ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 3
Ko wansa da suke ciki daya idan ya tsaya akan abu sai dai ya kyale shi, ma'ana kaifi daya ne idan zaiyi zaiyi ,idan ba zaiyi ba ba zaiyi ba ,Kuma ko kadan baya yarda hakan yasashi shiga hakin wani wannan kennan.
Duk da wannan lokacin mlm abu yayi girbin amfani Gona dan haka ya raba har gidan alhj aminu Yan magana dai sunce naji dadi shine gari, a bangaren alhj aminu shima yaji dadin abinda yayi masa ,a lokacin har ya nema sanin inda Mlm abu yake da zama , Mlm abu yayi masa bayanin sai dai ya nuna masa a halin da suke ciki yanzu na shirin tashi suke alhj aminu yace muddin ya samu daki a garin nan zaizo yasanar dashi in km bai samu ba zaso koma garinsu ne ,alhj aminu ya tambaye shi tsawon shekarunsa a garin da km lokacin da aka basu notice duka mlm abu yayi masa bayani komai alhj aminu ya Nisa yace yanzu dai zaiyi tafiya gobe ,km in Allah yaso nest week zai dawo dan haka yazo nan da kwana takwas ko Tara yazo yasamesa yace yadan jinkirta tashi har ya dawo, haka suka rabu ,A aminu yace a gaida masa da Aisha.
Ranar alhamis ta kama kwanansu Tara da yin magana ,jiya laraba kennan A.aminu ya dawo daga tafiya da yayi zaune a sitting room din A aminu tare da mlm abu byn gaishe gaishe A aminu ke tambayar sa dama can shi baya wata Sana'a ne mlm abu ya sanar da shi irin sana'ar daya tabayi da wacce yakeyi yanzu ,alhj aminu yace ai yanzu ina gani komawa gida ba naka bane hakan yawon biye biye gidan haya ba mai yuwa bane ,ina ganin abinda yafi ka tsaya ka nemi naka na kanka ka siya ka zauna da iyalinka .
Mlm abu ya zaro idanu zaiyi magana A Aminu ya katse shi ,ta hanyar daga masa hannu ,yace akwai wani dillali dake kawo min filaye ina siya byn Yan watanni kadan sai na siyar ,haka nan ya kawomin gidaje kanana har sau biyu na siya daga baya siyar dasu ,to nayi magana dashi tun a Daren da zanyi tafiya nasa ayi cigiyar gida karami a wancan zuwa da kayi kasanar dani kana da Gona a garin ku , dan haka zaka koma ka tsaida wancan Gona.
Mlm abu yasake zuba masa ido , A aminu ya cigaba "haka nan a labarin daka bani yanzu ba aikin da baza ka iya ba,.
ka iya tuki da sauri mlm abu yakada kai to ALHAMDULILLAH dan haka zanyi kokari naga nasamarmaka tuki a wani kamfani ka fara ,ba zasu biya ka ba har sai kayi wata biyu su hada su gabadaya ,to da wannan albashin naka da kudin wancan Gona ina ganin zasu isa ka nemi gida karami naka na kanka .
Mlm abu ya hadaye yawu da Kyar ga bikin zuwa .... A aminu yace kafin wannan yana da kyau kafarayin shawara tare da tunani akan hakan mlm abu yadan sake gyara zama sosai yace alhj ni banida kowa a garin nan sai matata da ya'yana sai kum abokin arziki irin ku ,don haka wannan shawara daka kawomin ma tayi min sosai na km gode kwarai da gaske ,sai dai km ita wannan Gona bani kadai ke da ita ba gadarta mukayi nida kanwata , haka nan a jikinta muke dan samun abinci na wani lokacin , wannan shine matsala , maganar komawa gida dama nidin ma sai takama dole don banason komawa alhj aminu yace wannan gaskiya ne sannan yace abunda zaayi mlm abu ....yasakeyin shiru can ya Nisa yace abunda zaayi kasake bani kwana biyu zuwa uku zan sake ganinka.
Mlm abu yayi godiya tare dayin musabaha alhj aminu yace muje na sauke ka a gidan.a hanya suna ta hira yanayin rayuwa ta titi da su mlm abu ke kafa tebur suka wuce har ya nuna masa inda yake zama alhj aminu ya sauke shi kofar gida da yake yammace ,a dai dai lokacin sai ga yusif da Umar Maryam na rike da hannun Ali antaso daga makaranta Allo dukkan su da allunansu a hannu da gudu sukayo wanjen mlm abu, yayin da Ali ya tsaya baya yaki tawowa wai don sun rigashi zuwa mlm abu yana dariya ya karasa ya dauko shi ya cika ZUCIYA ,alhj aminu ya rike hannu yusif da Umar yana tambayar su sunansu mlm abu ya karaso ya ajiye Ali yana lallabashi alhj aminu ya kama hannusa yace taho nan abokina ka rabu da su anan yake tambayar yaran ajinsu nawa a makarantar boko yusif yayi caraf yace ai bama zuwa alhj aminu yace subuhanallahi ya akai kuna cikin birni ba kwa karatu boko ,ya dubi mlm abu.
![](https://img.wattpad.com/cover/205938711-288-k658577.jpg)
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......