6

1.7K 84 0
                                    

3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 6

Tsaye take turus sai hawayen dake bin fuskarta bata san har yanzu yanan ba kawai sai taji badadi ko kadan ba nufinta tayi haka agaban shi ba ,bugu da Kari  Abdullah ya girmewa babnan yayanta yusif  dan sai taji tamkar tayi raini ga babba.

Cikin Yan mitina da suka wuce da faruwar haka ta tsinkayo maganar babanta subuhanallahi waye yayi barin kaya anan "ya turo kofar tare da Kiran sunanta Aisha ta fito daga kicin , babanta yaci gaba da tambayar ta ,karaf hadiza tace kayan wani ne Abdullah yace yaya Aisha taje wai dan taki zuwa shi kuma yaki tafiya ya tsaya a tsoro  an watsa masa kayan nasa yana gani ya tafi ya manta bai diba ba.cikin mamaki mlm abu yace waye ya watsa masa kayan?hadiza tace yaya Aisha mana "cikin murya mai nuna tsantsar bacin rai mlm abu ya dubi Aisha yace yayi kyau da abinda kikayi ina son da hannuki ki koma ki kwashe kayan da kika watsar .yashiga daki ,zuwa jimawa ya fito da abin sallah a hannusa bai sake ce mata komai ba ya fita ransa a bace "tabbas ta manta yau jama'a babanta yana dawowa Sha daya zuwa Shabiyu"ya sake fita saboda masallaci banda haka da tuni ta kwashe kayan kafin yazo,dan haka gabadaya a tsorace take ganin yadda ran baba yake a bace ,tun hadiza bata kai haka take son yarinyar  saboda surutunta yana bata dariya ,anan makotansu take,gashi yau surutun hadiza bai Yi mata rana b.tun bayan saukowa daga masallaci yake daki bai fito koina ba ,haka nan salis ma cewa yayi yaje  har sai ya nemeshi ,yasan Daddy ma bazai bukace shi a yanzu ba don haka ya kashe duka wayoyinsa hakan yabashi daman tariyo abinda da yafaru a dazu ,me sanya Aisha zata yiwa soyayyrshi mummunan fahimta ,shi da kansa ya amincewa kansa tun ranar da idanunshi suka fara ganinta har zuwa yau bai taba koda kallon dan yatsanta yaba sha'awa irin wacce ita Aisha ke nufi ba,sai dai ya kalla bashi Sha'awa irin ta birgewa wanda so ne kadai ke kawa haka Kuma koda ya aiyana wani abu da ita yakan kaddara wa sai sunyi aure , to Amman duk ya gane abunda take nufi da shi yana tattare da rashin son take masa"ya runtse idanunshi gam yanajin wani radadi na ratsa ilahirin jikinsa tare da fadin dole in hakura dake Aisha tunda da gaske kike bakya Dona,cigaba sonki zai sa in cutar da zuciyarki sannan ya bude idanunshi da suka gama rikedewa suka koma ja "Amman zan samu Dr sagir .wayar landline dake bedside dinshi ita ta katse daga duniyar tunani yana dagawa muryar teema ce ke cewa bros mami tace ko kana nan ,an Yi checking dinka a handset baa sameka ba . yace na dan kwanta ne tana son ganina ne yanzu?teema ta amsa  da Eh yace OK am coming duk da yanayin sanyin  garin    ,sanye yake cikin  karamar  riga baka da kadan hannuta ta sauko kafadarsa hakan nan takama jikinsa sai bakin wando jeans shigar ta kara fiddo masa da sigarsa ta cikakken "da" namiji  gashin kan nan sa ya kwanta luf kmr koda yaushe saboda gyaran dayake samu akai akai" cikin takun nan nasa mai birge duk wanda yakallesa Abdullah yashiga part din maminsa ,a falo ya sameta tare da kannesa sai bakuwar dayaga sunyi " yasamu waje ya zauna tare da daukar remot control yafara dadfanawa minal ce taajiye masa farfesun hanta da apply juice wanda mami da kanta tayi masa ,ta matso masa da stool gabansa ta zuba masa  sannan suka fita dama unguwa za'a kaisu mami ta kalleshi ta jiho masa tambaya halan wani abu ke damunka yadan kalli mami kadan yace noting na dai gaji ne , bakuwar ta matso ta gaisheshi ya amsa batare da ya kalli inda take ba"  mami tayi murmushi tace faiza kennan daga sokoto tun wajen daya ta sauka"Abdullah ya dan yadan  kalli faiza ta kasan idanunshi"Wanda ita tun shigowarsa ta kafa masa ido , ya tabe baki ya mai da kansa gafe shi sai yanzu ya gane kallon da take masa tun shigowarsa ,wato itace mami ke son ya aura diyar mama hafsa ,a kalla zata girmewa teema haka kawai yaji bai son yawan kallon datake binsa dashi yaji duk yatsani wajen cikin shagwaba wanda shi bai ma San yanayi ba  yace mami ina son inje in ga Dr sagir ,ya fada tare da duba agogon farin gold dake hannushi .namu tace to baka ci abinda aka kawo maka yadan can ciza lip's dinshi yace bazan iya ci ba   kuyi dinner da ni  aransa yace yaushe zan iya cin wani abu bayan akafe ni da mugun  kallo  mami tace mekaci ya lashi  basasun lebensa yace coffee tace coffee ba abinci bane ok mami indawo zanci yafadi haka tare da Mikewa yayin da faiza ta bishi da Ido tamkar kura taga nama ita duk yadda ta dauki Abdullah din sai taga yafi haka har yawuce da tunanin ta ,bata taba mafarkin zata samu irin sa ba ,yadda take ji ta a yanzu koda Abdullah bai da kowa da komai a duniya kyaunsa ya ishe ta haka daga ganin sa zai iya irin soyayyar datake mafarkin samu "mami ce ta katse ta tace karki damu yanayin sa haka idan yaga yana bukatar hutu .faiza tadanyi murmushin hade da sunkuyar da kai don ita har ta manta mami na zaune agun dan ta shagala da kallon danta .

Duk da abunda Aisha tayi masa ya bata masa rai matuka Amman sai tsinci kansa da kasa gayawa Dr sagir dukkan abinda tayi mada illa ya nuna maganganun da ta furta gareshi sune bai ji dadinsu ba Dr sagir ya numfasa yayi murmushin yace kasan mata fa koda suna sanka sai sun maka wannan borin  na farkon balle ita Aisha abun a tsaya aduba lamarinta Kuma su mata suna son arinka fada musu kalmar so  kai kuma sai dan banzar girman kan tsiya,ka kasa tsayawa ka sanarwa yarinyar karama damuwarka ,shi kace kana sonta shine aiki ok kabari ni zan rakaka inyaso sai sanar mata saboda ni nasan irin kamun data maka dan haka zance ka hakura duk bata taso ba "Abdullah ya aiko masa da harara shima ya rama , Dr sagir yayi dariya yace wallahi kayi mugun kamuwa Amman abunda nike so yanzu kadan bata  hutu zuwa wani lokaci.dan ni gobe early in the morning zan wuce sokoto da ni da kaina zanje gurinta muyi arba ,har yau bamu taba haduwa ba,sai dai idan na dawo a hankali  Abdullah yasauke hadiyar zuciya yace inga hakan zaifi kawai yana mai runtse idanunshi dan rashin ta tare dashi ba karamin illa bane" a kan haka suka Yi sallama .
Tara saura kwata na dare bayan yayi wanka ya nufi part din maminsa har yakusan shiga ko me ya tuna kawai ya juya ya koma part dinsa  yayi teema waya ta hado masa abincinsa takawo masa ta amsa da to mami dake kinshingide a falon tana dan gyangyadi ta wartseke tace ke sake kiransa kodai jikin ne naga dazu kmr wani abu na dakinsa mami ta karbi wayar take tambayar lafiya yake ,tunda yace akawo masa abincinsa,ya amsa da lafiya sa lau tace sam bata yarda ba sai da Abdullah ya rantse mata da lafiyarsa kalau sannan ta yarda .

Abangaren bakuwa faiza kuwa duk kwakwa da kulafucin son ta sake ganin Abdullah a wannan dare hakan bai samu ba dole ta hakura tabarwa safiya  .daga shi sai short niker sai white singlet  yake faman motsa jiki yana gamawa gudu gudu sauri sauri yaje  ya dawo sannan ya dinga daga karfen motsa jiki  yana ajiyewa daga karshe ya zube akasan gress carfet ya ajiye karfen yana hali (kabar muna gida kada ma wani yazo yazaci nima irinka ce ) maganar tace take ta masa yawo akai yasa kafa ya Ture weight lift sannan ya rigingina ya runtse yanasake tunanin maganganun ta gareshi  (kayi kuskuren idan kana tunanin zantaba sonka ) yasa hannushi duka ya dafe kansa .salis da sauri ya karaso  gareshi shi kadai ya dan fuskanci abinda yake tsakaninsa da Aisha tun ajiya da suka dawo daga gurinta ya Miko masa robar swan Abdullah ya Mike zaune ya karba ya guntsa a bakinsa ya fesar sannan ya daga kai yana Sha kawai jikinsa yabashi ana kallonsa byn salis dake gabansa "ya sake kallo a hankali "ya  juya faiza ya hango can barandar saman teema ta zuba masa idanuwana tamkar zasu fito cigaba yayi da shan ruwan ragowar ya tuttula a kansa sannan ya jefar da robar ya Mike salis ya Miko masa karamin towel ya karba yana goge ruwan dake kansa da yayi gaba zuwa part din sa salis nabin sa, dab da bakin kofar shiga ya tsaya yace salis kaje kasa a wanke min 4mat shadaya inason fita . salis ya amsa ya juya Abdullah kuwa yashige abunsa yayin faiza dake can sama tayi murmushi tare da sanya hannuwanta duka biyu ta rukunkume kanta gsky ta gama sa'a acikin mata muddin ta mallaki Abdullah .......

A takure take a gaban mlm abu ya Nisa tace tun tashi na arayuwata ban taba wulakanta kowa ba idan har nayi wulakancin daban kawo yanzu ba acikin rufin asirin Amman sai gashi a cikin gidan nan kin fito da naki salon wulakanta dan Adam in ko kika ce haka zaki Yi ,rayuwa baza ta miki kyau ba yaro me kima da mutunta mutane kina tunanin kina da wani abinda zaki iya wulakanta shi idan ma so ne ba kiyi masa baza ki Bari ku rabu lafiya ba,sai kin sako rashin daa a ciki.cikin bacin rai mlm abu ke magana , magana ta karshe duk randa yaron yasake dawowa baki bude baki kin basa hakuri ba ,ban yafe miki ba tunda duk cikin bbu wanda kika gado wajen wulakanta mutane

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now