*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh5️⃣5️⃣
Sai da tayi nisa da wajen sosai kana ta samu gindin bishiyar darbejiya ta zauna bata yi bacci ba har aka kira sallar asuba, kasancewar babu ruwan yin alwala yasata yin taimama, mayafin data d'aura a kanta ta warware ta yafashi sosai a jikinta ta tada sallar, haka kan k'asa babu abun shinfid'awa tayi sallar, bayan ta idar ta d'aga hannayenta sama ta soma yin addu'a while hawaye na bin kuncinta, ta dad'e tana addu'ar har garin Allah ya waye kana ta shafa, ta kakkab'e jikinta sannan tabi hanya dan yunwar data ke ji bazata kyale ta ba.
Ta dad'e tana kartar k'asa da k'afufuwanta dako takalmi babu ga zafin rana, ta k'arasa gari, gaban wata me siyar da koko da k'osai tayi tsaye tana kallan k'osan tana had'iyar yawu kamar mayya, batare dame k'osan tace mata komai ba ta zuba mata a cikin faranti ta mik'a mata, saura kad'an ta afka cikin man toya k'osan saboda yadda jikinta ke muguwar tsuma da kerrrrma.
"Bi a hankali mana, me k'osan ta fad'a tana kallanta, " zaki sha koko?
Da sauri ta d'aga mata kai, alamar eh, batayi mata magana ba ta d'auki robar siyar da kokon ta zuba mata ta saka mata siga da ludayi ta mik'a mata, da hanzari ta karb'a bakinta cike da k'osan data cunkusa a bakinta tace " nagode!
Mai k'osan bata ce mata komai ba illa satar kallanta da takeyi harta gama shan koko da k'osan, ta mik'a mata robar da farantin tana fad'in " nagode sosai Allah ya saka miki da mafificin alkhairinshi yadda kika taimakeni Ubangijin Rahama ya taimakeki, fuska cike da murmushi ta amsa mata da " Amin ya Allah nagode nima.
Maimakon tabi titi saita sake yankar daji ta natsa taitai tafiya, sai da ta fice daga cikin gari kana tasamu gindin bishiya tayi kwanciyar dama ciki ya d'auka dakyar ta kawo kanta wajen saboda baccin da take ji, bacci ya soma d'aukarta taji an jeho mata k'urgumemen abu jikinta firgigit tayi ta bud'e idanuwanta dake cike da bacci, ganinka ba alheri bane ta gani tsaye kanta, (sunan da take kiranshi dashi) yasata saurin bud'e idanuwanta a kanshi.
Wani abu ya wulla mata a cikin kwali, kwalin na fad'uwa ya rabe biyu kan mutum ya mirgino zuwa gabanta kallan abun tayi taga kan wannan mutumin ne daya zuba mata ruwan tsami a jiki ya kuma tofa mata yawu, ko gezau Deeyanah batayi ba balle tsoro ko firgici ya bayyana a tattare da ita, kallan kan mutumin tayi had'i dayin tsaki tasa k'afa tayi ball da kan ta juya ta gyara kwanciyarta tana fad'in " ni ai yanzu naci dubu sai ceto babu wata gawar da zata razana ni, ta rufe idonta da nufin yin bacci amma sai me?
Ranar da komai ya k'are mata a rayuwarta, duniyarta ta tarwatse, farin ciki da walwala suka yanke mata ta shiga dawo mata cikin kwayar idanuwanta.
Waiwaye....
Wayar ta data dame ta da ringing ta d'aga kamar jira yake ta d'aga ya kwashe da mahaukaciyar dariya yana fad'in " tik tok tik tok rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, yau ne adadin kwanakin dana baki zasu cika cif-cif ina fatan kin shiryawa komai, kin shiryawa tarbar aradu daka?
Zatayi magana yayi saurin cewa har yanzu kina da sauran 10 second, so mu irga tare, amma ki sani idan har sakanni goman nan suka cika batare da kin d'auki zab'in daya danace ba har ki mutu kina danasani, so mu fara irgawa 10,9,8,7,6,5,4,3,2,1,0 ....., sai kawai ji tayi ya kashe wayar, wayar ta zame daga kunnenta ta zubawa ido kamar tana jiran wani abu ya fito ta cikin wayar.
Yana tsaye gaban mudubi ya fito daga wanka k'ugunshi d'aure da towel ya matsi lotion zai shafa a fuskarshi wayarshi ta d'an yi k'ara alamar shigowar sak'o kallan wayar yayi haka nan yaji gabanshi yayi muguwar fad'uwa, d'auke idonshi yayi daga kan wayar ya cigaba da abinda yake yi, har ya gama shiryawa bai sake bi takan wayar ba danshi yama manta da shigowar sak'on, jallabiya ya zira, har ya kai bakin k'ofa zai fita wayarshi ta sake yin k'ara a karo na biyu, sai lokacin ya tuna da wayar, komawa yayi ya d'auki wayar yana nufar k'ofar fita daga bedroom d'in yana duba sak'on daya shigo, video aka turo mishi ta WhatsApp da wata new number, video ya danna yayi playing, videon ya bud'e dai-dai lokacin daya d'ora hannunshi akan handle d'in k'ofa.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...