*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh4️⃣5️⃣
Allah ya taimake ta harta koma gidan bai dawo ba, dan daga gidan Ajlaal direct gida ta wuce bata bi ta kan motar ba, balle ta koma inda motar take, jakarta da hijabinta kawai ta aje a bedroom ta fito ta shiga kitchen ta d'ora tuwon shinkafa, fiki sukunbiya da markad'add'un kayan miya ta fiddo daga freezer, ta d'auko non stick ta zuba mai ta d'ora saman gas, dayake kifin a yayyanke yake kuma a wanke yake tas yasata d'ora man, tunda tasan ba wani lokaci zata b'ata ba, cikin ruwan zafi ta saka kifin ya saki, ta sake d'auraye shi ta zuba mishi gishiri ta zuba cikin man tare da yanka albasa me d'an yawa ta zuba cikin dan kar k'arnin kifin ya cika mata gida, ranshi a mugun dugunzume ya shigo gidan, yadda kasan yayi bindiga ya fashe haka yake ji.
Saman sofa ya zube ya kishingid'a da fari bai ji motsinta ba sai daga baya, d'an shiru yayi tare da yin kasak'e da kunne danya tabbatar, sake jin motsinta yayi a kitchen, kamar mara gaskiya ya mik'e ya nufi kitchen d'in, tana ta faman aikin hankalinta kwance yadda kasan babu wani abu, tun shigowarshi tasan ya shigo haka yanzu ma dayake tsaye jikin fridge tana sane dashi, amma yadda kasan bata san Allah yayi ruwan halittarshi a wajen ba, har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya kalle ta sosai yace " kin fita yau ne?
D'an firgigit tayi wai ta tsorota, har da dafe k'irji tace " kai! Yaya ka tsorata ni, bai kula da maganar da tayi ba, ya d'aure fuska babu alamun wasa kwata-kwata a tattare dashi yace " nace kin fita yau ne?
Kai tsaye tace " ba'a gabanka na fita ba koka manta ne?
Sai lokacin ya tuna yana zaune a falo ta fita, sake tsuke fuska yayi yace " da kika fita ina kika je?
"Gidan kunshi naje, kallan da yayiwa hannunta da k'afarta ne yasata dafe goshinta tana murmushi tace " ops ban k'arasa gidan ba nayi faci motar ma acan na barta, kai kaga unguwar Yaya?
"Wai ina 'yan siyasar mu zasu kai hakk'in talakawa ne?
"Wallahi d'ai-d'ai daga cikin 'yan siyar Nigeria ne bazasu ci wuta ba, kallan sosai yayi mata, kamar bazayyi magana ba sai kuma yace " ya akayi kika dawo gida, sai da ta juya idanuwanta kana tace " Napep nahau mana, " wannan lokacin da kika d'auka anan kawai kika tsaya?
Wata irin mummunar fad'uwa gabanta yayi, k'irjinta ya doka da tsananin k'arfi, ta tsaya cak tabar abinda take yi, a hankali ta juyo ta kalli cikin kwayar idonshi, shima tar yake kallan idonta, ganin irin kallan da yake yi mata yasata yin rau-rau da ido zatayi kuka tace " me kake nufi da wannan maganar taka Yaya?
Sosai take k'ok'arin k'ak'aro kuka tace " Yaya zargi na kake yi?
Tsoki ja mtswwww yace "idan ma zargi nake yi laifi ne?
"Ko ba kece kika jawa kanki zargin ba?
Ya fad'a idonshi tar cikin nata, abinda ta hango cikin kwayar idonshi ba k'aramin firgita ta yayi ba, wanda har ya hanata magana, tana kallanshi har ya fice bata iya furta koda kalma d'aya ba, ta dad'e tsaye nan inda ya barta a matuk'ar tsorace da abinda ta gani tattare dashi, cikin sanyin jiki ta juya ta cigaba da aikinta, kafin Magriba ta gama tuwon shinkafa da miyar Ogun leaf dayasha kifi sukunbiya da bushashshen kifi d'an Maiduguri, ga ganda da kwalla, ta zubawa Ammi nata a kula haka ma Ammu, da kanta ta mik'a musu, sama-sama ta tsaya suka gaisa saboda bata cikin nutsuwarta, taso ma tayi sob'o ko coconut drink amma ta kasa tuwon ma danta riga ta d'ora ne.
Bazata iya fassara abinda ta gani cikin idonshi ba amma koma meye abun tayi masifar tsorata dashi, har tayi wanka tayi sallah a firgice take, sai da tayi waya da Ajlaal kana yad'an kwantar mata da hankali.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
EspiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...