ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A BAGUDO
Page 20
Sannan kuma naji kace kana bukatar auren cikin sauri nan kusa nidai ina ganin idan har ba wata matsalar a dan dagamin kafa zuwa nan da sati hudu nan gaba.
Dady ya sake Yi musu bayani dalla dalla akan yadda likitan Abdullah yace alhaji aminu ya numfasa yace a satin nan kennan a yadda kuke so dady ya girgiza kai Amman yake dan nakalci wani abu kadan game dasu "wanda da kamar ya manta Amman nan da nan yayi saurin cewa basa bukatar komai game da kayan daki yarinyar kawai suke bukata" mlm abu yace matsalar dai kennan tun farko ta hargitsa abu idan har ya kasance kowa yayi hakuri abin yawuce to a gaskiya ni dai sadaki kadai da yazama dole shi kadai nike bukata daga yaro ya fada yana duban mlm dahiru.... sannan batun daurin aure abarshi nan da sati biyu alhaji Mansur abokin dady kusan duk wata dawainiyar nan da shi akayi ,wanda tun zuwansa sau biyu kawai yayi magana sai yanzu ya shiga juya kai yace yaya za'ace za'ayi haka mu da aka taimakawa aka bawa yaron mu ai mu yakamata muyu komai .Mlm abu yace sadaki ma dan shine aure in ba haka bbu abunda zan amsa a auren AISHA dady kuwa shiru yayi mutane nan sukara cika masa Ido irin mutane da suka zabi su tsira da mutuncinsu ne ba su tsira da dukiya ba ,a fili yace to haka ma mun gode kwarai Amman maganar gurin da za"ayi taron daurin auren fa?
Daman shi alhj aminu tun ba yau ba yake da burin matukar Aisha bata zo gidansa amatsayin surika ba to shine madaurin aurenta domin Allah ne yahada su da mlm abu Amman silar haihuwar ta hakan kuma ya taba gayawa mlm abu ,sai dai maganar hadata da yasir yabarwa ransa "dan haka yayi saurin cewa ai in Allah ya kai muna numfashi nike da waliccin yarinya dan haka a can gidana za'a daura aurenta ..Dady yayi dan tunani sannan ya girgiza kai bbu komai mu dai muna sake godiya a yadda aka tsayar da maganar daga ranar jumma'a kennan za'a yi daurin auren ...cikin Raha sosai wanda dady yakara kima a idanunsu har mlm abu ya yarda da maganar matarsa ,tabbas alhj ishaq mutumin kirkine sai dai kawai bai Yi sa'ar macen kwarai ba" to mlm dahiru dai yayi shiru yana nazarin mlm abu ganin bashi da niyyar sanar da dady kusancin sa da mai dakinsa shiyasa ya gyara zamansa hade da gyaran murya yace yana fuskanci dady da kyau yace sannan kuma akwai magana mai mahimmanci dana zan sanar "gabadaya falon ya dauki shiru suka maida hankali su gunsa inban mlm abu da yasan me mlm dahiru yake son fadi dan shi gabadaya yama manta da wani zance can " nan dai mlm dahiru yasanarwa dady da komai har zuwa inda yace masa maimuna dai kanwar itace matar mlm abu ya nuna mlm abu da yatsansa kuma uwa ga yarinyar da Abdullah naka yake so "nan take jikin dady ya dauki rawa banda zufa bbu abunda ke tsatsafowa masa gabadaya jiyayi kmr ba haka yaji mlm dahiru ya ce ba "yasake duban inda mlm dahiru ke zaune da kyau "yace in kana mamaki ne ko tantama tashi mushiga ciki kaganewa idanunka ...jiki a tsanyaye dady ya Mike tsaye yana jin yadda zufa ke sake karyo masa , jikinsa yayi sanyi matuka bai taba kawowa ransa hakan ba duk da yaga da mlm dahiru acikin lamarin" ya dai dauki hakan da wani dangantarka ce tadaban ta hadasu da mlm abu, a tsaye yake kawai Amman gabadaya yazamo mutun mutumi yayin da mlm abu yayi gaba sannan mlm dahiru sai dady dake biye da bayan su sannan sauran har suka shiga cikin gidan bai san ta yadda kafafunsa suka iso ciki ba ,da idanuwa yake bin koina da kallo yana karewa gidan kallo tsaf yana alwadai da kansa da masu hali irin nashi yanzu acikkn wannan dan a kurkin yar'uwarsa take rayuwa mlm abu ya leka dakinta yakirawo sanye take cikin hijab kmr tasan zasu shigo tafito cikin tsanyi jiki dan kusan ma ita Aisha ta dauko wajen tsanyi ,ta gaishe su, shi ko dady kasa dauke kansa yayi daga gareta ya dai amsa mata gaisuwarta, maganar mlm dahiru ce ta tabbata tabbas itace dai a gabansa , yanzu yasan yayi babban kuskure a rayuwarsa kuma yasan ya aikata laifi Mafi girma". da kyar dady ya iya bude baki yakira sunanta mai..mu..na !ta amsa da na'am yaya ya bayan rabuwarmu ya girgiza kai kawai yana nasawa aransa yanzu baizo neman Yar uwarsa dan Allah ba gashi Abdullah ya kawo shi zama yayi akan shifidar da akayi masu mlm dahiru yayi magana yace kaganni ko abunda rashin zumunci ka yajawo bakasan mutane ishaq bansan meyasa ba itama data rage maka a duniya ka watsar da ita balle akai garemu shi zumunci nan fa dakake ganinsa inbayi shi a duniya za'a yi shi a lahira kuma a cikin wuta, ban kada kai bbu abinda dady yake saboda yasan bai kyauta ba, inna ta tashi takawo musu ruwa ta durkusa har kasa ta Mika wa yayanta byn taajiye sauran a babban jug tanajin wasai yau ga wani tarin farinciki mara misaltuwa da ta tsinci kanta ciki , ranta fas yau gata ga danuwanta har inda take ita ko mai zata cewa haduwar Aisha da Abdullah sai hamdala , yasa hunnu ya amsa duk da ba wai yana bukata hakan bane yasha ya ajiye kofin yana kallonta hira ce Sosai ta barke a tsakanin su a inda basu bar gidan ba har sai da yasake bawa inna hakuri akan abubuwan da suka fara sosai taji dadi hakan sannan akakira masa duk yaran suka gaisa Amman banda Aisha....
AISHA kuwa tun akwana biyun da ta fahimci haka , kayanta ta diba guda biyu ta sanarwa inna ta wuce gidan aunty Maryam ganin da aunty Maryam tayi mata har da kayanta batare da kuma ta aika tazo ba ya dan bata mamKi ,Amman dake tasan halinta sai ta rabu da ita ..
Kwananan ta hudu usman yazo yace wai ta dawo inji baba tare suka dunguma har aunty Maryam...Duk abinda ake tanajin inna da aunty Maryam suna hirarsu,a Amman takanji aunty Maryam na fadin sunanta Amman bata fahimci me ake ba balle ta saurara sai a daren mlm abu yake mata bayanin har da dangantakar su da Abdullah .....
Shiru dare ya tsula Amman idanunta ko alamun barci bbu ita duk tsoro ne ma ya cika mata zuciya wai yau sauran kwana goma cif a daura mata aure da wanda iyayensa suka zo har gidansu duka ci mutunci su, ta rufe idanunta sosai to Amman yata iya auran Abdullah yazame mata dole tunda innarta ta furta, ita kam bata San yadda zatayi dasu mami ba a rayuwar '"ta sauke naunauyen hadiyar zuciya,t a furta Abdullah kuma yayi hatsari kuma har yanzu bashida lfy take taji wata gajiyar atare da ita , jikinta yayi sanyi ta sake runtse idanunta tace "Allah ... Allah ka bashi lfy ta fadi hakan batare da tasan sanda bakinta ya fada ba..
Ita da aunty Maryam sukaje zariyar Kala kala kwanan su biyu suna zaga dangi daga baya inna tazo suka wuce ka'oje, Aunty Maryam kuwa tadawo gida ,Aisha dai Ido ne kawai nata sai yadda akayi da ita tamkar wadda aka Tarawa gajiyar duniya komai cikin sanyi jiki takeyi sa ..
Mlm dahiru yayi mata nasiha sosai duk wani abu na tsarin jiki har ma da kyautatuwar jiki anyi mata ita dai sai kallo bbu kuma zance gardama ..
Alhj aminu ya kara zama cikakken uba domin tun zuwansa indiya wajen yasir ya gano wasu gado da yayiwa sakina sha'awarsu, ya koma ya siyo sai gashi ai she Aisha ce zatayi amfani dashi shima mlm abu sai gashi bbu wanda yasan tun yaushe yake ajiyarsa ya nuna bajintarsa ta uba dan yabawa kowa mamaki domin dai dama shi ya dade da rikewa a ransa cewa mai kwarmin Ido da wuri yake fara hawaye ..aunty amarya ma matar alhj aminu da ita ake komai ,yakasance gidajen biyu duk acikin zirga zirga suke wanda mlm abu ya tabbatar wa ransa samun irin su alhj aminu a yanzu sai an tona ...Duk wani abu da shafi kayan kicin aunty Maryam ce tayi shi yadda yakamata musamman dayake tana da kawaye gogaggun tana jin Aisha tamkar yar'uwarta da Duke ciki daya wanda tafi so ..
Byn dawowar su da kwana biyu aunt Maryam da kanta taxo ta dauketa ta tafi da ita gidan ta domin akwai masu gyaran jikin data gayato kuma tasan takan komai dan haka koina sai da aka gyara Aisha tas,...
AISHA har kuka tayi dan abunda wata kawar aunty Maryam ke kawo mata ta titseye Aisha tasha shi ke bata haushi ..sakina tazo har sau biyu bata tarar daita ba lokacin tana ka'oje ,shi yasa yau tana zaune tana tunanin ta jin ana cewa yau sauran kwana biyar daurin aurenta Amman ita ko kawarta bata gani ba balle taran ko tasani ma ..aunty ce ta leko tana sanar mata ana neman awaje wai abokin Abdullah ne gabanta ya fadi, rabon da taga Abdullah ko wani abu daya danganceshi an kusa wata biyu kennan zuciyarta ta dinga bata shi din ne ma ,tsoro ya cikata har sai da aunty ta sake shigowa tana Yi mata magana ta kalli aunty idonta cike taf da hawaye ni kawai aunty su barni tunda dai auren zaayi su kyaleni in akayi yaganni ni ba zanje ba ... aunty ta hau salati tace ke dai har yau zuciyarki bata saduda ba ki bawar Allah ikonsa kinki,cikin murya kuka tace ni kawai Abdullah din ne banason ya ganni ..
Aunty tasaki Ido da baki tana kallonta kice auren Yan iska za'ayi kennan ai akace miki abokinsa ne ko ....Da kyar da hayya alal Sala ta lallabata ta fita tana wallahi yanzu zan dawo ,aunty tace ke kika sani .irin kune da anyi auren kuma sai ajiku shr ...Dr sagir har dan fara kosawa da Jira yana duba agogon sa sai gata ta fito sanye take cikin doguwar Riga har kasa sai guntun hijab iya kafada tayi kyau Sosai shigar ta karfrta matuka tamkar ita ma diyar mamin Abdullah ce ,haka kuma tun fitowarta jikinta yake ta rawa kai tsaye ta iso gurin Dr sagir dun gaisa yake mata bayanin yaje gun sakina bai same ta ba da man kuma akwai ragowar abubuwan da zai kai mata wanda ita sakina ta rubuta suna bukata shine yazo nan ko kuna tare a hankali take masa bayanin sakina bata zo ba Dr sagir ya zuba mata Ido yadda take magana da kyar kmr mai shirin yin kuka ya gane dole ta rikitawa Abdullah brain yarinya ce Sosai" natsuwa ce kawai Allah yabata sai ka mata kallon kmr tafi shekaru ta lallai Abdullah yashiga one chance yana da sauran aiki ....Dr sagir ya kalleta ya girgiza kai yace shikenan ya Miko bundles na kudi yace da akwai kaya a bayan mota idan kinshiga ki aiko a kwashe ...
Sannan ya tambayi ta ko da akwai sauran abinda suke bukata ta girgiza kai ya lura tabatason yawan magana dan haka ya kyaleta suka Yi sallama da cewar zai dawo gobe idan sakina tazo dan tace itama nan zata dawo ......MMN SUDAIS ce
YOU ARE READING
zuciyar masoyi
Romancezuciyar masoyi labari ne akan tsantsar tsaftatacciyar soyayya mai had'e da yan'uwantaka, yana matukar kaunarta fiyye da komai nashi, sai dai adaidai gabar da zai mallaketa ,mahaifiyarsa ta kawo wa zuciyarsa da rayuwarsa tsaiko .......