ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 43-44
Suna isa kai tsaye aunty Maryam tasa aka wuce daita gurin likita .
Doctor salim shine akan duty da haka da saurinta tace doctor taimaka kanwata ce bbu lfy mun rasa gane kan ciwon nata .wani irin ciwon ciki ne yake damunta .
Ita kuwa Aisha a lokacin ji tarinkayi tamkar mutuwa ce tazo mata saboda balain ciwo dake ji ajikinta sai zufa take hade da tsinkewar zuciya .
Tayi sharkaf a gado dr salim ya karaso kanta ya zuba mata idanunshi sosai tayi kmr batasan yana kallonta ba nan da nan yace a sauya mata daki .
Yaba ta taimakon gaggawa , ya jima yana checking dinta sannan ya daura mata drip din magani .
Allurar bacci aka mata sannan ya fito yana sake tambayar aunty Maryam game da ciwon tana masa bayani a karshe tace bari taje tayi reporting a bangaren su ta dawo.Dr salim ya dawo dakin ya zuba mata idanunshi sosai bacci take Amman daga Gani tana jin jiki ya dinga kallonta kmr wata halitta ce da bai taba ganin irinta ba . tamkar diyar wasu manya ko kusoshin gwanati a cikin Nigeria .
Ya jima yana dube dubensa da aune aunensa Amman gabadaya kacokan hankalinsa ya daura akanta .
Ragowar marasa lfy ma wani likitan ne ya karba .
Hatta scanning shi yayi mata sannan ya dibi jininta ya auna..Aunty Maryam ta dawo har kusan uku yana nan gurin Aisha sai da zai tafi sallah ne ya fito ransa a dan bace yana nannade hannu riga zai yi alwala yake cewa aunty Maryam .
Kikace sister din kice yarinyar nan tace kanwata ce mana doctor me faru daita cikin fargaba ta amsa masa ya sake dubanta yace tana da aure ne ?.Aunty Maryam tace tana da mana amarya ce ma yace ina mijinta ?
Aunty tayi Jim na wani lokaci sannan tace bayanan yayi tafiya me yafaru ne doctor ta fada jikinta na rawa .Ya kara bata fuska sannan ya kauda kai yace ciki ne daita bai kai wata daya ba ..
Yacigaba akan samu wasu mata idan sun samu ciki sai suyi ta ciwon ciki .
To itama ina ganin tana cikin wannan jarin Amman duk da haka ya nuna ta Sha wani abu ne wanda bai kamata ta Sha ba shine ya sake janyo abun yayi worse har cikin yake kokarin zubewa .
Amman Allah yasa bai fita ba .
Dr salim ya numfasa yace sai a kiyaye .Ya tsugunna zai fara alwala aunty tayi gaba da sauri zuwa dakin da aka kwantar da Aisha tana zubda hawayen tausayin..
Dr salim yayi shiru yakasa alwala yayi matukar bakin ciki jin matar aure ce duk tunaninsa bata da aure koda ya fara aunata ya gane tana da shigar ciki .
Sai dai ya rantse ko cikin shegene daita yana sonta haka..
Bai taba ganin yarinyar da ta tayar masa da hankali lokacin guda ba sai ita .Komai nata irin wanda yake so ne , tunda ya zauna kusa daita kamshin jikinta yake shiga hancinsa da gangar jikinsa shi yasa har bai so fitowa ba .
Yaso yakasance tare daita yayi ajiyar zuciya ya dafe kansa yace kai..Kai Kai har sau uku sannan yace Amman dole na bincika idan bbu yadda zanyi dole sai hakuri kowaye wannan mijin nata yamasa shigar sauri ya ja tsaki .Aunty Maryam ma har jikin gadon takarasa tana baccinta ta zauna a gafe ta ruko hannuta ,tana kallonta da irin balain kyan data kara ga ciki . Amman Abdullah ya saketa meyasa ? komai ba jikinta ya canza hatta gashin kanta yafi da tsawo ,fatarta tai balain gogewa daga Gani Abdullah ya jiyar daita dadi Sosai .
Ta sake kallon fuskarta tace yanzu cikin Abdullah ne ajikin Aisha ?tana maganar tamkar wanda Aisha ke jinta sai kuma tasa tana goge hawayen dake xubo mata ...MMN
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......