52

1.8K 76 0
                                    

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 68-69

Abdullah ya waiwayo byn ya rufe kofar bai tsaya wata wata ba ya kamo hannuta har ciki bedroom dinsa tana binsa a tsorace "suna shiga ya janyota jikinsa  ya matseta a kirjinsa  har tasa kara "yaki sakinta ahankali ya tura hannusa kasanta yana shafo cikinta sai alokaci ya dan ji tudunsa .
  tun dazu dasu ke gidan Dr sagir yake ta kallonta Amman  bai ga cikin ba hakan ne yasa tasa iya karfin ta" ta fizge jikinta daga gareshi.
ta watsa masa harara  sai kuma ta fara kuka ,yayi murmushi ya jata ya zaunar daita a gefen gadon.
yace ina meyye haka   hade da shafo saman kirjinta da sauri ta buge masa hannu tana turo masa dan karamin bakinta ta turo masa bazato taji bakinsa kan lip's dinta ya hade   yasoma tsatsa kmr zai cire mata lip's ,sai da ya tsosa san ranshi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya"ahankali yake tafiya da baya da baya har yabar dakin  .

Yana fita tacigaba da dan kukanta wanda dagani duk na shagwabar ne . tana kallon dakin ahankali har idanunta ya sauka kan  hoton data Gani a gefen gadon yasa ta dan fara gane kan abun .
hotonta ne wanda batama san ko wani iri bane " Amman dai ta san tabbas itace .

Abdullah ne yashigo da snacks a plate " ya koma  ya kwaso kayan tea da flask , sannan ya duba store din shi .
ya ballo swan water da sauran lemuka guda uku saboda yaji Dr sagir yace ba'a son masu ciki  su dinga shan tsanyi.
shiyasa bai debo a fridge ba ,ya kwaso yazo gabanta ya zube yana kokarin hada mata tea ta kalleshi tace Abdullah ina ne nan ka kawo ni?.
  Yadda ta fadi maganar a natse" cikin mamaki yasa ya bar abinda yake ya kalleta.
sai kuma yayi murmushi yace gidanmu na kawo nan part dina ne ni dake ta zaro ido tana girgiza masa kai tace dan Allah kayi hakuri ka maidani gidanmu ni tsoro nake ji ta sake barkewa da wani sabon kukan "yayi murmushi
      Yace me akayi kuma kike kuka nan fa gidanmu ne , mu kadai ne fa a gidan sai ma'aikata su mami basa nan sun tafi abuja bikin wasu neighbors dinmu shima dady dazu ya tafi daurin aure .
ta karkace kai tana kallonsa idanunta cike da Hawaye ya sake yin murmushi ya tura mata tea daya gama hada mata .
yace Aisha kici abinci Dr yace muna zuwa a nemam miki abinci kici tayi shr tana binsa da Idanu.
yadda tayi shr yaji har cikin ransa tayi mugun bashi  tausayi .
ya mike ahankali yana murmushi yace ki sha tea bari nayi wanka rabona da wanka tun awanni tara  har nasoma jin ba dadi ajikina.
bata kalleshi ba ballanantana ta amsa wanda shima yasan basamu zaiyi ba  murmushi kawai yayi ya shige bathroom .
   Tayi shr " wannan wacce irin rayuwa ce sukeyi ita da Abdullah kmr za'a yi kmr baza ayi ba "bata so bata so Abdullah ya sake dawo  mata yasa ta a damuwa ta koina ta duba Abdullah ya wuce yadda take zato Abdullah na rayuwa anan Amman yake  damuwa daita "da ta fito daga wannan lungun .

Bataso  a kuma yin irin ta jiya gara duk yadda za'a yi ta lallabashi   ya maida ita gidansu , idan  ya maida ita  kuwa da ikon Allah ta bar hannushi kennan sai dai ya nemi wata Aishar "duk ta gama tsara  yadda zatayi idan  ya maidata a ranta .
dan ita a yanzun duk da yace iyayensa basa gidan Amman ita gabadaya a tsorocr take dan alal hakikanin gaskiya tana mugun tsoron mahaifinsa kmr me .
gashi yau zata kwana a cikin gidan da take .
Bai dade ba ya fito kugunsa   daure da white  towel   gashin  kirjinsa na   kwance suke luf luf luf dasu  ga dan karami towel a hannunsa yana goge kansa zuwa tsantsar  jikinsa .
Kallo daya tayi, masa ta dauke kanta daga gareshi dan bazata jure kallonsa haka .
"yazo  har kusa daita yace "oh" my God this girl won kill me oooo Aisha har yanzu baki ci komai ba  ya kalli agogo shadaya saura  yace kalla Aisha a kalla kin yi awa takwas baki sawa cikin komai ba.
kina jin kuma abinda Dr ya fada .
Tayi banza dashi sai idanunta data zuba masa yayi dan murmushi iya bakinsa sannan ya zauna gefen gadon kusa daita ya ruko tafin hannuta yace please Aisha kiyi hakuri da komai kici abinci nan karki min haka kinji ta watsa masa harara hade da zame hannunta daga nasa .
tace ni na koshi ya dubeta dakyau yace Aisha yaro cikinki bashi da laifin komai ki tausaya wa bbyn mu dan Allah.
    ni nayi miki laifi " to yaya zaki hukunta wanda bai san komai ba " idan kinci shima sai ya samu.
Suna nan  zaune a haka har shabiyu ta kusa Amman bata da niyar cin komai.
Ran  Abdullah yasoma baci  yaji wani abu ya tsaya masa a wuya yana kallonta yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya" tabbas  Aisha bata  sonshi  tunda gashi bata son dansa.
ganinsa muddin bata ci abincin nan ba .
wani abu zai iya faruwa da yaron cikinta .
  to abu ne idan akace maka na fari ne anfi rudewa akansa .
sai ya dinga ganin dan bata damu da shi bane shiyasa  take son yarasa cikin ,.
shi kuma  a halin yanzu ganinsa yake ba wata kadara da ya mallaka da ta   kai cikin jikin Aisha
  Ya dan kalleta  a nutse take kuma fuskarsa ta canza .
ahankali yake magana Aisha na rokeki kada kiyayyata ta shafi dana shi bbu ruwansa bashi ya miki laifi ba.
In kin tashi yin  hukunci ni nan zaki hukunta ya nuna kansa da yatsansa yana sake daure fuska.
  maganar tazo mata a bazata kuma  wani irin da sauri ta dago kanta ta kalleshi shima ita yake kallo  sun dan jima suna kallon juna da kyar tasamu ta iya  janye idanunta  ta sunkuyar da kanta.
batayi magana ba still ahankali Abdullah ya zamo daga kan gado ya zube kasa gabanta .
tana dagowa afrigice ta gashi a durkushe da kofin tea a hannunsa yana miko mata .
taji kmr an zuba mata wani abu ne a jikinta ne. ita wacce da kmr Abdullah zai durkusa mata da sauri tasa hannu ta karbi kofin hannusa ta kai bakinta .
ta fara sha a lokacin guda kwalla ta cika mata idanu.
ya mike ya zauna yana  miko mata snacks tana karba cikin sanyi jiki  har yayi mamakin abinda taci" bbu wanda yayi magana acikinsu har ta gama ya kwashe kayan ya fita falo.
ya zauna kan kujera yayi shiru  yana jin dacin abinda Aisha tamasa  ya jima a gurin" sannan yaji abinda ke wuyansa ya wuce.
Yarasa me zai mata aduniya in akwai abinda yafi  so da muradin kasancewa tare itace .
  iya kokarinsa yana yi "akanta ya runtse idanunshi  ya dade   Zaune a falo bai shigo bedroom din ba .

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now