shine ta bawa Aisha ta tura gashinta cikin farar hula , Amman saboda yawan gashin sai daya burtso ta baya da wanda yabi gefen fuskarta tananan tsaye taji murya mlm dahiru yana Bismillah.
Juyawar da zatayi idanunta suka sauka akanshi tare da wani suna shigowa kamshin turaren su tuni ya game gurin cikin shiga ta alfarma,"sanye Abdullah yake cikin farin voyal mai ratsin gidan sugar dinkin doguwar Riga zuwa gwiwa kallo daya zaka masa kaji yayi matukar birgeka , cikin sanyi jiki Aisha ta juya ta shige daki,abdullah da Dr sagir ne a zaune kan tabarma suna gaisawa da inna hajo tace ai bangane mijin nawa ba acikin ku,naga duk kun shawo min kwalliya Dr sagir yayi dariya ai kowa so yake ki zabe shi , sannan ya nuna Abdullah . Abdullah ya sunkuyar da kai "Inna hajo
Tace Af to kai me ya tsaya birge ka da wannan mai karamin bakinta koko muryar ta ne mai kama da ta gyare ce ta dauki hankali ka ,sukai dariya gabadaya tace Allah in kuma ma jar fatar ce kai ma ga ka nan da ita" Dr sagir yace kodai ya fasa da ita ne ya dawo gunki tace ashe dai kagane ".suna zaune
akarinka shigowa da kayayyakin tun daga bahun Hunan shinkafa taliya makaroni sabulai abun dai tamkar za'a bude shago"tsarabar su Abdullah kennan mlm dahiru yarasa inda zai saka bakinsa dan gaskiya ya yaba da Abdullah yaji ya kwanta masa a rai cikin lokacin daya "kyautar kudi kuwa Abdullah tamkar wanda yake da injin bugo su agida "mlm dahiru har kasa magana yayi sun sha fura sunci zabbi da aka soya musu anan sukayi la'asar sannan sukayi shirin tafiya Aisha dai tana daki tamkar ta fasa ihu da Kyar tayi sallah ko abinci kinci tayi ta sanya dan guntun hijab hular kanta ya sauko mata iya kafadarta ,farin takalmi tasa sai farin handbag data makale a hannunta ,a haka mlm dahiru yakarayi mata nasiha ta fito dan hasken ranar da ya nufi gabas zai fadi tana fitowa shi ya hasketa tasa hannu ta Kare fuskarta ,Dr sagir ya kallota ya girgiza kai yayin da yadan zunguri Abdullah ga madam nan fa. Abdullah ya kalleta tsab yayi murmushin a hankali yace ai aganinta duk mun matsa mata ne fa,suka sa. dariya ,lafiyayyun motoci tamkar na wasu shugaban kasa aka bude mata daya ta shiga ta gane direban da ya kawosu ne,ashe Abdullah ne ya turo shi,mlm dahiru na tsaye har sai daya ga tafiyar su tare da tsaraba man shanu nono fura kwan zabbi musamman dayake lokacin sane.salis da yaya Ali sune a motar gaba sai musa dake tuka su a dayar mota kuma shida Aisha a baya yayin da Dr sagir a gaban gurin me zaman banza Dr sagir ke ta kokarin janta da hira wani ta amsa wani tai shiru shi kuma Abdullah inda ka ganshi tamkar wanda akayiwa gafara jin sa yake kmr ya aure ta ne sun fito yawon ziyara yasa hannushi ya dauko jakarta dake kan cinyarta tana kallonshi batai magana ba har ya bude bbu komai a ciki sai kayan make up dinta yayi murmushin ya Ciro wani passport dinta na makaranta da uniform a jikinta har da dan kwalin perfect akanta ya zubawa hoton idanunshi sannan ya dago ya kalleta itama anyi sa'a ta dago da niyyar ta saci kallonsa ai kuwa suka hada Ido ,Ido cikin Ido suke kallon juna ya kashe mata idanunshi daya yayi murmushin ya zura hoton a aljihunsa , Aisha ta dauke kanta tacigaba da kallon hanya shida saura suka shigo birnni kebbi taso ace sai dare suka shigo , Amman ko sanda suka sauka daga mota Ido CA akansu musamman ita da Abdullah daman Kuma abunda bata so kennan gashi biye yake da ita jakar ta ma tana hannushi nan da nan tarinkajin tamkar ta nutse dan kunya yanayin ta ya sauya jikinta har rawa yake hatta Dr sagir sai da ya lura da yanayin da tashiga har kofar gida suka rakata suka Yi sallama da Dr sagir , Abdullah ya Mika mata jakarta ta juya zata karba ya lura hatta idanunta sun cika da kwalla ya rike jakar yana kallonta ya kira sunanta cikin sanyi murya Aisha..... are you alright .....?ta daga masa kai are you sure tasake daga masa kai sannan a hankali ya Miko mata jakarta tare da fadin I will come back letter ,ta amsa ta juya ta shige gida ya tsaya yana binta da kallo bbu halin yabita ya rarrasheta ya karaso inda Dr sagir yake yana ganinsa ya fashe masa da dariya yace kai friend be a man duk kabi ka susuce akan karamar yarinya "tension ne kawai ta samu na rashin sabo na gane irinsu duk kabi kawani rude Abdullah yayi murmushin karfin hali dan shi kadai yasan halin da ya tsinci kansa lokacin da suke tare Dr sagir ya bugi kafadarsa yace my friend a dage da addu'a .dan yarinyar taci ayi komai a kanta Abdullah ya mika masa hannu suka tafa yace thank you doctor ...
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......