ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 47-48
Dr sagir ya zuba masa ido watau har yanzu dai rikicin mami na nan kennan na rashin son auren Abdullah da Aisha.
a ganinsa zuwa yanzu ya dace ace mami ta barwa Allah komai .
ya jima, yana jinjina al'amarin sannan ya numfasa yace Abdullah a hanya nake yanzu.
bbu wani hanzari da zan iya Amman karaba kanka da wannan kadaicin .
,kada ka mutu a cikin daki kai kadai.Ganin yadda jikin Abdullah har yanzu rawa yake kmr mazari yasa Dr sagir yin hanzarin Mikewa ya ja hannunsa zuwa bedroom ya kwantar dashi kan gado sannan ya dubo wayoyinsa duka ya kunnansu da duk wata na'urar dake dakin.
sannan ya koma waje yayi kiran salis yace a shigo a gyra koina.
ya koma kusa da Abdullah wanda yake kwance yana numfashi ahankali, yace da sati guda zanyi a sokoto Amman ya zama dole na rage kwanakin su koma hudu zuwa biyar saboda yadda na sameka Amman dan Allah ka tashi yanzu kayi duk abinda kasaba Aisha...sai kuma yayi shr yakasa magana ya dan dafe kai shi yarasa ma wani abu zaiyi akan lamarin ,ya girgiza kai yana duban agogonsa yace dole ne in dawo da wuri saboda kai Amman zan neme ka dana isa.Abdullah ya dan daga masa kai a hankali.
Dr sagir ya fice saboda shi Sam baya son ma kallon yanayin da Abdullah ke ciki gashi Kuma abinda damuwar wai mami ce da alhakin haka .Ko minti goma Dr sagir bai yi da fita ba.
daya daga cikin wayar sa ta fara kuka ta danyi kmr sau biyar sannan yakai hannu ya dauka dayake kusa dashi Dr sagir ya zube su.
yana dubawa bakuwar number ya Gani ya kara a kunnesa Amman sai murya dady Abdullah yaji zuciyarsa ta sake tsinkewa tamkar ya fara mishi kuka,
dady yace Abdullah where ar you gobe nake shirin yin abinda ya kai ne Denmark, Amman duk na nemi wayoyinka ba same ka ba ,
Da duk wanda yakamata na nema na nema Amman ance ba'aganka ba meke faruwa da kai ne ?.Muryasa ta sake rauni sosai yace dady ina gida a daki ,da sauri dady ya Kuma tambaya meyasa Meka kai ne ko Aisha ba lfy .
Shr yayi dan wani abu dayaji a daidai makogaronsa yana shirin tokare mishi numfashi .
sai da dady ya sake magana sannan yace dady Aisha bata gidana mami ta tilasani sai na rabu da ita,
shiyasa nasaketa kuma da gaske mun rabu yau kwana biyar da rabuwarmu .
da sauri dady ya katse shi yace Abdullah be a man ka nutsu sosai zan bugo byn minti goma.
sai ka maida hankali kamin bayani yadda zan fahimta dady ya katse wayar .Yana nan zaune har minti goma suka cika dady yasake kira dady yace yanzu kana ina kana gidanku ko side dinka yace ina part dina yace mhn ina jinka .
Ahankali Abdullah yawa dady bayanin komai tun daga ranar ya tafi har zuwa yanzu da yake zaune .
dady ya numfasa yace to Abdullah shine kake neman ka susuta kanka saboda macce ? maganar ta dan shigi Abdullah har ya kara tada hankalinsa .
dady yace yes macce gishiri ce ta rayuwa ,.kuma dukan wani jin dadi na rayuwar duniya ya kan haduwa da macce ,Amman macce wani fanni takan zama hadari ga rayuwar wasu.har yakansa wasu su gwammace yin rayuwarsu su kadai batare da macce ba . Abdullah Allah yabaka maccen da kake so. kuma ka aura to idan ya karbi abunsa fa .
sai kace dan me ,.
ma'ana idan Allah ne ya karbi ran AISHA shi kennan baza ka sake amfanuwa ba kennan.Abdullah yayi shr dady ya sake maimaita tambayar Amman still Abdullah bai ce komai ba dady yace ka auna da kanka ka Gani zan sake bugowa byn awa daya .
Ahankali ya sauke wayar a sanyaye ya dan kalli agogo dake gefen gadon sannan ya mai da kasa ya zubawa Tay's din dakin ido yayi shr yana tunanin maganar dady.
shine kake neman susuta kanka akan macce ,barin da ya tuna ma yadda Aisha bata wani son sa.
kawai mikewa yayi ya shige bathroom ya kunna fonfo dake manne cikin sink sai daya cika sannan gabadaya ya tura kansa ciki yayi dan Jim sannan ya dago yana maida numfashi ahankali ya kurawa kansa ido ta cikin mirrow din gashin kansa daya jike duk ya kwanto goshinsa ruwa na dinga .
idan Allah yakarbi ran Aisha shikenan baza ka sake amfanuwa ba kennan maganar data sake zuwa masa kennan.
ya runtse idanunshi sosai yana sakin numfashi ahankali ya furta alhamdulilllahi tunda Allah yasa Aisha ba mutuwa tayi ba .
ya sakarwa kansa shawa yayi wanka Amman har alokaci yana jin kadaicinta ajikinsa , ya fito yana goge jikinsa ya ya koma yayi rigingine da jikin gado ya zubawa celling dakin Ido ,duk son da yake mata idan wanda ya hallice tane ya dauketa bai isa yace komai ba,.
ya rufe idanunshi gam ahaka har wayar dady ta sake shigowa ya Mike zaune yana amsa wayar dady yace ina sauraronka .
Ahankali Abdullah yace kayi hakuri.
dady yace kai za'a bawa hakuri dan kai aka batawa.
Abdullah yayi shr dady ya sausauta murya ya kirawo sunansa yace Abdullah ba tun yau ba nake nuna maka mahimmanci idan wani damuwa ya sameka ka daina sa shi a ranka .
ka dinga barwa Allah komai inda ba haka ba zaka sa kanka a wani hali.Abdullah tabbas nasan an bata maka tunda aka saka rabu da matarka an katse maka wani farinciki na rayuwa duniya.
ni nasan da haka to Amman karike aranka bbu wani dadi dayake samuwa batare da an Sha wuya ba.
kuma muddin kasan zaka samu wata rana dole zaka rasa .
Zuciyata ta amince maka da yarinyar nan Aisha.
dari bisa dari Kuma na amince ka zauna daita ko byn Raina , kuma ko ba komai wannan yarinyar diyata ce halak malak bazan so wani mugun abu yasame ku kai daita ba.
domin kuwa nasan adaidai wannan yanayin maimuna na can cikin bakin ciki da tashin hankali fiyye da wanda ka tsinci kanka ciki ..
dan haka Abdullah ina son ka daurewa zuciyarka na rashin matarka a kusa ka ajiye komai har sai na dawo.ko inda take kada ka dosa hakan zai iya sa zuciyarka sake karyewa ko wani ban yarda ka tura ba.
har sai na dawo da kaina zan same iyayenta dan yanzu duk wanda za'a tura zasu ga an dauki auren wasan yara .
Amman bbu komai nasan maminka ni tabatawa bakai ba .
Saboda haka ka sawa ranka hakuri matukar Aisha rabonka ce.
gaba zaku sake zama ,ka maida hankali kan abinda nabarka dashi a game da ma'aikatan Abdullah idan ba'ayi da gaske ba company yana iya durkushewa a dalilin wannan satar.
Abdullah mutane nan so suke suga karshenmu Abdullah gashi bananan nasan zaka mayye gurbina har yafi idan ina nan.
dan haka Abdullah idan baka ajiye al'amarin Aisha a gefe zuwa wani lokacin ba zamu kwana aciki fa.
Abdullah ya jinjina kai ahankali yace inshallahu zan ajiye komai zai daidaita.
dady yace Mashaallah zan sake nemanka .
Ita kanta mami taga canji a ranar hatta kannensa yau sun dan sake dashi salis kuwa tamkar sallah haka yaji jin Abdullah yace zasu fita .Amman daddare sai da Aisha tazo, ta hanashi bacci da tunanin halin da take ciki bbu yadda zaiyi da kaunarta ta zama naman jikinsa .
Wani tashin hankali da yazo masa nan da nan jikinsa ya dau rawa karfe biyu da mintina na dare ya lalubi wayarsa yasoma neman dady yaji duka wayoyin dady a kulle .
tunanin da fadomasa arai akalla dady zai yi wurin wata uku zuwa hudu kafin ya dawo , Kuma sai ya dawo zai je masa Biko AISHA .
to idan kafin lokacin suka aurar daita fa ?dan a wancan karon ma mlm abu cewa yayi zai aurar daita ga duk wanda yagadama.
Allah ya kiyaye to har dare ranar haka ya kwana yana surutai ba wanda yaisa ya aurar masa mata.
tashi ce shi kadai .Da safe wayar dady nashigowa korafin daya farayi masa kennan dady ya danyi shr yana jinjina al'amarin Abdullah game da yarinyar .
sannan yayi dan murmushin yace to Abdullah a ganina duk maccen da,aka aura aka saka sai tayi idda kafin ta sake yin wani auren.
ma'ana sai tayi jini uku kennan kaga a kalla zai dauketa wata uku zuwa hudu ina ganin itama Aisha ai haka ne malam Abdullah dole sai tayi idda kafin suyi mata aure dan haka a tunani sai tayi idda itama ko ba haka ba ne .
Abdullah yadan sotsa keya kmr dady tamkar dady yana kallonsa yace haka ne .
dady ya sake yin murmushi to kaga kuwa har na dawo ..
Abdullah yadan janye wayar yayi .
yana murmushi dan gabadaya yagama rudewa gashi har yasa dady ya fahimceshi ya fada aransa .
Shima bangaren dady dariya yayitawa Abdullah .MMN SUDAIS CE

YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romantikzuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......