10

397 23 3
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh

🔟

Take duk ilahirin jikinshi ya d'auki kerrrrma idanuwanshi suka rufe ruf baya ganin komai sai duhu, a haukace Ajlaal yayi kan Babah ya rik'e kwalarshi ya d'aga hannu zai nausheshi, jini nabin bakinta ta d'aga murya da k'arfi tace " Baba na ne mahaifi Ajlaal,
hannunshi ya dunk'ule had'i da dukan iskan bayan ya saki Babah, Babah da sauran jama'ar dake wajen suman tsaye sukayi cike da mamaki,
gaba d'aya 'ya'ya mazan Family d'in sukayi kan Ajlaal suna dukanshi kamar zasu kashe shi,
Babah da har lokacin yana tsaye kamar an dasa shi yayi k'arfin halin cewa " ku daina dukanshi, ba laifinshi bane laifin 'yar mu, ku kyale shi bashi da laifin komai,
Abbi yace " ku fitar mana shi daga gidanmu, cali-cali sukayi da Ajlaal suka fitar dashi waje,
bai damu da yadda jikinshi yayi jina-jina ba ya mik'e da sauri ya shiga mota, ikon Allah ne yakaishi gidansu, daga yadda yayi parking iyayenshi suka san ba lafiya,
a tare Hajiya Halimatu da Alhaji Basaan suka fito, ganinshi haka a birkice kamar wanda ya kwato daga bakin kura yayi masifar d'aga musu hankali dan duk duniya babu abinda suke so sama da Ajlaal,
" Abba nace kaje tunda wuri ka nemar min auren Deeyanah kak'i, idan na rasata mutuwa zanyi Abbah, wallahi mutuwa zanyi, yayi maganar yana dafe saitin zuciyarshi,
jikinsu na rawa suka tallafeshi suna tambayarshi " lafiya Ajlaal?

"Meke faruwa ne?

"Ba lokacin doguwar magana Abbah inba haka ba lokaci zai k'ure zan rasata rasawa ta har abada, kazo muje gidansu Deeyanah yanzu ka nema min aurenta dan Allah Abbah,
Alhaji Basaan zayyi magana Hajiya Halimatu ta daka mishi tsawar datasashi rud'ewa " dalla Malam karka tsaya b'ata lokaci d'ana ya mutu,
wallahi idan Ajlaal ya mutu kaima saika bishi lusari kawai ka tsaya kana shirme rayuwar  d'anka na neman salwanta  kan ya rasa abinda yake so,
a dururuce Alhaji Basaan ya mik'e yana fad'in" to to  tashi muje Ajlaal , " kai kad'ai zan bari kaje neman auren kaje kayi hauka ka lalata komai?

"Tsaya nazo muje tare, tayi maganar tana komawa cikin gida.

Abbi da Deen suka tallafe Babah suka shigar dashi babban  parlour'n gidan, duk akabi bayansu har matan, parlour'n yayi shiru ba mai magana, babu abinda ke tashi sai sautin kukan Deeyanah,
tsawa Azan ya daka mata yana fad'in " dalla yiwa mutane shiru mutuniyar banza kawai,
Hannu Babah yasa a aljihu ya ciro kud'in da baisan adadinsu ba, ya mik'awa Abb muryarshi na rawa can k'asa yace  " ga sadakin d'ana Deen nan ina nemar mishi auren 'yarka Deeyanah.

Duk da halin da take ciki bai hana ta shiga mummunan tashin hankali ba, gabanta yayi mummunar fad'uwa,
a razane ta d'ago kanta ta kalli Deen suka had'a ido, in banda hawaye babu abinda ke rige-rigen sauka saman kuncinta,
kanshi ya langwab'ar gefe yana kallan kwayar idonta, Abbi ya kalli Babah cike da neman tabbacin abinda ya fad'a,
gane irin kallan da Abbin keyi masa yasa Babah gyad'a kanshi tare dayin murmushin k'arfin hali, dan bazai iya fad'ar koda kalma d'aya bace,
" me kake san ce min Abduljalal?

"Karka yanke hukunci cikin fushi da b'acin rai, kar muyi abinda daga baya zai raba kanmu, ya kawo rugujewar zumuncinmu, farin cikinmu da kwanciyar hankalinmu,
kar muyi abinda zai tarwatsa kanmu ya kawo lalacewar komai, dakyar Babah ya iya bud'e baki da fad'in " babu komai sai Alkhairi in sha Allah,
Abbi ya bud'e baki zayyi magana cikin sanyi yana danne abinda ke taso mishi ya katse shi da fad'in " dan Allah Yaya....!
ni dai alfarma nake nema a wajenka ta aurawa d'ana 'yarka in kuma....! shiru Babah yayi ya kasa k'arasa abinda yayi niyyar fad'a,
Abbi ya mayar da kallanshi ga Deeyanah da Deen, kan Deen duk'e, fuskarshi fayau cike da annuri, while Deeyanah nata faman kuka kamar ranta zai fita,
" dan Allah Yaya please! Babah ya kuma fad'i har zuwa lokacin yana mik'a mishi sadakin, jikin Abbi a sanyaye ya karb'a, anan take a gaban kowa, aka d'aura auran Deen da Deeyanah,
ana shafa fatiha Babah ya sauke numfashin da bai san yana rik'e dashi ba, yace " Allah ya sani dai-dai nayi, Ubangiji yasa hakan ya zama Alkhairi,
Na yafe muku duniya da lahira, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari, ya d'ora da " yaushe zaku tafi?

Yayi maganar yana kallan Deen, kanshi ya k'ara duk'arwa k'asa cike da matsananciyar kunyar Babah data saukar mishi a lokaci d'aya yace " cikin satin nan in sha Allah,
" Allah ya kaimu, Babah ya fad'a yana mik'ewa ya fice, Abbi ya kalli Deeyanah cike da tausayawa dan yaga kamar bata san Deen d'in,
bayasan yak'i yarda da hukuncin da Babah ya zartar ne dankar ya zargi wani abu musamman da Deen ya kasance d'anshi,
" Allah baku zaman lafiya,  Abbi ya fad'a yana mik'ewa, gaba d'aya suka mik'e suka fice daga parlour'n, a harabar gidan suka iske Babah da Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu tsaye,
mamaki shinfid'e a saman fuskar Abbi ya k'arasa wajen tare da mik'awa Alhaji Basaan hannu suka gaisa, Deen da Deeyanah da sauran 'yan gidan sunyi tsaye suna kallansu,
"Mu shiga daga ciki, muyi magana, ba musu suka koma parlour'n gaba d'ayansu har su Deeyanah, bayan kowa ya zauna Abbi ya tsaida kallanshi akan Alhaji Basaan cike da san jin meke tafe dasu,
sai da Alhaji Basaan yayi gyaran murya had'i da satar kallan Hajiya Halimatu kana ya soma magana,
" munji abinda Ajlaal yayi tabbas bai kyauta ba, muna baku hak'uri a bisa abinda yayi, ya d'anyi shiru kafin ya d'ora da " tun a kwanakin baya ya sameni da maganar inzo na nemar mishi auren Deeyanah a wajenku to sai aka samu d'an akasi Allah yasa ban zo ba,
murmushi Babah yayi yana fad'in " ayya sai dai kun makara dan yanzu-yanza aka d'aurawa Deeyanah aure da d'an uwanta Deen,
cikin kid'ima Ajlaal ya mik'e tsaye kanshi ya shiga sarawa, ya kalli Deeyanah da Deen, murmushin da Deen ya sakar mishi ya bashi tabbaci akan maganar Babah,
" kaga sadakinta a hannuna, cewar Abbi yana nuna musu sanadin Deeyanah...... ihunnnn da Ajlaal ya saki yasa Abbi yin shiru,
" nooo! A'a hakan bazata tab'a faruwa ba, Deeyanah tawa ce ni kad'ai, danni kad'ai aka halicceta, yayi maganar kamar zararre,
Gabanta yaje ya durk'usa ya k'ura mata ido, " kina so na Deeyanah na sani, ina sanki kin sani, karki bari a rabamu please yayi maganar yana k'ok'arin rik'o hannunta,
cikin zafin rai Deen ya had'ashi baya, " are you mad?

" Kasan me kake k'ok'arin yi kuwa?

"Matar tawa zaka tab'a a gaba na dan iskanci?

Jin Deen ya kira Deeyanah da matarshi yasa Ajlaal durk'ushewa k'asa ya kifa kanshi yana wani irin kuka mai gunji, Deen ya rik'o hannun Deeyanah suka bar parlour'n, Abbi da Babah da kowa suka fita suka bar Ajlaal , Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu zaune.

" Saika tashi mu tafi asararre lusari wanda ya kasa nemarwa tilon d'ansa aure, dan mutuwar zuciya ka kasa cika masa buri da muradinshi, zungwi-zungwi sumi-sumi ya mik'e ya fita.

D'akinta ta wuce direct ta fad'a saman bed had'i da sakin rikitaccen kukan da ta rasa dalilin yinshi, ita dai tasan ba kukan rasa Ajlaal take yi ba tunda dama can ba wani sanshi take ba, ta d'auke shi as friend d'inta, haka bana auren da aka d'aura mata da Deen take yi ba, tunda bata k'inshi, takamaimai ma bata san tana sanshi ko bata ranshi ba, tasan dai takan jishi sosai cikin ranta, haka tana yawan tunaninshi, duk sanda ta tuno shi gabanta yakan fad'i, sosai take fitar da sautin kuka while duk ilahirin jikinta na motsa.

A hankali ya turo k'ofar bedroom d'inta ya shigo, shi kad'ai yaji sallamar da yayi a saman leb'enshi, mazaunanta dake motsawa kamar an k'ulla ruwa a leda ya zubawa ido yana jin wani abu na taso mishi, ya dad'e tsaye idonshi kan k'ugunta kana ya taka k'afarshi cikin mutuwar jiki ya k'arasa gadon ya zaune a gefe d'an nesa da ita.

"Deeyanah!

Ya kira sunanta a kasalance, cak ta tsayar da kukanta, had'i da saurin goge hawayenta, bata san shigowarshi ba sai sautin muryarshi taji a kusa da ita, sake kiran sunanta yayi da yanayin daya sata tashi zaune, d'an kallanshi kana ta sunkuyar da kanta k'asa.

"Deeyanah!

Ya kira sunanta da wani irin yanayi me nauyi, yanayin daya nuna har cikin idanuwanshi, yanayin da yayi dai-dai da kamar ya kwashe b'angarorin zuciyarta data tarwatse ya ririta su cikin hannunshi ya mayar da ita kurbinta, numfashi taja ta sauke shi tare da abubuwa da yawa cikin kanta.

Idanuwanshi ya sauke cikin nata lokaci d'aya kasala ta saukar mata, ashe k'arya tayiwa kanta data k'i yarda tana sanshi, ashe yaudarar kanta tayi da take tunanin zata iya rayuwa babu shi, da ta hango wata rayuwa tare da Ajlal ashe duk gizo ce.

" Ina sanki Deeyanah! ina sanki fiye da so! ina sanki da duka zuciya ta, ki yarda dani bazaki tab'a yin nadama ko danasanin kasancewa tare dani ba, ki mallaka min kanki da zuciyarki, ki bani damar nuna miki zallar soyayya ta, Deen ya fad'a yana k'ara natsa idonshi cikin nata......

JIDDARH

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now