ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 55
Bai san iya adadin cup din coffee da yaje sha a kullum kafin yabaro office.
Hotonta yana nan a bude a system dinshi ,shi ke tayashi hira da debe masa kewarta a duk sanda soyayyarta ta bijiroma masa , sannan yake samun ya gudanar aiyukansa .Dady da kansa yace yadinga yin haka domin ya zama jarumi a office ko idan yana kallonta zai iya aiwatar da komai cikin natsuwa "batare da ansamu wata matsala ba .
Kiran dady ne yashigo wayarsa ya daga yana kallon hotota yasa hannu yana shafa beauty face dinta .
bangaren dady kuwa cewa yayi mhm Abdullah tell me tun safe zuwa yanzu sau nawa ka tuna Aisha?
Abdullah ya dan ciji karshen Biro da ke hannunsa yana tunanin. yayi dan yi murmushin takaici yace sau uku ne ma kawai.
shima sai yanzu dana bude system da rufewa nayi saboda ina son kammalawa da wani aiki ne .Dady yace da kyau yarona kaga daga goma Sha ya fara raguwa gashi ya dawo sau uku .
Abdullah ya sake yin murmushin kadan dan shi kadai yasan halin da zuciyarsa ke ciki game da rashin matarsa ya dau cewa dady haka ne kawai ahankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yacire white glass din dake manne da idaonsa.
ya jingina bayansa da kujera yana jujjuyawa ahankali manner da wayar a kunnesa yace dady akwai hanyar dana gano wacce tafi waccen saukin fahimtar komai ina ganin itace zata kawo karshen komai da muke bukata .
dady yace da kyau ina jinka Abdullah yace sai zuwa anjima idan na koma gida zan maka bayanin komai .
Da sauri dady yace shikenan sai ka koma din"Abdullah yace yauwa sannan yakashe wayar .Yana juyowa ya sake ya zuba mata idanunshi yace kin gani ko Aisha komai na rayuwata ya canza, narasa farinciki da sukuni tun sanda kika tafi kika barni .
bana son a bani dariya saboda bana son nayi ,dariyar ki kawai nake so a tare dani .
gashi dady yace kada naje gareki ni Abdullah ya zan yi da rayuwata komai ya taru ya cakudemin waje daya.
rashin ki kadai ya isa ya tarwatsani .
shi kadai yake maganar shi tamkar wani zararre .
kawai idanunshi ya gane masa tana yi masa dariya ta cikin system dinsa.
ai ko yashiga danne danne a jiki yana sake neman ragowar hotunanta wai shi lallai sai yaga wushiryarta data yi masa dariya yanzu.
har sanda salis yashigo da coffee ya ajiye masa bai san wani duniya yake ba .
Sai can hankalinsa ya dawo jikinsa .
Gashi lokacin tashinsa ya kusa Amman baya kaunar abinda zai saya doshi gidan. sai yarinka jin gabansa na wani irin faduwa" tun kwana biyu da faiza da mama hafsa suka sauka a gidan,
yaji gabadaya baya son kusantar gida dan haka gurin Dr sagir kawai yace a wuce dashi dan shi kadai yake tayashi hirar Aisharsa in ba cin dady ya hana aje da tuni Dr sagir ya je masa gunta .
to zaune agun Dr sagir ne mami ta neme shi a waya" dan tasan lokacin tashinsa yayi daga office tashin hankali da mami ta sake jefashi da yaje kiran nata yafi wanda yake ciki a halin yanzu .
dan magana ce akan faiza ita dai lallai ita take son ya aura Kuma tana son ayi komai kafin dawowar dady .
Tana son faiza ta zama matarsa ta hakika .
mama hafsa dake kusa da mami ta kara tabbatar da hakan suke bukata ayi auren da wurwuri .Abdullah ya zubawa maminsa ido shi kansa ya amince tun ba yanzu maminsa na matukar kaunarsa fiye da komai .
a tun sanda batun aurensa ya bulo ta sauya masa kar dai mami ta tsane shi ne ayanzu yaji gabansa yayi wani irin faduwa da sauri ya kauda wannan a ransa saboda dady ma ya hana shi ganin laifin mami yace yin haka bbu kyau .Yarigada yasan halin dadinsa dan haka sai daya gama yi masa dukkan bayanin tsarin daya shirya game da masu son salwantar musu da dukiyar .
dady yayi shr yana jinjina kai yayi Ammanna da shirin Abdullah din.
da yaba masa Sosai da irin dabararsa a karshe har yayi masa godiya dasa masa albarka.
Bangaren Abdullah kuwa ba wannan ne a zuciyarsa ba .
dan haka yana gama jin dady shima ya dora akan sanar da dadinsa halin da'ake ciki na game da maganar auren faiza da ake ciki .
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Lãng mạnzuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......