*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh1️⃣2️⃣
Suna gama cin Abincin Abbu ya fice Ammu kuwa tayi ciki dan amsa waya itace da kanta ta tattara gurin ta tsaftace sa ta dawo palo gurinsu Azrah tana k'in tanka neman maganarta da sikeyi akan aurenta.
Bata wani fahimtar abinda ake fada a kallon datakeyi d'in saboda sam hankalinta bai wani damu da kallon ba sakewa take son tayi kaman yanda take a baya amma igiyoyin da aka d'aura mata na aure take jin kaman a gangar jikinta aka nannad'e ta dasu.
Kallon Azaan dake kokarin mik'ewa tayi da fararen idanuwanta tace,
"lafiya dai?
Bai waiwayo ba ya nufi kofa da sauri yana cewa,
"Wani guri zanje yanzu zan dawo.
Bayanshi tabi da kallo kafin ta maida kallonta kan Azrah dake ta son suyi maganganunsu na mata tace,
"Menene kuma?
'Yar dariya Azrah tayi tana cewa,
"Ke wai to auren kawai aka d'aura ne bazaki fara d'an maintaining kanki ki fara dabaru ko k'ok'arin tattala mijin ba?....
Katseta Deeyanah d'in tayi da mamakin karfin halin zancen nata tace,
"Dan Allah dena fad'a ma kada wani yaji wannan maganar,
Meye kuma tattala miji da maintaining din?
Ni dai Gaskia bana cikin wannan zancen.Dariyar takaici da kin rainawa kanki wayo Azarah ta sake tana cewa,
"Au haka kikace?
Bakisan tattala mijin ba?
Ok badamuwa zaki fada da bakin ki ne."Nidai dan Allah ki dena zancen nan Allah nidai banaso"
Ganin hakan Azrah tak'i denawa taci gaba da yi
Abin kunya da damuwa wasu maganganun amma saboda dagewa da karfin halin Azrah din dariya ma abun yafara bata
Ita kuwa Azrah ta sake dagewa bakin rai tana mata huduba sai ga Deeyanah na dariya sosai tini suka fada wata hirar dan kawai Deeyanah din ta sake.Ammu ce ta fito jin dariyar tasu ta k'arasa gurinsu tana kallon Deeyanah dake washe da fuska ta zauna da wayarta a hannu tana cewa,
"Deen bai fito breakfast ba gashi har rana na neman yi banajin kuma ya fita saboda bai shigo ya gaida ko Abbunku ba ya kafin fita ba.
Shiru Deeyanah tayi tana kasa saka baki a maganar
Azrah tana kallon Ammun tace,"May be ko wani uzirin yasashi fita da wuri kokuma bai fitan ba yana hutawa ne amma an kira wayarshi anji ne?
"Eh nakira wayarshi a kashe
Jiya dai yace kashewa yayi saboda masu kiranshi tako ina akan maganar aurenshi da sukaji.Deeyanah ce ta dan kalli Ammun a gajarce tace,
"Ammun zaifa fito da kansa ne idan ya tashi menene na damuwa akan bai fito ba tunda ba yaro bane. Tayi maganar cike da k'oasawa da maganarshi.
Katseta Ammu tayi da fad'in " ke! rufe min baki ko inci gidanku, Deeyanah ta d'an turo baki, cike da tsokana Azrah tace " Ammu ai da taje ta dubo a bedroom d'inshi a gani ko lafiya.
Harara ta zubawa Azrah batare data ce komai ba, Ammu tace.
"Jeki ki dubo min idan yana nan lafiya, sai kizo ki had'a mishi breakfast ki kai mishi.
Kallon Azrah da itama ta gyada kai tayi alamar tayi kafin ta maida kallonta kan Ammu tana dan sauya fuska zuwa ta mamakin da fargabar turata da Ammun tayi, tsautsayi ne ma yasata yin magana data sani tayi musu shiru da suna magana wata k'ila da Ammun ta manta ita matarshi ce.
Shiru ta d'an n yi batare da ta motsaba tana dan sake kallon Ammun wadda ta sake maimaita mata kalmar taje ta duboshi d'in.
Baki ta kuma turowa tace " Ammu ga Aunty Azrah nan taje ta dubo shi mana lalle sai ni?
"Kinci gidanku! Ammi ta fad'a tana kai mata duka kafin ta d'ora da " ba ke ce matarshi ba?
"Ko kuma kawai ba'a san yanayin da yake ba sai a tura mishi matar wani, dama haka ake yi?
"To da ban zama matarta shi ba dawa za'a tura?
"Ni zani, Ammu ta bata amsa a k'ufule, sai ta sake turo bakinta kana tace " yanzun ma saiki je.
Duka Ammu takai mata tayi saurin mik'ewa, cikin fad'a da had'e fuska Ammu tace " nace kije ki dubo shi ko?
Mutuwa jikinta yayi ta mik'e a sanyaye ta bar wajen tana hana kanta damuwa ko jin komai game da aiken tunda ba yau ne karon farko da aka taba tura ta kiranshi ko dubo shi ba, haka nan yau d'in take jin abun daban, duk lokacin da Ammu zata jishi shiru batada nutsuwa idan ba'a dubo mata shi ba, kusan duk za'a aika duboshi itace wannan kaddarar take hawa kanta sai dai bata taba jin komai ba idan an aikatan amma yau d'in ko kuma tace yanzu tana wani irin dabaibayi na nanannad'e akan baya kodan auren dayake tsakaninsu ne oho.
Kai tsaye hanyar bedroom dinshi ta nufa tana kokarin basar da komai.
Bakin k'ofar ta tsaya cak had'i da sauke numfashi mai had'e da ajiyar zuciya a hankali tukuna ta daga hannunta na dama ta mik'a kan k'ofar tayi knocking cikin nutsuwa.
Shiru taji ba alaman motsi ta sake kai hannu ta buga k'ofar tana d'an k'osawa da tsayuwar.
Shiru-shiru ba alaman ma yana ciki tasake bugawa da d'an karfi amma ba motsin komai daga ciki.
Juyawa tayi zata koma sai kuma ta dakata ta sake buga k'ofar tareda kama handle din kofar ta murda tana turawa ta shiga.
Sanyin Ac da k'amshin turarensshi na CHANEL daya gama kama d'akin da komai na d'akin shine ya shiga hancinta kai tsaye ta sake sauke wani sanyayyan numfashi gabanta na d'an fad'uwa.
Bata tsaya k'aarewa dakin kallo ba kai tsaye gurin data hango lafiyayyan gadonshi ta kalla taga ba alamar mutum akai dan haka ta juya dan ficewa daga dakin,
taku biyu tayi aka bud'e k'ofar bathroom d'in dayake cikin d'akin tana jin hakan ta tabbatar da shine kuma k'amshin sabulun wankanshi na Jaggins daya sake shiga hancinta tasamu tabbacin wanka ya fito dan haka bata juyoba ta daga k'afafuwanta dan ficewa daga d'akin.Taku biyu yayi ya rik'o hannunta ta baya batare da ya bude baki yayi magana ba saidai kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya
Ita na sanyin hannunshi dayake da ruwan wankanshi mai tsafta
Shikuma sbd dumin fatar hannunta data hadu da tasa mai sanyin.JIDDARH
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
EspiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...