare karatu a makarantar yan'mata dake  federal gwandu abin farinciki ,nagarta kamun kai da kokarin yarinyar yasa har tayi suna da aka santa a makarantar sosai ita ta rike shugaban dalibai dady ya dan tsagaita to daman wannan ake so a duk wani iri da'ake nema .

Dady ya janyo wasu hotuna guda biyu ya zuba masa a gabansa to Abdullah dai wani iri yake ji  ajikinsa cikin sanyi jiki ya dauki hotunan yana dubawa hotunan  Aisha ne sanye da uniform tare da yan'uwanta  dalibai  sai teacher dinsu sai Kuma dayan  gurin wani daurin aure ne yagano mlm abu zaune a gefe shi da wani Abdullah dai yakasa magana dady yacigaba abinda na nunawa mamin ka kennan tun  dazu ,nagarta yarinyar ta fito kuma  shi zaisa a yada zuria ta gari  dan haka tunda an samu wannan sai ature duk wani rashi tunda bashi ake bukata  aure ba, ahankali yake kallon dady tamkar yasaka masa kuka farinciki haka yakeji ,dady na sonsa dan yadamu da damuwarsa alhaji ishaq yagama karanto hakan a fuskar Abdullah ya girgiza kai kasanar da iyayenta zanzo da kaina in ne ma maka aurenta murmushin Abdullah yayi dan tsabar farinciki, yana fadada  murnarsa a fili yace thank you dady
Yace bbu komai tashi kaje ya fita yana rayawa aransa dadynsa ya dauki Aisha'rsa da mahimmanci da kansa zaije ya nema masa aureta sabanin yawancin abubuwa sai dai ya wakilta aje .

Tsantsar mamaki ne ya rufe mami to ita har yaushe Abdullah ya samu yarinyar dayake so batare da ita din tasani ba har  zuwa yanzu dayake gabanta kallon  mamaki take masa tace Abdullah tsawon wani lokacin kuke tare da yarinyar a garin nan batare da na sani ba Abdullah  yayi shr ya fuskanci yadda mami ta dauki zafi akan maganar tace bazai yuwu ba  dadynka yayi bincike akan yarinyar dole nima zanyi nawa  bincike  daban ,tashi kaje zan nemeka Abdullah yayi shiru kwance yake kan doguwar kujera   a falonsa ya harde hannuwanshi a kirjinsa yana tuna maganganun mami ko me mami zatayi shi dai  ta ceceshi ta amince ya auri Aisha shine kadai kwanciyar hankalinsa da samun lafiyar a rayuwar sa .to har yau dayadawo daga aiki yaje gurinta abubuwa biyu sun cushe masa farinciki da damuwa dady da mami ,yana matukar tsoron mami yadda  tanuna rashin son ta akan Aisha  yasan mami sosai idan ta nuna......

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now