4

614 28 5
                                        

*BAK'AR SHUKA...!*

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

Bazan rink'a yin posting ranar Asabar da Lahadi ba, daga Monday zuwa Friday zan rink'a yin posting in sha Allah.

4️⃣

A fusace ya juyo tare da d'aga murya yace " enough ya isa please! Am tired from all your drama, stop it please, yadda yayi maganar cikin hargowa ya jawo hankalin dalibai,
kan kace me an cika wajen makil, ya cigaba da cewa " bana sanku! ni kadai ne namiji a makarantar nan?

"Ni kadai ne keda abinda kuke so?

" Ni kadai ne nayi dai-dai da kalar namijin ra'ayinku?

" Ya isa please! stop it right now, bana sanku bani da ra'ayin soyayya daku, haba abun ya isheni haka kowacce mace ni, kowacce mace tana so na, koma zanyi soyayya bada irin ku ba, balgaza, jaka mara sanin daraja da k'imar kanta, ya k'arasa maganar yana nuna su a wulakance,
Raleeya dafe da kunci hawaye na gangaro mata ta kura mishi ido, bakin ciki ya hanata furta koda kalma daya,
takaici ya hana ta yi mishi bayanin ba cewa zatayi tana sanshi ba, so take tace mishi INA SAN KA KOYA MIN ASSIGNMENT,
amma ya datse maganarta ya tozartata ya wulakantata agaban dubban jama'a har da malamansu,
cikin fushi Raleeya tace " kai! ba abinda muke nufi kenan ba, assign..... " quite, I said ya isa haka ban san sake jin koda kalma daya tak,
yayi maganar yana nuna ta da yatsa while duk ilahirin jikinshi na kerrma,
baya Deeyanah taja saboda yadda Ajlaal ya matso gaf da ita har suna iya juyo fitar numfashin juna, a hankali ta d'ago kanta ta kalli mutanen dake wajen,
magana sukeyi sosai suna nunata harda masu zunbenta, da gudu ta juya tabar wajen had'i da fashewa da kuka, Raleeya ta nunashi da yatsa kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tayi kwafa tabi bayan Deeyanah da sauri tana kwala mata kira, cike da halin ko in kula ya taka ya shige class babu damuwa balle nadamar abinda ya aikata a tattare dashi.

Bata tsaya ba duk da kiran da Raleeya keyi mata, ta fad'a napep tana fad'in " muje...,!
Napep din ya tada yana cewa " ina zan kaiki Hajiya?

Bata d'ago kai ba ta bashi amsa cikin murya kuka, " Magajin Rumfa, bai kuma magana ba yaja suka tafi, Raleeya ta k'araso wajen tana fad'in " wait... wait ku tsaya, amma ina sun riga sun tafi, kanta ta tana sharb'ar kukan takaicin yau ita namiji ya disga a gaban mutane, har bakin get ya kaita, tun kafin ya ida tsayawa ta bashi 1000 ta sauko, me napep d'in na kwala mata kira kan ta amshi canji, amma ko takan canjin bata bi ba,
da gudu ta shiga gida bata tsaya a parlour ba ta wuce bedroom dinta tare da rufe kofa ta fad'a saman bed ruf da cikin tare da saki saban kuka, saida tayi kwana uku bataje makaranta ba,
sai a rana ta uku ne ta shirya ta tafi, tunda ta shiga makarantar kanta ke duk'e k'asa, koda wasa batayi gangancin d'agawa ta kalli kowa ba,
duk inda ta wuce sai taga dalibai na nunata suna magana da dariya k'asa-k'asa, tafiya kawai take batare data san inda take jefa k'afarta ba,
jinta take kamar tana tafiya a saman kayoyi duk ta tsargu, kamar daga sama taga gungun dalibai sun kai goma sun sha gabanta,
cike da shakiyanci suna dariya guda daya daga cikinsu ya make murya yace " ina sanka.....!
sauran suka had'a baki wajen cewa " aaahhh bana sanki, sai kace dole, suka dau ihuuuu gaba d'ayansu,
batayi musu magana ba ta zagaye su ta raba ta wuce, suka bi bayanta suna ihuuuu, gabanta wani namiji yasha yana rangwada kamar mace ya yafa mayafi ya kalli wani dake gefenshi yace " ina sanka,
fuska dayan ya bata had'i da yiwa dayan marin karya yace " bana sanki, banza ballagaza kawai, daya namijin mai mayafi ya durkusa yana yarfa hannu yace " bafa haka nake nufi ba,
cewa zanyi ka koya man assignment, a tare sauran daliban suka dau ihuuu da shewa, batare da tayi musu magana ba ta wuce abinta ta shiga aji ta zauna a darare.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now