13

376 20 0
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh

1️⃣3️⃣

Kasa juyowa tayi saboda hanashi ganin yanda kirjinta ke bugawa yana harbawa da k'arfi, kamar wanda ya tuna wani abu ya saki hannunta had'i da d'an kamewa ya juya gaban mirror yana goge jikinshi da d'an k'aramin towel, kamar b'arauniya taja k'afa zata fita har ta kai bakin k'ofa taji yace " ki wanke min bathroom, cike da mamaki ta juyo ta sauke idanuwanta akanshi tana juya maganar cikin kanta yadda kasan bashi ne yayi maganar ba, " ko in cire miki towel d'in yadda zaki ji dad'in k'are min kallo?

Saurin d'auke idonta tayi daga kanshi dan bama ta kula dagashi sai towel d'aure a k'ugunshi ba, juyawa tayi zata fice saboda sai yayi mata kamar kunnenta ne bai ji mata dai-dai ba, hannunshi ya mik'a zai sake rik'ota tsantsin ruwan wankan jikinshi ya d'ebeshi, yayi baya zai fad'i batare daya sani ba ya rik'o ta, ta fad'a saman bed rigingine shi kuma ya fad'a kanta, lips d'inshi na gogar nata, tsayawa sukayi a haka suna kallan kwayar idon junansu while zuciyoyinsu na tsananta bugawa da wani irin yanayi me wuyar fassarawa.

" D'aga ni!.

Ya fad'a har lokacin idonshi cikin nata, kallan renin hankali tayi mishi tana jin yadda ya sakar mata nauyinshi gaba d'aya.

" Nace ki d'aga ko?

Bai bari tayi magana ba ya d'ora da " ki tashi ki wanke min bathroom...

Baki ta cono gami da cewa " to ba saika d'aga ni ba?

" Tayaya zan wanke maka bayan ka danne ni, tayi maganar a wahalce tana jin kamar k'asusuwanta zasu karye, had'i dayi mishi kallan ka raina min hankali, ido ya zubawa d'an tsukakken bakinta daya k'arawa fuskarta kyau,  yana san bakinta, dan yafi san bakinta a fuskarta sai fararen idanuwanta, ido ya runtse had'i da tattaro gaba d'aya gwarin gwiwarshi ya had'e bakinsu, a firgice ta zaro idanuwanta waje kamar zasu fad'o k'asa.

Cikin salo yake tsotsar bakinta da harshenta while yana tura mata harshenshi cikin bakinta, so take tayi mishi magana amma babu bakin magana, ya rufe bakinta ruf da nashi bakin ta yadda bazata iya kwacewa ko tayi magana ba, mutsu-mutsun kwace kanta ta somayi dan har lokacin yana kanta, wani irin bak'on yanayi me sanyi-sanyi zafi-zafi suke ji a jikinsu, yanayin da basu iya tantance hak'ik'anin shi ba.

Bazai iya dauwarewa ba, bazai tab'a iya jurewa ba yau saboda yadda take goga mishi k'irjinta da boobs d'inta a nashi k'irjin, kamar zata fasa ihuuu lokacin da taji hannunshi saman boobs d'inta, cikin rashin kuzari ta had'iyi yawun dayake tayi mata yawo tsakanin bakinta da mak'ogwaronta, a hankali taji wani irin dad'i me had'e da sanyi yana shigarta, numfashin data kasa rik'ewa ta fitar had'i da lumshe idanuwanta tana sake bashi damar yin komai, ta k'asan bayanta ya zura hannunshi ya zage zip d'in rigar jikinta yayi k'asa da rigar, sai da numfashin shi yayi tsayawar 'yan sakanni lokacin da yayi arba da boobs d'inta dako Bra babu, inde tana gida lokuta da dama bata fiya saka bra ba haka take zama, gasu nan a tsaye jajur dasu gwanin ban sha'awa, bai san sanda ya cire bakinshi daga cikin nata ba ya mayar kansu, saukar bakinshi da d'an lemar yawu data ji saman boobs d'inta ya k'ara birkita 'yar k'aramar kwakwalwarta.

Abubuwa suka d'auki zafi romancing d'inta yake cikin salo while yana bida ita a hankali yadda ya kamata, dukkaninsu sun gama tafiya wata duniya ta daban basa cikin nutsuwarsu, towel d'in jikinshi ya soma k'ok'arin zamewa tayi saurin rik'e mishi hannu had'i kwab'e fuska a shagwab'e muryarta bata fita sosai can k'asan mak'oshi tace " a'a please!

Fasawa yayi ya kwantar da kanshi a saman k'irjinta yana mayar da numfashi, nauyinshi yayi mata yawa bazata iya d'auka ba d'an zamewa ta soma yi tare da mutsu-mutsun tashi, fahimtar abinda ke faruwa yayi dan haka ya d'agata jikinshi babu kwari ya zame gefe ya kwanta yana mayar da numfashi, " sorry! ya furta so calm, batayi magana ba ta mik'e ta fice yana kallanta har ta fice yana san yayi mata magana amma bakinshi yayi mishi nauyi.

Tana fita sukayi kicib'us da Ammu da Azrah kallan tsanaki Azrah tayi mata tana murmushi tace " daga cewa kije ki dubo shi shikenan sai mu jiki shiru, nina d'auka ma can zaki kwana, harara Deeyanah ta watsa mata had'i da shigewa bedroom d'inta batare data ce mata komai.

Saman bed ta fad'a tana mayar da numfashi, ta dad'e kwance tana jin hannunshi yana yi mata yawo a jikinta har lokacin kafin ta mik'e ta fad'a bathroom tayi wanka had'i da d'auro alwala ta fito.

Yakai awa d'aya da mintuna yana kwance inda ta barshi ya kasa tashi sai juyi yake har lokacin bai dawo dai-dai ba, sai da yaji kiran sallar azahar kana ya mik'e a daddafe ya fad'a bathroom.

Bayan sati d'aya....

Sanye take da doguwar rigar Turkish Material rigar tayi mata kyau sosai kamar a jikinta aka d'inka rigar shape d'inta ya fito d'as, ga rigar so softy & slink tabi jikinta ta kwanta, d'an heavy make up tayiwa fuskarta ta shafa red jan baki, ba k'aramin kyau jan bakinta yayiwa fuskarta ba, ta gaji da zaman cikin gidan, ga ba aiki balle tayi committing kanta busy kota samu d'an sauk'i.

Kanta tsaye ta fito harabar estate d'insu ta nufi garden da nufin zama koba komai ta kalli furanni, Deen da Azan da wasu abokanan Azan tsaye suna magana, magana Deen yake yiwa d'aya daga cikin abokanan Azan amma kwata-kwata hankalinshi baya wajensu, bin inda yake kallo Deen yayi da kallo shima dan yaga meya d'auke masa hankali haka daya shagala yana kallanshi.

Deeyanah ya gani tana nufar Garden jikinta ko mayafi babu balle Hijab kanta kawai ta d'aurawa wani d'an yalolon mayafi, "wow! Allah yayi halitta anan!

Abokin Azan ya fad'a fuskarshi d'auke da murmushi har lokacin idonshi kanta, abinka da mutum mai bak'ar zuciya, take yaji wani irin abu ya tsarga mishi tun daga tafin k'afarshi har zuwa tsakiyar kanshi, idanuwanshi sukayi jajir, yayinda jijiyoyin kanshi sukayi rad'o-rad'o, ganin yanayin da Deen ya shiga yasa Azan rik'o hannun abokinshi yana murmushin yak'e yace " muje!

Ya fad'a yana jan abokin, " dama akwai irin wannan halittar a k'asar nan?

Abokin Azan ya fad'a yana zare hannunshi daga cikin na Azan, babu abinda Deen yake yi sai k'ok'arin saita kanshi tare da danne abinda ke taso mishi ta cikinshi, " i love her! ya fad'a yana nufarta, ai Deen ji yayi kamar ya watsa mishi acid bai san sanda ya kifawa abokin Azan marukan da suka sakashi kifawa ba, yasa hannu ya d'ago shi gami da nuna mishi yatsa yace " ka koyi girmama matan wasu, ka koyi bawa matan wasu daraja da k'ima a bayyane dan kaima a girmam mahaifiyarka, ya sake shi had'i da nufarta ranshi a masifar b'ace, duk abinda ke faruwa bata sani ba, tafiyarta take d'as-d'as kamar me jin tausayin k'asa.

"I'm very sorry, she's his wife.

Azan ya fad'a yana dafa kafad'ar abokin nashi.

Taku taji yana nufota dan haka ta d'aga idonta ta kalli wajen kamar bata so ganinshi ya nufo a birkice kamar ba shiba yasata firgita, tsoro da tashin hankali ya fito ya bayyana k'arara saman fuskarta, bakinta na rawa tace " Ya.....ya...!, bayyi mata magana ba ya damk'i hannunta had'i da nufar cikin gida da ita, Ammu na zaune a falo ya wuce rik'e da hannun Deeyanah binsu tayi da ido harta bud'e baki zatayi magana ta fasa, ya shige bedroom d'inshi da ita, had'i da dannawa k'ofar key, yayi cilla da ita saman bed, saurin mik'ewa tayi daga kan gadon, ya juya mata baya tare da cusa hannunshi cikin sumar kanshi.

Ji yake kamar ya shak'eta yayi ta dukanta, ji yake kamar ya d'auki wuk'a yayi ta cakawa abokin Azan har ya mutu, ya rasa meke yi mishi dad'i a duniya, " Ya....ya!

Ta fad'a cikin sanyinta, shhhhhh yace yana d'ora hannunshi saman lips d'inshi, ya d'ora da fad'in " kiyi shiru kawai!.

Yadda yayi maganar ya k'arasa tsoratata ta fasa kuka marar sauti sosai, idanuwanshi ya runtse had'i da kaiwa iska naushi da hannu, juyowa yayi ya kalle ta ya had'iyi wani abu kana ya nufeta, ya d'ago ta ya rungume ta da k'arfi  har saida tayi 'yar k'ara " ashhhhh!, sasauta rungumar da tayi mata yayi, tana jin yadda k'irjinshi ke sama da k'asa, tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa da k'arfi.

"Ina sanki Deeyanah.

"Ina sanki da duka zuciya ta.

"Ina kishinki karki bari kishinki ya illata ni koya kashe ni, karki bawa kowanne d'a namiji samun dama akanki, zan iyayin komai akanki Dee! raina yana bani kamar zan iyayin kisa akanki, ina ji a jikina zan iya kashe kowa a kanki, dan Allah karki bari hakan ta faru, ki killace min kanki ki zama tawa ni kad'ai please, ni kuma nayi miki alk'awarin shinfida miki rayuwata a k'asan k'afarki.....

Yayi maganar cike da zallar raunin zuciya, ita kam gaba d'aya tsoronshi ya gama cika ta, ji take kamar ta saki fitsari, duk abinda yake fad'a jinshi kawai take yi amma ta kasa furta komai, k'ara matseta yayi tsam a jikinshi yana jin sauk'i da raguwar rad'ad'in dayake ji........

JIDDARH

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now