*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

1️⃣

Gudu-gudu sauri-sauri take tafiya tana waiwaye kamar zata hantsila, kallo d'aya zakayi mata ka fahimci bata cikin nutsuwarta,
a mugun kid'eme take, ganin ta shigo cikin mutane yasata tsayawa had'i da durk'usawa tana fitar da nishin wahala,
ajiyar zuciya ta sauke ta goge gumin data gaji da gogeshi, " sannu baiwar Allah, taji an furta daga bayanta, a matuk'ar tsorace ta kalli inda tajiyo sautin maganar ta fito,
ganin yadda fuskasta ta bayyana tashin hankali yasashi cewa " lafiya kuwa!?

Yayi maganar yana k'arewa jikinta dake rawa kamar mazari kallo, batayi mishi magana ba, ta taka k'afarta dakyar a galabaice zata bar wajen,
saurin shan gabanta yayi yana fad'in " kada ki tafi ki zauna ki huta mana, yayi maganar cike da tausayawa, batayi mishi magana ba ta cigaba da tafiya,
a zatonshi bataji abinda yace ba, dan haka ya sake shan gabanta cike da tausayawa yanayinta yace " baiwar Allah ki d'an zauna ki huta,
ganin bata bashi amsa ba yayi zaton ko kurma ce, dan haka ya yarfa mata hannu irin yadda ake yiwa bebaye magana had'i da cewa " bakya jina?

Kallan datayi mishi ne ya bashi tabbacin tuninshi ba gaskiya bane,
bayyi niyyar k'ara yi mata magana ba amma abun *K'ADDARA* haka nan yaji baiji dadin yadda tayi mishi ba,
" wulak'aci babu kyau musamman ga mutumin dayaso taimakawa rayuwarki, bada wata mammunar manufa nace ki huta ba, taimakonki nayi niyar yi amma tunda hankalinki bai kyauta ba shikenan,
dummmm! hawaye na gangaro mata, batare data sani ba kalmomi biyu zuwa uku suka sub'uce daga bakinta,
" kayi hak'ur.....! da wani irin sauri ta jiyo ta kalle shi tana girgiza kanta tare da ja baya cikin matsanancin tashin hankali,
" na shiga uku magana nayi maka?

"Na amsa maganarka?

Binta yayi da kallo mai ma'anoni da dama ciki kuwa harda kallan mahauciya, cikin tsawa da masifa tace " meyasa ka matsani nayi maka magana?

" Meyasa baka barni na tafi ba?

Cikin rashin fahimta yace" me kike nufi?

A tsorace tabar wajen da gudu-gudu, ta d'anyi nisa kad'an ta jiyo sautin ihuuu mutumin da k'arfi, cak ta tsaya,
hawaye mai d'umi ya biyo kuncinta muryarta na rawa ta furta " *ALLAH YAJI K'ANKA, UBANGIJI YAYI MANA SAKAYYA,*
*WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA....,* duk da inda sabo yaci ace ta saba, amma ta kasa sabawa da jiyo ihuuun azabar fitar ran mutane da dama,
wanda itace ta zama *SILAR MUTUWARSU,*
babu irin mutuwar da bata gani ba, babu wani tashin hankali, tsoro, firgici da kid'imar da zasu gigitata, amma ya zatayi dole akwai tausayin rai, ta juya ta kalli gawar mutumin kwance cikin jini,
tafiya ta cigaba dayi batare datasan inda take nufa ba, zuciyarta ta k'ek'ashe ta bushe babu d'igon tsoro a cikinta,
tafiya tayi sosai kafin ta isa bakin titi, mutanen da suka santa suna ganinta suka fara guduwa suna ihuuu, siraran hawayen da suka biyo kuncinta ta goge tana cigaba da tafiyarta batare data tsaya ba, sai da tayi tafiya me nisa kana ta samu me napep, ta tsaida ta hau, " ina zaki Hajiya?

Wajen gari ta bashi amsa tana duk'ar da kanta k'asa, jin shiru bai tada mashin din ba yasata d'agowa tana fad'in "muje mana Mala.....,
sark'e mata maganar tayi a mak'ogwaro ganin mutumin a kwance kan sitiyarin napep din,
idanuwanshi a waje kallo d'aya zakayi mishi kasan babu rai a jikinshi, wani irin ihuu ta saki had'i da dirowa daga napep din,
kasa motsawa tayi balle tayi k'ok'arin guduwa, kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita, " banyi mishi magana bafa,
koda nayi mishi ma bai amsa min ba, meyasa bazaka barni haka ba?

"Meyasa bazaka bar rayuwata ta huta ba, bayan iyayena, 'yan uwana da dangina *DAKA KASHE, HAKAN BAI ISHEKA BA, ACE DUK NAMIJIN DA YAYI MIN MAGANA, KO NAYI MISHI YA AMSA SAIKA KASHE SHI MEYASA....?*

Wata irin mahaukaciyar dariya ta jiyo daga bayanta, bata motsa ba, balle ta juya ta kalleshi, ko ba'a fad'a mata ba tasan waye,
tasan shine, dan ya zama inuwarta, ya zame mata damkar ruhi da gangar jikinta, bata ganinshi da idonta,
amma duk inda ta sanya k'afa yana biye da ita, "wakike tambaya bayan kin san kece silar faruwar komai,
* DEEYANAH* ke kika ja komai duk abinda ke faruwa da rayuwarki ke kika jawa kanki, yayi maganar yana zagayata, cikin kuka tace " na sani... nasan nice sila,
shiyasa nake rok'onka nake kuma baka hak'uri akan ka fita daga rayuwata, da sauri ya durk'usa gabanta yana yi mata wani irin kallo,
" hak'uri fa kikace *DEEYANAH* wannan wacce kalma ce mara dad'in ji da furtawa, kanshi ya d'aga yana kyalkyala mata dariya,
" karya kike Deeyanah ba wannan maganar, har abada bazan barki ba, ni inuwarki ne, ko mutuwa tare zamu mutu, kuma a kabari d'aya za'a binne mu,
ke ko mutuwa kikayi bazan tab'a barinki ki kwanta lafiya a kabarinki ba, haka idan ni na rigaki mutuwa fatalwata bazata barki ba Manassah,
ta bud'e baki zatayi magana tajiyo hayaniyar mutane, kafin tayi wani yunk'uri sun k'araso inda take,
saurin mayar da kallanta tayi inda yake taga bayanan, al'amarinshi har tsoro yake bata mutum kamar aljani ba'a ganinshi sai dai aikinshi,
fincikota wani k'ato yayi ya d'agata sama ya buga da k'asa yana fad'in " tsinanniya annoba, wacce ta zama sanadiyyar mutuwar ahalinta da jama'ar da basu ji ba, basu gani ba,
da ace ban san mutuwa hutu ce a gareki ba, da ni da kaina zan kasheki, inyaso nima a kashe ni, daga gefe wani ya amshe da cewa " aiko kasheta zamuyi yanzu bak'ar daga,
taya zamu sakawa shegiya mu k'ona tsinanniya, " bazamu kasheta ba mu d'ibarwa kanmu sai dai mu nad'a mata dukan da saita kasa tashi,
daga gefe wani yayi ihuu tare da d'ora hannu aka yace " ga gawar wani ta kashe shi, kukan kura mutanen sukayi suka afkawa Deeyanah da duka,
saida suka had'a mata jini da majina, kafin suka d'auketa suka kaita daji suka yar,
" idan muka k'ara ganinki a ariyar unguwar nan wallahi sai mun aiki inda kikayi sanadiyyar aika iyayenki, ya k'arashe maganar yana tofa mata yawu a fuska,
sosai take kuka kamar ranta zai fita, mussamman da ake jifanta da kalmar tayi AJALIN AHALINTA, kalmar na mata ciwo a duk lokacin da aka jefeta da ita,,
bataso sanya su cikin bala'i bane, data amsa musu maganarsu, tasan matuk'ar ta amsa d'ayansu bazai koma gida da rai ba duk yawansu, tasan sayya k'arar dasu tas, a hakan ma bata da tabbacin zai kyale su, tunda suka tab'a tafiyarta,
ba ruwanshi da mata, idan kaga ya tab'a mace to matsawa Deeyanah tayi, kota shiga rayuwarta,
amma namiji hmmmm ko kallanta kayi da wata manufa to sunanka *GAWA* musamman idan kayi mata magana ta amsa,
bata damu da cikin bola take ba, ta cigaba da zama tana kuka, ta mik'e da niyyar barin wajen ta fara jiyo ihuuuun mutanen da suka daketa yanzu,
ido ta runtse ta k'arfi hawaye na zubo mata, tun tana jiyo ihuuuun su harta ji shiru, alamar ya gama dasu, 'yar tafiya tayi kad'an ta samu waje ta zauna, kanta ta d'aga sama ta kalli sararin samaniya, a hankali komai ya soma dawo mata sabo kamar a lokacin yake faruwa.

*WAIWAYE...*

Family d'insu Deeyanah babbane a garin Kano, Malam Abduljalal shine mahaifinta, kusan gaba d'aya zuri'arsu suna zaune ne a Estate d'aya, a unguwar magajin rumfa
sai danginsu na can nesa dake zaune a k'auyuka ko wani garin amma muddin kana cikin garin Kano to kana cikin Estate d'insu,
duk k'ank'antar alakarku, suna da wayewar ilimin boko duk da basu bari iliminsu ya gurb'atasu ba, dan sun cud'anya ilimin bokon dana addini,
haka ma yaransu a nutse suke sun samu tarbiyya dai-dai gwardado, tsaka-tsaki ne su, baza'a ce basu da tarbiyya ba, haka baza'a kira su da masu cikekkiyar tarbiyyar Islama ba,
dan suna had'awa da boko, da wayewar zamani sai dai wayewar zamanin ba wai irin ta yaran nan fitsararru masu shaye-shaye da fidda tsiraici, marasa tarbiyya ba,
yaransu a nutsu suke dai-dai gwargwado, Aina'u itace mahaifiyar Deeyanah, kuma ita kad'ai ce matar mahaifinta ,
yaransu hudu, mata uku namiji d'aya, Azan shine babba sai k'annanshi mata Azwah da Azrah, sai autarsu Deeyanah , Azrah da Azwah sunyi aure tuni, ya'yan wan mahaifinsu suka aura, Abdulraheem da Abdulrasheed uwarsu d'aya ubansu d'aya, Abdulhakeem shine mahaifinsu, su biyar ne a wajen iyayensu, hudu maza sai autarsu mace Busainah, dukkaninsu suna nan zaune cikin Estate din, suna yiwa yaransu auren zumunci,
koda wasa wata ko wani cikin zuri'arsu bai taba auren bare ba, Aina'u mahaifiyar Deeyanah , mace ce ta gari, ga hak'uri da kawaici,
shiyasa duk yawancin yaran da suka taso a Estate d'in ita ta rik'esu, harta aurar dasu.

DEEN...

D'a ne ga Abdhulhakeem da Halimatu yana da yayye, maza biyu Abdhulrasheed da Abdulraheem, sai k'anwarsa Abeerah, yayyan Deen suke auran yayyan Deeyanah,
Deen yana d'aya daga cikin yaran da Ammah (Aina'u ) ta rik'e, kuma har gobe yana gidan, sosai Ammah da Babah (Abdhul Jalal) ke ji dashi.

~JIDDARH~

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now