34

291 20 4
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

3️⃣4️⃣

Wayar Babah yabi da kallo kana ya kalli Deen suka had'a ido, sake kiran wayar yayi yaji busy sau uku yana kiran wayar amma busy hakan ba k'aramin hasala ran Babah yayi ba, wayar Ammu ya kira tana d'agawa yace " jeki taho min da Deeyanah, bai jira jin abinda zatace ba ya kashe wayar.

Abbi na d'agawa ta fasa kukan kissa wiwi, " subhanallah lafiya Deeyanah?

Cikin kuka da marairaicewa tace " Abbi Deen ne ya kai k'arata gun Babah kan nace bazan bishi America ba saboda tarbiyyar Deedee, " to! ikon Allah, yanzu Ina Babah da Deen d'in?

"Suna falon Babah, " ki taho falon nima bari naje can na same su, cikin zumud'i ta amsa da "to dan tasan duk wacce za'ayi Abbi bazai tab'a bari ayi mata dole ba, tana kashe wayar Abbi ta kira wayar Babah, amma harta tsinke bai d'aga ba, zata sake kiranshi Ammu ta shigo, a d'an tsorace ta mik'e tana gaida Ammu kafin tayi shiru tana jiran taji abinda zatace mata dan tasan ta  ba wasa, " wani laifin kika yiwa Babanki ne!?

Da saurinta ta girgiza kanta gami da cewa " a'a! " hmmm kedai kika sani, yace kije falonshi yana san ganinki, jikinta na rawa tabi bayan Ammu, hanyar part d'insu Ammu ta nufa Deeyanah tayi saurin cewa " Ammu ke bazaki wajen kiran ba?

"Akan me zani?

"Ni 'yar aike ce a tsakaninku mahaifi ne yace na kira mishi 'yarshi na kuma isar da sak'o na meye nawa da zanyi katsalandan a ciki!?

A fili ta sauke ajiyar zuciya cikin ranta take godewa Allah kan k'in zuwan da Ammu tayi, da Ammi ce ma da d'an sauk'i-sauk'i dan tasan idan aka cirza bayanta zata bi, " Wai bazaki tafi bane kika tsaya kika tsare ni da ido kina mimi da baki!?

Saurin barin wajen tayi kafin Ammun tace zata biyota, tana kaiwa k'ofar zata shiga Abbi na kawo kai, a hankali ta fitar da sassanyan numfashi had'i dayin hamdala cikin ranta, sai da ta baari Abbi ya wuce gaba kafin ta bi bayanshi bakinta d'auke da sallama, daga Babah har Deen babu wanda ya amsa mata sallamar sai ma harara da Babah ya galla mata yana fad'in" wato sai da kika biya kika taho da Abbanku saboda kin san baki da gaskiya ko?

Kanta ta sunkuyar had'i da nemar guri ta zauna kana ta d'an rusuna tace " Ina yini Babah?

Batare daya amsa gaisuwar tata ba yace " kije ki fara shiri jibi zaku wuce in sha Allahu, sai da ta k'ara yin k'asa da kanta kana tace " Babah dama bance bazan bishi babu wani dalili ba, kallan banza Babah ya watsa mata yana fad'in " ki rik'i dalilin naki.

"A'a fa Abduljalal karkayi gaggawar yanke hukunci batare daka ji ta bakinta ba itama, "ai dama nasan dan haka ta sako ka a gaba.

Dariya Abbi yayi kafin yace " ta sako ni a gaba kuma?

"Eh mana, danka shigar mata ba, Abbi yayi murmushi kafin ya kalli Deen yana fad'in " meke faruwa ne!?

Cikin girmamawa ya kwashe yadda sukayi kan komawarsu America ya sake fad'awa Abbi, a fili Abbi ya sauke ajiyar zuciya had'i da jinjina kanshi.

"Kaji fa fisabilillahi in ba shirme ba har mijinki yace ki shirya ku koma ki tsaya kina wani b'ata lokaci dan samun waje.

Ita kam ido ta zubawa Deen tana k'ara ganin girma da k'imarshi kan rashin fad'awa su Babah hanashi hakk'inshi da take yi, wani mugun tausayinshi taji yayi bala'in kamata, hawayen tausayinsu dake shirin zubo mata take ta k'ok'arin mayarwa, ji take yi tamkar ta bishi amma wane ita fad'an yafi k'arfinta, dan idan ta sake tayi kuskuran binshi komai yana iya faruwa.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now