*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh5️⃣8⃣
K'arfe shida na safe sautin kukan Ammi da salatinta ya cika gaba d'aya Estate d'in, kowa ya fito cikin tashin hankali ta fito harabar gidan d'auke da Deedee a hannunta, mazan gidan suna masallaci dan idan suka yi sallar asuba basa fitowa sai k'arfe shida, gaba d'aya suka fito har Babah da Abbi, Abbi ta nufa cikin tashin hankali ta mik'a mishi yaron tana fad'in " Alhaji na tashe shi zan shirya shi makaranta yak'i tashi babu irin tashin da banyi mishi ba yak'i tashi, tana kara kunnena a k'irjinshi banji komai ba, jikin Abbi na tsuma ya karb'i Deedee bai tsaya b'ata lokaci ba yayi asibiti dashi, su Babah suka bi bayanshi, gwajin farko likita ya gano yaron ya mutu a wanni biyu zuwa uku da suka wuce, sai dai sunyi duk wani binciken da zasuyi sun kasa gano dalilin mutuwar yaron.
Gaba d'ayansu jikinsu a sanyaye suka dawo gida d'auke da gawar Deedee, dakyar Babah yaje bakin k'ofar d'akin Deen, muryarshi bata fita sosai saboda yadda yake kokawa wajen danne abinda ke taso mishi, " Deen ka fito Allah yayiwa Deedee rasuwa, yakai ruku'un sallar azahar, jin abinda Babah ya fad'a ya sashi d'agowa had'i da cewa " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mutuwa! Deedee ya mutu?
Ai ya manta da batun sallar da yake yi, jikinshi na b'ari yayinda da zuciyar ke tsalle kamar zata fad'o ta bakinshi ya bud'e k'ofar, Babah na tsaye yana jiranshi, hannunshi ya kama kamar k'aramin yaro ya fito dashi falo inda gawar Deedee ke kwance, gaban gawar ya zauna had'i da dunk'ule hannunshi ya saka a baki ya cija gami da fashewa da wani irin kuka me k'una, shi kad'ai ne abinda ya rage mishi shima gashi nan sun raba shi dashi, Deeyanah ta cuce shi mak'ura duk wani abu da yake so sai ta raba shi dasu, da gaske yake jin tsanarta har cikin jinin jikinshi, a sanadinta ya rabu da d'anshi, cikin k'araji ya rungume gawar Deedee yana kuka kamar ranshi zai fita, duk da yaji tana ihuun ya fito ya taimake ta zai kashe Deedee ko kusa bai tab'a tunanin da gaske take ba, bayyi zaton rashin imanin shi har ya kai haka ba.
Ammu na rik'e da hannun Deeyanah kamar daluwa take bin Ammi, cikin sanyi murya Ammi na share kwalla tace " mun rasa Deedee, bata fahimci inda zancen Ammi ya dosa ba dan haka ta zubawa Ammi ido, gane bata fahimci maganar ba yasa ta sake fad'in " Deedee ya rasu Deeyanah ga gawarshi nan.
"Wanne Deedee kuma?
"Waye Deedee?
Ta fad'a tana bin kowa dake falon da kallo dan kanta ya gama kullewa gaba d'aya.
Sai da su Ammi suka kalli juna cike da tsoron kota haukace kana cike da fargaba Ammi ta dafa ta tace " Deeyanah d'anku keda Deen.
Wani abu taji yana yawo saman kanta, lokaci d'aya taji duk ilahirin jikinta ya d'auki k'aik'aiyi.
Ji tayi kamar an kama jijiyoyin jikinta an tsinkasu lokaci d'aya, komai ya gama kunce mata, duniyar ta tsaya mata cak, babu abinda bai tsaya mata cikin kanta ba, a hankali ta zube bisa gwiwowinta so take tayi kuka amma ta kasa, magana take sanyi amma bakinta yayi mata mugun nauyi, cikin ranta take fad'in " dama dayace mata zai kashe d'ansu da gaske yake yi?
Duk da tasan zai iya aikata komai dan mafitar kanshi batayi zaton rashin imaninshi yakai mak'ura har haka ba, batayi zaton zai iya kashe yaro ba, rashin imanin yayi yawa, ita da kanta tayi sanadin d'anta, addu'a take san ta bud'i baki tayi amma yadda kasan an d'aure mata harshenta.
Cikin mutuwar jiki ta duk'a, cikin sand'a ta mik'a hannu zata tab'a gawar Deedee yayi saurin rik'e hannunta had'i da janye gawar Deedee d'in, idonshi cikin nata sun kad'a sunyi jajir, sai da k'irjinta ya kusa tsagewa saboda yadda ya doka da k'arfi, kanshi ya girgiza muryarshi na sark'ewa yace " karki soma tab'a min d'a dan bazan tab'a baki wannan damar ba, jikinta a sanyaye ta zame hannunta had'i da mik'ewa tabar falon, d'akinta ta koma ta jin gina bayanta da jikin k'ofar d'akin so take tayi kuka amma yadda kasan an shak'e ta haka take ji.
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...