13

1.3K 79 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
       💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page13

Tayi shr batace komai,tashiga wani yanayi na daban, tarasa  gane kanta  meke shinrin farawa da rayuwata ta furta haka acikin ranta  , Abdullah nasan ruguzamata zuciya  da wayan nan idanun nashi masu frigita ta  ZUCIYAR duk wanda aka kalla dasu, ta takasa amincewa da farinciki take ciki ko tashin hankali a lokacin guda km  taji kamar ta tambaye shi ko zai iya amsa mata tambayoyin da suke cunkushe akasan ranta masu neman tarwatsa mata zuciya da tsantsar jiki "da idanu take binsa da kallo tanason taganu ko shima yashiga  makamancin halin datake ciki " shima ita yake kallo ,yayi murmushin daman yasan bazata iya furta  Kalmar daya nema daga gunta ba "   , acikin zuciyarsa ya furta" OH" ni Abdullah tawa tasamini nashiga one chance , ya zuba mata manya idanunshi yace gobe zanyi tafiya  ta dago dara daran idannuta ta kalleshi yasake yin murmushi yace a kallonki nagane tambayar ki , Aisha ni bazan yarda da wannan shr naki  ba idan munyi aure kidinga kinmin magana ba gaskiya ya fada har da turo baki batasan sanda murmushin kufce mata ba  shima dariya yayi Amman nasan abinda zan dinga miki zaki dinga yimin magana sosai ,ni kadai nasan abun.
Tasake yin murmushi yana kallonta kaunata na sake huda masa zuciyarsa, yadan gyara murya cikin natsuwa yace Aisha zanje  interview a Denmark gobe zamu wuce Lagos ta can zamu tashi nan da kwana uku zan zauna interview Aisha kiyimin addu'a samun nasara  ,dady ya zabi da inje in zauna masa ,har inajin tsoro Kar inyi disappointing dinsa ya fada yana kallon kwayar idanunta yanason tace wani abu ta fahimce abinda shr nasa yake nufi ta dan girgiza kai  sannan ahankali tace zakayi nasara ya dan kalleta yace meyasa kika ce haka tace nasan zakayi nasara in Allah yaso "ya lumshe idanunshi yana mai jin tsanyi na ratsa kowani sashi na gangar jikinsa  ko ba komai yau tazo masa da abubuwa masu mahimmanci daga gareta     yace to Allah yasa Aisha bbu igiyar aurena akanki Amman ina da matukar kishi most especially akanki sati biyu  kawai zanyi Aisha dan Allah kada kibari wani yashiga tsakaninmu Kar ki Amince da duk wani abu da zai bata tsakanimu a yanzu haka nasan ni ba wani zaunanne ne a ranki ba Amman ina sa ran idan muyi aure zaki soni , Aisha inajin tamkar in tafi dake idan muje can a daura mana aure Aisha  ina son Allah yabani ikon Yi miki abunda zaisa ki so ni idan muyi aure .
Yadda yake maganar ya dada sa kirjinta yacigaba da bugawa..
. wuraren daban daban  na halittar jikinta ke bude suna karfan sakoninsa" a zuciyarta tanason ta furta masa koda kalma daya ce mai mahimmanci da zai tafi dashi Amman hakan ya gagareta sai binshi take da shanyayun idanunta yayinda take sake kashewa Abdullah jiki , Abdullah ya dubi agogon hannushi karfe goma ta shige yace wai Kar aunty tayi fushi dani pas ten Aisha ta Mike cikin sanyi jiki uhmm har sauri kike ki tafi kibarni  ko, ta sunkuyar da kai shima ya Mike yace akwai zanen company da guest house  da zanyi acan  shine Nike ganin zai tsayar dani har tsawon sati biyu  ban da haka da next week zan juyo "tsaitin datake tsaye   nan ya tsaya suna kallon juya ,ya suke hannuwanshi duka acikin aljihun wandonsa kara step uku yayi zuwa inda take har suna jin bugun zuciyoyinsu  ya xuba mata idanunshi shidai yana son ta har bai san yadda zai misalta ba ,ita din wata sashi ce ta zuciyarsa yasake tsareta da Ido yace Aisha me zaki bani zan tafi ?
Tayi shr takasa cewa komai ,yace to ke me kike so daga gareni ?ta girgiza kai yayi murmushin yace gobe salis zai kawo sako har da Nasu yaya yusif dukansu ,ta kalleshi tana tunanin shi baya gajiya da kyauta ne ,ta tuna kyautar kudin da yayi mata ba a kai sati guda ba har tsoro suka bata da sauri ta rufe ledar ta wurga su bayan akwatin kayanta har zuwa yau bata kuma bi ta kansu ba. hakan nan bbu wanda yasan dasu yanayinta ya kalla ya gane tana son Yi masa godiya ne kawai ya share ta yacigaba yasake duba agogo yace let me go Aisha please say something for me wanda zai yimin rakiyya da ragemin yawan kewarki da zanyi har tsawon sati biyu  ya zuba mata idanunshi yace I'm gona miss you Aisha please ya maimaita kusan sau uku kicemin wani abu mana ..... still tana tsaye kmr an sassakata ,yaga alamun bata da niyar yin magana yace ba zaki gaya min komai ba ko haka kike son na tafi ya furta hakan yana mai langwabar da kai to muje har gaban aunty nace ta roke ki kigayamin abinda zai dinga tayani bacci , ahankali yake matso ta tana ja da baya har ta mannu da bangon dakin   yayin da zuciyarta ke dokawa tana  harbawa  gabadaya jikinta yagama mutuwa murus kafafuwa sungaza tsayuwa akaran kansu  da Kyar ta iya tattaro dukan wani kuzarin dake jikinta  ta furta I will Miss you too........ Hade da lumshe idanunta tana jin wani tsanyi na ratsa sansar jikinta yasake motsata sosai ya tsaya kawai yana kallon bakinta da yadda ya hudu ya furta Kalmar sai yaji kmr ya daura bakinsa akan nata mai abin sha'awa ya zuba bakin Ido yana mai cizan lip's dinshi gefenshi ta bi zata wuce dan baza iya jurewa kallon dayake binta da shi ba,ya kamo tafin hannunta cikin nasa ya matsesu gam   wani shock suka alokaci guda  yana musu yawo ajikinsu  sakamakon haduwar da tafin hannyensu ,kokarin cire hannunta takeyi daga  nasa  batare da sun kalli juna ba  sausauta rikon ta yayi ta zame hannunta ta saya dai dai bakin kofar ciki tana kallonsa yadda yake kallonta ne yasa tarinka jin wani abu atare da ita nan da nan ta juya ta shige dan bata son irin abun da tafara ji a game dashi din bata San iya lokacin da ya bata kafin yatafi ba, .

Tafiyar Abdullah da kwana shida maminsa tadawo Nigeria to abinda ta tarar ya maseefar gigitata domin dady yagama zartar da komai na batun auran Abdullah abin ya daure mata kai tana can dady na nan yana shirin yiwa Abdullah aure batare da itama an tuntubeta ba "tsawon kwanankin dayawa da dady ke nuna mata me za'ajira tunda Abdullah din yadamu da yarinyar kuma ta kowani bangaren yarinyar tayi illa daya gareta  shine su din bawa wasu bane "ya nuna mata wannan ba wani abu bane tunda  Abdullah yana son yarinyar bbu abunda zai gagara"mami  tace Amman auren farko daza'atabayi a gidan nan yadace ace Yar manyan mutane zai aura koma ba haka ba a samu wacce akasan halinta ciki da waje ba irin wannan ba dan ni halin danaji daga bakin mutane batamin amatsayin matar da Abdullah zai aura.

Dady yayi murmushin to ke bakisan mutum da shi da kansa bai san yadda halinsa yake ba sai mutane sun fada ,to duk yadda dady ya bullo mata sai tace ba haka ba ,akarshe yace shi kam yariga ya gama  magana ,in Allah yaso Abdullah bashi da wata mata sai zabin ransa sai kuma idan bangaren yarinyar ne suka ki.
Ran mami in yayi dubu to ya baci kwata-kwata a wannan taki jinin yadda dady yake mata musamman akan Abdullah Dr sagir ta fara sa aka nemo mata ta tunhumeshi akan maganar yarinyar da Abdullah yake nema iya abunda yasani shi ya fada mata to shi din yana da sauran kima a idon mami "Amman salis kuwa fata fata tayi masa ta kuma rantse akan idan har ta kamashi yana da hannu a hadin Abdullah da yarinyar nan to ya kawo karshen aikinsa . domin wannan karon bada salis Abdullah yayi tafiyar ba tare da security din dady sukayi RK da Immanuel shima (SS)ne na dady hatta part din Abdullah mami da kanta taje bbu wani abu data samu na game da yarinyar .

Mami na cikin wannan tashin hankali mama hafsa ta dira a kebbi tazo yiwa mata gaisuwa ta tarar da wannan mummunar labarin kusan ma hankali mama hafsa har yafi na mami kololuwar tashi, ita mama hafsa a yadda  suke ji  ayanzu ita da faiza da su rasa Abdullah  gwara su rasa mahaifin faiza .to duk dai yadda mami ta kai ga bincikenta akan Aisha bata samu komai ba mama hafsa ce ta fara kawo shawara suje inda iyayen Aisha suke su samesu , haka kuwa akayi da yamma ranar lahadi mami tasa musa ya tuka su dan tasan duk munafukanta ne" sun san inda Abdullah ke neman aure har gidan mlm abu tun daga inda suka sauka suka Tako lungun gidan komai yafara tsinkewa mami kmr ta zubda kwalla haka takeji , tama yaya Abdullah me kamkyame yake iya shigowa wannan kazamin  lungunan   .

Aisha na tsakar gida tagama daka kayan Miya tana gyara zogale da zata musu Miya kmr wadda akace ta tashi  kawai tashiga dakinta ita kanta ta rasa me ta shigo dauka ta jiyo sallama daga kan da zatayi ta window tagar tayi arba dasu mami Amman su basu ganta ba  ,idan aka cire shekaru za'aiya cewa Abdullah na biyu ne yazo gidansu Amman sai dai wannan macce sabanin shi" Aisha ta fadi haka aranta tunda take a rayuwa bata taba ganin halitta da sukai kama sak ba irin Abdullah da wannan bawair Allah da batasan kowace ce ba,tabbas Abdullah balarabe ne akamaninsa da yanayin shigarsa zaka gane haka ko bai sanar ba, murya mama hafsa ce ta doki kunneta tana cewa A'a mu ba zama muka zo Yi ba ...........

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now